• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Kasuwanci

Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote, Shugaban NASCON Sun Buƙaci A Ƙara Zuba Jari A Cibiyoyin Kasuwanci

October 29, 2026
in Kasuwanci
Reading Time: 2 mins read
0
Dangote Da NASCON Sun Buƙaci A Ƙara Zuba Jari A Masana’antu Domin Bunƙasa Tattalin Arziki
0
SHARES
5
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daga; Bashir Bello, Abuja

Karanta HakananPosts

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Olakunle Alake, da Manajan Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudnarwar Kamfanin NASCON Allied, Aderemi Saka, sun jaddada buƙatar ƙara zuba jari a masana’antu da sarrafa albarkatun ƙasa zuwa kayayyakin da aka ƙara wa ƙima, domin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya, ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma inganta ƙarfinsu na yin gogayya a kasuwannin cikin gida.

Da yake Jawabi a yayin taron shugabannin manyan kamfanoni wanda aka gudanar karo na 32, a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, Mista Alake,wanda Isa Yusuf Aruwa ya wakilta,, ya bayyana cewa rukunin kamfanonin Dangote na taka rawar gani wajen inganta masana’antu, waɗanda za su iya zama ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki. Ya kawo misalin shirin kafa Cibiyar Masana’antu ta Dangote Olokola a Jihar Ondo, yana mai cewa hakan na nuna ƙudurin kamfanin na faɗaɗa masana’antu a Najeriya.

A cewarsa, kafa masana’antu masu alaƙa da juna a wuri guda zai rage kuɗaɗen gudanarwa, ƙara ingancin samar da kayayyaki, samar da guraben ayyukan yi da kuma bai wa kamfanoni damar musayar ilimi da ƙwarewa.

Alake ya ce, irin waɗannan cibiyoyi na iya taimakawa wajen magance matsalolin da masana’antu ke fuskanta, musamman ta fuskar samar da makamashi, sufuri, kayayyakin more rayuwar masana’antu da damar shiga kasuwannin. Amma fadada harkokin kasuwanci zai ta’alaka ne da yanayin yadda aka hada harkokin kasuwancin.

“Nasarar fadada cibiyar masana’antu ba za ta tsaya ga gina manyan kamfanoni kawai ba, sai dai za a auna ta ne da harkokin kasuwanci da ke kewaye da ita.

Acewar sa, manyan kamfanoni za su iya taimaka wa ƙananan masana’antu ta hanyar ba su horon fasaha, tantance masu samar da kayayyaki, shirye-shiryen koyon sana’a, damar gwada ingancin kayayyaki da kuma samar musu da damar shiga yarjejeniyoyin samar da kayayyaki.

A nata jawabin, Manajan Daraktar NASCON Allied Industries, Aderemi Saka, ta yi kira da a sake duba tsarin samar da kayayyakin da masana’antu ke buƙata, musamman samun kayan aiki, tasirin tsarin kayayyakin da aka kammala da sauran muhimman abubuwan da ake amfani da su wajen samar da kayayyaki.

Saka ta gabatar da wannan matsaya ne yayin da take magana kan yadda za a inganta yawan aiki da ƙwarewa domin bunƙasa tattalin arziki.

Ta ce, “wajibi ne a duba inda ake samun kayayyakin aiki da kuma ko ƙananan kamfanonin cikin gida za su iya samar da waɗannan kayayyaki, kana su ƙara ƙima ga manyan masana’antu. Shin muna da karfin da zamu iya samar da kayayyakin aiki domin gudanar da harkoki? Ta tambaya

Saka ta kuma jaddada cewa, domin masana’antu su bunƙasa yadda ya kamata, dole ne a bai wa ma’aikata horon fasaha da ƙwarewar sana’a da za su taimaka musu wajen inganta ayyukansu, musamman a wannan zamani da fasahar masana’antu ke sauyawa cikin sauri.

Ta ce rukunin kamfanonin Dangote, ƙarƙashin jagorancin shugabanta kuma babban jami’in gudanarwa, Aliko Dangote, na ci gaba da ba da muhimmanci ga horas da matasan Najeriya da kuma inganta ƙwarewarsu ta hanyar tsare-tsaren koyon aiki da shirye-shiryen haɓaka ƙwarewa.

Kamfanin Dangote Industries na daya daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin gudanar da Babban Taron Tattalin Arzikin Najeriya karo na 32.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa rukunin kamfanonin Dangote bisa irin gudunmawar da ta ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.

Previous Post

Hotuna Masu Ban Sha’awa

Next Post

Kamfanin Simintin Dangote Na Gboko Ta Gudanar Da Shirin Sake Fasalin Direbobi

Related Posts

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026
Kasuwanci

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

November 26, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya
Kasuwanci

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

November 25, 2026
Kasuwanci

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

November 25, 2026
Shugabannin Masana’antu Sun Yabawa Dangote Kan Tasirin Noma A Afirka
Kasuwanci

Shugabannin Masana’antu Sun Yabawa Dangote Kan Tasirin Noma A Afirka

November 19, 2026
Kasuwanci

NNPC Ta Tabbatar Da Tashin Gobarar A Wani Gidan Mai Da Ke Jihar Legas

November 17, 2026
Makon Ɗorewa: Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana Ta Tallafawa Ƙananan Masana’antu Da Yan Kasuwa
Kasuwanci

Makon Ɗorewa: Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana Ta Tallafawa Ƙananan Masana’antu Da Yan Kasuwa

November 9, 2026
Next Post
Kamfanin Simintin Dangote Na Gboko Ta Gudanar Da Shirin Sake Fasalin Direbobi

Kamfanin Simintin Dangote Na Gboko Ta Gudanar Da Shirin Sake Fasalin Direbobi

ADIPEC 2026: Mun Ƙara Ganga 600,000 A Kowace Rana Ga Man Fetur —Ojulari

ADIPEC 2026: Mun Ƙara Ganga 600,000 A Kowace Rana Ga Man Fetur ---Ojulari

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

November 26, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

November 25, 2026

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

November 25, 2026
NNPC Ta Lashe Kyautar Duniya Ta Ƙungiyar WBA Bisa Kyawawan Ayyukanta A Fannin Sayar da Man Fetur

NNPC Ta Lashe Kyautar Duniya Ta Ƙungiyar WBA Bisa Kyawawan Ayyukanta A Fannin Sayar da Man Fetur

November 22, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin