
Daga; Bashir Bello, Abuja
Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Olakunle Alake, da Manajan Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudnarwar Kamfanin NASCON Allied, Aderemi Saka, sun jaddada buƙatar ƙara zuba jari a masana’antu da sarrafa albarkatun ƙasa zuwa kayayyakin da aka ƙara wa ƙima, domin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya, ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma inganta ƙarfinsu na yin gogayya a kasuwannin cikin gida.
Da yake Jawabi a yayin taron shugabannin manyan kamfanoni wanda aka gudanar karo na 32, a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, Mista Alake,wanda Isa Yusuf Aruwa ya wakilta,, ya bayyana cewa rukunin kamfanonin Dangote na taka rawar gani wajen inganta masana’antu, waɗanda za su iya zama ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki. Ya kawo misalin shirin kafa Cibiyar Masana’antu ta Dangote Olokola a Jihar Ondo, yana mai cewa hakan na nuna ƙudurin kamfanin na faɗaɗa masana’antu a Najeriya.
A cewarsa, kafa masana’antu masu alaƙa da juna a wuri guda zai rage kuɗaɗen gudanarwa, ƙara ingancin samar da kayayyaki, samar da guraben ayyukan yi da kuma bai wa kamfanoni damar musayar ilimi da ƙwarewa.
Alake ya ce, irin waɗannan cibiyoyi na iya taimakawa wajen magance matsalolin da masana’antu ke fuskanta, musamman ta fuskar samar da makamashi, sufuri, kayayyakin more rayuwar masana’antu da damar shiga kasuwannin. Amma fadada harkokin kasuwanci zai ta’alaka ne da yanayin yadda aka hada harkokin kasuwancin.
“Nasarar fadada cibiyar masana’antu ba za ta tsaya ga gina manyan kamfanoni kawai ba, sai dai za a auna ta ne da harkokin kasuwanci da ke kewaye da ita.
Acewar sa, manyan kamfanoni za su iya taimaka wa ƙananan masana’antu ta hanyar ba su horon fasaha, tantance masu samar da kayayyaki, shirye-shiryen koyon sana’a, damar gwada ingancin kayayyaki da kuma samar musu da damar shiga yarjejeniyoyin samar da kayayyaki.
A nata jawabin, Manajan Daraktar NASCON Allied Industries, Aderemi Saka, ta yi kira da a sake duba tsarin samar da kayayyakin da masana’antu ke buƙata, musamman samun kayan aiki, tasirin tsarin kayayyakin da aka kammala da sauran muhimman abubuwan da ake amfani da su wajen samar da kayayyaki.
Saka ta gabatar da wannan matsaya ne yayin da take magana kan yadda za a inganta yawan aiki da ƙwarewa domin bunƙasa tattalin arziki.
Ta ce, “wajibi ne a duba inda ake samun kayayyakin aiki da kuma ko ƙananan kamfanonin cikin gida za su iya samar da waɗannan kayayyaki, kana su ƙara ƙima ga manyan masana’antu. Shin muna da karfin da zamu iya samar da kayayyakin aiki domin gudanar da harkoki? Ta tambaya
Saka ta kuma jaddada cewa, domin masana’antu su bunƙasa yadda ya kamata, dole ne a bai wa ma’aikata horon fasaha da ƙwarewar sana’a da za su taimaka musu wajen inganta ayyukansu, musamman a wannan zamani da fasahar masana’antu ke sauyawa cikin sauri.
Ta ce rukunin kamfanonin Dangote, ƙarƙashin jagorancin shugabanta kuma babban jami’in gudanarwa, Aliko Dangote, na ci gaba da ba da muhimmanci ga horas da matasan Najeriya da kuma inganta ƙwarewarsu ta hanyar tsare-tsaren koyon aiki da shirye-shiryen haɓaka ƙwarewa.
Kamfanin Dangote Industries na daya daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin gudanar da Babban Taron Tattalin Arzikin Najeriya karo na 32.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa rukunin kamfanonin Dangote bisa irin gudunmawar da ta ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.



















