

Ministan Raya Ma’adanai, Dr. Dele Alake, ya bayyana cewa kamfanin Dangote Cement Plc na taka rawa mai muhimmanci a ci gaban al’ummomin da ke karɓar bakuncinsa a Gboko, Jihar Benue.
Yayin kaddamar da ayyukan samar da ruwa na miliyoyin naira, bayar da tallafin karatu da horar da matasa kan sana’o’i, ministan ya yaba da gudunmawar da kamfanin ke bayarwa ga al’ummomin da ke kusa da shi.
An wakilce shi da Daraktar Ma’adanai da Bin Ka’idojin Muhalli a Jihar Benue, Hajiya Adijatu Usman, inda ya ce Dangote Cement na cika alkawuran da ya dauka a yarjejeniyar Raya Al’umma (CDA).
Ya ce yarjejeniyar CDA na tabbatar da cewa kamfanonin hakar ma’adanai suna mayar da wani kaso na ribarsu don ci gaban al’ummomin da suke aiki a cikinsu.
Ya ce: “Zan iya tabbatar muku cewa Dangote Cement ya aiwatar da ayyuka da dama ga al’ummomin da ke kusa da shi.
“Wannan aikin ya samo asali ne daga wata doka ta Gwamnatin Tarayya wadda ke bukatar kamfanoni irin su Dangote su mayar da alheri ga al’ummomin da suke aiki a cikinsu.
“Mun zauna da wakilan al’ummomi guda shida da ke kusa da kamfanin, kuma sun amince da cewa suna bukatar wadannan ayyuka. A yau muna nan domin kaddamar da su bayan kammala su.
“Muna fatan al’ummomin za su dauki wadannan ayyuka a matsayin nasu, su kula da su, domin su dore. Hakan zai kawo ci gaba a tattalin arzikin yankunan.”
A yayin bikin kaddamar da ayyukan, Shugaban Sashen Ayyukan Zamantakewa na Kamfanin Dangote Cement a Gboko, Dr. Johnson Kor, ya bayyana cewa an kammala wadannan ayyuka ne domin al’ummomin da ke fama da karancin ruwa mai tsafta.
Ya ce: “A yau muna kaddamar da ayyukan da aka tsara tun watan Disamba na shekarar 2024. Mun kammala da dama daga cikinsu, kuma sun hada da rijiyoyin burtsatse masu amfani da injin da kuma hasken rana.
“Yarjejeniyar CDA an kulla ta ne tsakanin Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya, al’ummomin da ke kusa da kamfanin, da sauran masu ruwa da tsaki.
“Yarjejeniyar na tsawon shekaru biyar ne, kuma wannan shekarar ce ta farko. A shekara mai zuwa za mu shiga zagaye na biyu. Hakanan muna aiki kan wasu ayyukan lantarki da ba a kammala ba tukuna.
“Wadannan yankuna na fama da karancin ruwa, wasu ma suna amfani da ruwan koguna saboda kusancinsu da Kogin Benue. Saboda haka muka ga dacewar samar musu da ruwa.”
Ya ce rijiyoyin burtsatse suna cikin al’ummomin Pass Brother, Mbaakpoghol-Mbatyu, Mbaswa-Mbatser da Agboghol-Amua.
Dagacin Mbaakpoghol-Mbatyu, Chief Kunav Anum, ya bayyana farin cikinsu da samun rijiyar burtsatse a cikin al’ummarsu.
“Muna matukar farin ciki. Ba mu yi tsammanin hakan zai faru da wuri haka ba. Mun ji dadin wannan kyauta daga Dangote Cement Plc” Yace.
Sarkin ya kara da cewa al’ummarsa ta riga ta amfana da wutar lantarki daga kamfanin, kuma ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan kamfanin.
A wata sanarwa daga kamfanin, an bayyana cewa: “A matsayin ci gaba da wannan kudiri, an kara yawan kudin tallafin karatu zuwa ₦28,800,000.00 a bana, tare da fadada shirin zuwa dukkan al’ummomi guda shida da ke kusa da kamfanin, kamar yadda yarjejeniyar CDA ta tanada. Wannan mataki na nuni da burinmu na tabbatar da adalci, hadin kai da raba moriyar ci gaba ga kowa da kowa.”
Kamfanin ya kuma aiwatar da wasu ayyuka da dama, yayin da wasu ke ci gaba, ciki har da Shirin Tallafawa Mata, Manoma da Matasa dukkansu domin inganta rayuwar al’ummomin da ke karbar bakuncin kamfanin.



















