Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Dangote Industries Limited, ya janye korafin da ya shigar gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka (ICPC) akan tsohon Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.
Fitaccen dan kasuwar ya janye korafin ne ta hannun lauyansa, Ogwu Onoja, wanda shi Babban Lauya a Najeriya ne (SAN). Kakakin ICPC, John Odey, ya tabbatar da wannan ci gaba.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Odey ya bayyana cewa an isar da sanarwar janye korafin ne ta cikin wata wasika daga lauyan Dangote. Ya ce mai korafin ya janye korafin gaba ɗaya, kuma wata hukuma mai bin doka ta karɓi alhakin ci gaba da lamarin.
Sai dai Odey ya jaddada cewa duk da janyewar, ICPC za ta ci gaba da gudanar da bincike bisa doka da huruminta.
Ya kara da cewa ci gaba da binciken yana da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma yaki da cin hanci da rashawa domin amfanin Najeriya.
Sanarwar ta ce: “ICPC na so ta bayyana a fili cewa bisa tanadin sashe na 3(14) da 27(3) na dokarta, binciken da ke da alaka da muradun al’ummar Najeriya da kasar gaba ɗaya ya riga ya fara kuma yana ci gaba da gudana.
“Saboda haka, ICPC za ta ci gaba da binciken wannan lamari bisa huruminta na doka da kuma don tabbatar da gaskiya, rikon amana da yaki da cin hanci da rashawa domin amfanin Najeriya.”



















