Dangote, Kamfanin Mai Na Ƙasar Congo Sun Fara Tattaunawa Kan Haɗin Gwiwa a Fannin Tace Mai da Samar da Kayayyakin Man Fetur…
Yunkuri na ƙarfafa tsaron makamashi da zurfafa haɗin masana’antu a Afirk
Daga Bashir Bello, Abuja
Kamfanin man ƙasa na Jamhuriyar Congo, Société Nationale des Pétroles du Congo (SNPC) tare da Kamfanin Matatan Mai na Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals sun fara tattaunawa kan haɗin gwiwa na dabaru domin ƙarfafa samar da kayayyakin man fetur da aka tace a Jamhuriyar Kongo, tare da bunƙasa haɗin makamashi da masana’antu a nahiyar Afirka.
Shugaban SNPC, Maixent Raoul Ominga, wanda ya jagoranci tawagar Kongo a ziyarar da suka kai Dangote Petroleum Refinery a Legas, ya bayyana wannan cibiyar a matsayin muhimmin ginshiƙi ga Afirka, tare da nuna sha’awar kamfanin wajen kafa dogon haɗin gwiwa da Dangote.“Muna ziyartar wannan matatar mai mai ban mamaki, wadda ta zama babban nasarar masana’antu ga Afirka.
Jamhuriyar Congo tana da ƙarfin tace mai, kuma muna sha’awar binciken haɗin gwiwa na dabaru da zai taimaka wajen ƙarfafa samar da kayayyakin man fetur da aka tace tare da ƙirƙirar ƙima ga kowanne bangare,” in ji Ominga.
Ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan damar haɗin gwiwa a fannin tace mai, samar da kayayyakin man fetur, tsaron makamashi, bunƙasar masana’antu da musayar ilimi. Ominga ya yaba wa Dangote Group saboda nuna cewa Afirka na iya samun kuɗi, gina da kuma gudanar da manyan cibiyoyin masana’antu na ƙasa da ƙasa, yana mai bayyana matatar mai a matsayin muhimmin mataki a sauyin masana’antu na nahiyar.
Ya kuma yaba da jarin Dangote Group a Jamhuriyar Congo, musamman a fannin siminti, inda ya ce hakan ya ƙarfafa ƙarfin masana’antu na cikin gida, ya faɗaɗa samarwa kuma ya inganta samun kayan gini.
Shugaban Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya sake jaddada kudirin kamfanin na bunƙasa masana’antu a Afirka ta hanyar ƙara ƙima, haɗin gwiwar yankuna da jarin da ake zuba a duk faɗin nahiyar.
“Muna tare da Afirka, ba Najeriya kaɗai ba. Ku gaya mana bukatunku, za mu duba yadda za mu iya yin aiki tare,” in ji Dangote.
Ya bayyana cewa matatar mai ta kafa sabon ma’auni na ingancin man fetur a Afirka ta hanyar samar da kayayyakin man fetur da suka cika mafi girman ƙa’idodin ƙasa da ƙasa, tare da inganta samun man mai tsabta da rage dogaro da shigo da man da aka tace daga wajen Afirka.
A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Rukunin, Oil and Gas, Dangote Industries Limited, Devakumar Edwin, ya bayyana dabarun faɗaɗa dogon lokaci na kamfanin, wanda zai ƙara ƙarfin tace mai zuwa ganga miliyan 2.1 a kowace rana, wanda ya haɗa da ganga miliyan 1.4 a Najeriya da kuma shirin gina cibiyar tace mai ganga 700,000 a kowace rana a Kenya domin hidimar kasuwannin Gabashin Afirka.
Ya kuma bayyana shirin kamfanin na zuba jarin ƙarin dala biliyan 46 tsakanin shekarar 2026 da 2028 a fannin tace mai, siminti da takin zamani a matsayin wani bangare na yunkurin hanzarta bunƙasar masana’antu a Afirka.
Wannan tattaunawa ta nuna kudirin haɗin gwiwa na SNPC da Dangote Industries wajen zurfafa haɗin makamashi a Afirka, ƙarfafa sarkar ƙima ta yankuna da kuma ƙara samun ‘yancin kai a fannin kayayyakin man fetur da aka tace yayin da nahiyar ke ci gaba da ƙarfafa tsaron makamashi da kuma ƙara cinikayyar cikin Afirka.
A cikin taron, akwai Fatima Aliko Dangote, Darakta Janar na Rukunin, Kasuwanci, mai da iskar gas (Oil and Gas), Dangote Industries Limited; Peggy Ndongo, mai ba da shawara ga Shugaban Jamhuriyar Congo; da masu ba da shawara ga Shugaban SNPC, Aymar Ebiou da Norbert Mabiala.


















