Daga Bashir Bello. Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya samu gagarumar lambar yabo daga Ƙungiyar Matasa Lauyoyin Arewa (Arewa Young Lawyers’ Forum Award) a matsayin girmamawa bisa jajircewarsa wajen inganta sana’ar lauya da ƙarfafa bangaren shari’a a Jihar Kano.Wannan sanarwa ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Alhamis.
An mika lambar yabo a taron shekara na biyu na Ƙungiyar da aka gudanar a Kano, inda lauyoyi, manyan masana shari’a, malamai, jami’an kotu da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta domin tattauna matsalolin da ke shafar sana’ar lauya da isar da adalci a Najeriya.
Yayin mika lambar yabo, Babban Lauya (SAN), Barrista Oyinkansola Badejo Okunsanya, ta bayyana cewa an zaɓi Gwamna Yusuf ne saboda gudummawar da yake bayarwa ga sana’ar lauya, goyon baya ga ayyukan Ƙungiyar Matasa Lauyoyin Arewa, da kuma ci gaba da zuba jari wajen ƙarfafa bangaren shari’a.
Ta yaba da yadda gwamnan ke mutunta doka, jajircewarsa wajen tabbatar da ‘yancin kotuna, da manufofinsa na sauƙaƙa wa jama’a samun adalci a Jihar Kano.
A cikin jawabinsa, Gwamna Yusuf ya gode wa Ƙungiyar bisa wannan girmamawa, inda ya bayyana lambar yabo a matsayin gata da kuma kira ga ƙarin hidima.
Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta adalci, gaskiya da bin doka, tare da bayar da goyon baya ga kotuna da haɗin gwiwa da lauyoyi domin inganta isar da adalci da kuma ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya.




















