Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.
A wani muhimmin mataki da ke nuni da ƙudurinta na gyara fannin kiwon lafiya a Najeriya, Majalisar Dattawa ta amince da kudurin dokar da ke neman kafa Hukumar Kula da Inganci da Tsaron Marasa Lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya a fadin ƙasar. Wannan kuduri ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar, wanda ke nuna cewa an kusa kaiwa matakin karshe na amincewa da shi.
Kudurin, wanda Sanata Samaila Dahuwa Kaila daga Bauchi ta Arewa ya gabatar, na da nufin daidaita tsarin bayar da kulawar lafiya, ƙarfafa tsaron lafiyar marasa lafiya, da tabbatar da cewa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu suna aiki da ingantattun ka’idoji da tsari.
Sanata Kaila ya bayyana cewa rashin gamsuwa da ayyukan kiwon lafiya a Najeriya ya sa mutane da dama ke komawa ga magungunan gargajiya, warkarwa ta addini, da shan magani ba tare da izinin likita ba.
Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda yan Najeriya ke yawan fita ƙasashen waje domin neman lafiya, alamar gazawar tsarin kiwon lafiya na cikin gida.
Ya ce kafa wannan hukuma za ta kawo ƙarshen sakaci da rashin bin ƙa’idoji a fannin, musamman ga waɗanda ke gudanar da ayyukan lafiya ba tare da lasisi ba, ko kuma waɗanda ke aikata laifukan cire sassan jikin marasa lafiya ba bisa ƙa’ida ba.
“Mussaman zakaji cewa an sace ma wani Koda ko kuma an cire ma wata Mata mahaifa a Asibiti ba tare da amincewar ta ba, Wannan hukumar zai Magance irin wannan matsalolin, Idan aka kama Wanda ya Aikata haka to zai fuskanci hukunci” Inji Sanata Samaila Dahuwa
Daga cikin muhimman abubuwan da kudurin ya ƙunsa akwai buƙatar takardar shaidar bin ƙa’idoji (certification) ga kowace cibiyar lafiya. Wannan zai tabbatar da cewa sabbin asibitoci za a gina su ne kawai a wuraren da ake da buƙata, kuma su cika dukkan sharuddan tsari, tsaro da ingancin aiki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya mika kudurin zuwa kwamitin da ya dace domin ci gaba da nazari da shirye-shiryen daukar matakin doka na gaba.
Idan aka amince da wannan doka, za ta zama wata babbar dama wajen farfaɗo da fannin kiwon lafiya a Najeriya, da kuma dawo da amincewar jama’a ga asibitoci da Cibiyoyin kiwon lafiya cikin gida.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale da dama a fannin lafiya, ciki har da ƙarancin kayan aiki, rashin isassun ma’aikata, da kuma yawaitar cututtuka masu yaduwa.
Wannan kuduri na iya zama ginshiƙi wajen gina sabuwar makoma ga kiwon lafiya a Najeriya makoma mai cike da inganci, tsaro, da amincewa daga jama’a.



















