• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Siyasa

Kudurin Dokar Kafa Hukumar Kula da Ingancin Cibiyoyin Kiwon Lafiya Ya Tsallake Karatu Na Biyu

December 11, 2025
in Siyasa
Reading Time: 2 mins read
0
Kudurin Dokar Kafa Hukumar Kula da Ingancin Cibiyoyin Kiwon Lafiya Ya Tsallake Karatu Na Biyu
0
SHARES
15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.

A wani muhimmin mataki da ke nuni da ƙudurinta na gyara fannin kiwon lafiya a Najeriya, Majalisar Dattawa ta amince da kudurin dokar da ke neman kafa Hukumar Kula da Inganci da Tsaron Marasa Lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya a fadin ƙasar. Wannan kuduri ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar, wanda ke nuna cewa an kusa kaiwa matakin karshe na amincewa da shi.

Karanta HakananPosts

YANKIN AREWA TA ZABI HANYAR DA TAKESO: ABBAS NA JAMIYAR ADP YA GINA TSARI A KAN KANANAN HUKUMOMI 774 KAFIN 2027

Shugabar Jamiyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana

Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Ya Kare Ayyukan Majalisa Ta 10, Ya Ce Buɗaɗɗen Tsari, Gyaran Haraji da Muhimman Dokoki Dasuka Sa Majalisar Ta Kafa Tarihi Mai Kyau

Kudurin, wanda Sanata Samaila Dahuwa Kaila daga Bauchi ta Arewa ya gabatar, na da nufin daidaita tsarin bayar da kulawar lafiya, ƙarfafa tsaron lafiyar marasa lafiya, da tabbatar da cewa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu suna aiki da ingantattun ka’idoji da tsari.

Sanata Kaila ya bayyana cewa rashin gamsuwa da ayyukan kiwon lafiya a Najeriya ya sa mutane da dama ke komawa ga magungunan gargajiya, warkarwa ta addini, da shan magani ba tare da izinin likita ba.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda yan Najeriya ke yawan fita ƙasashen waje domin neman lafiya, alamar gazawar tsarin kiwon lafiya na cikin gida.

Ya ce kafa wannan hukuma za ta kawo ƙarshen sakaci da rashin bin ƙa’idoji a fannin, musamman ga waɗanda ke gudanar da ayyukan lafiya ba tare da lasisi ba, ko kuma waɗanda ke aikata laifukan cire sassan jikin marasa lafiya ba bisa ƙa’ida ba.

“Mussaman zakaji cewa an sace ma wani Koda ko kuma an cire ma wata Mata mahaifa a Asibiti ba tare da amincewar ta ba, Wannan hukumar zai Magance irin wannan matsalolin, Idan aka kama Wanda ya Aikata haka to zai fuskanci hukunci” Inji Sanata Samaila Dahuwa

Daga cikin muhimman abubuwan da kudurin ya ƙunsa akwai buƙatar takardar shaidar bin ƙa’idoji (certification) ga kowace cibiyar lafiya. Wannan zai tabbatar da cewa sabbin asibitoci za a gina su ne kawai a wuraren da ake da buƙata, kuma su cika dukkan sharuddan tsari, tsaro da ingancin aiki.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya mika kudurin zuwa kwamitin da ya dace domin ci gaba da nazari da shirye-shiryen daukar matakin doka na gaba.

Idan aka amince da wannan doka, za ta zama wata babbar dama wajen farfaɗo da fannin kiwon lafiya a Najeriya, da kuma dawo da amincewar jama’a ga asibitoci da Cibiyoyin kiwon lafiya cikin gida.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale da dama a fannin lafiya, ciki har da ƙarancin kayan aiki, rashin isassun ma’aikata, da kuma yawaitar cututtuka masu yaduwa.

Wannan kuduri na iya zama ginshiƙi wajen gina sabuwar makoma ga kiwon lafiya a Najeriya makoma mai cike da inganci, tsaro, da amincewa daga jama’a.

Previous Post

Kungiyar ECOWAS Ta Naɗa Dangote Shugaban Majalisar Kasuwanci Don Bunƙasa Tattalin Arziki

Next Post

Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci

Related Posts

YANKIN AREWA TA ZABI HANYAR DA TAKESO: ABBAS NA JAMIYAR ADP YA GINA TSARI A KAN KANANAN HUKUMOMI 774 KAFIN 2027
Siyasa

YANKIN AREWA TA ZABI HANYAR DA TAKESO: ABBAS NA JAMIYAR ADP YA GINA TSARI A KAN KANANAN HUKUMOMI 774 KAFIN 2027

August 11, 2026
Shugabar Jamiyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana
Siyasa

Shugabar Jamiyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana

August 1, 2026
Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Ya Kare Ayyukan Majalisa Ta 10, Ya Ce Buɗaɗɗen Tsari, Gyaran Haraji da Muhimman Dokoki Dasuka Sa Majalisar Ta Kafa Tarihi Mai Kyau
Siyasa

Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Ya Kare Ayyukan Majalisa Ta 10, Ya Ce Buɗaɗɗen Tsari, Gyaran Haraji da Muhimman Dokoki Dasuka Sa Majalisar Ta Kafa Tarihi Mai Kyau

July 26, 2026
Gwamna Yusuf Ya Yi Kira Ga Matasa Lauyoyi Su Rungumi Gaskiya da Adalci
Siyasa

Gwamna Yusuf Ya Sake Jaddada Kudirinsa Na Aiwatar da Tsarin Cigaban Kano

July 16, 2026
Gwamna Yusuf Ya Kai Ziyaran Gaisuwa da Girmamawa ga Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Ya Taya Shi Murna Bisa Fitowarsa a Matsayin Abokin Takaran Tinubu
Siyasa

Gwamna Yusuf Ya Kai Ziyaran Gaisuwa da Girmamawa ga Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Ya Taya Shi Murna Bisa Fitowarsa a Matsayin Abokin Takaran Tinubu

July 13, 2026
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Shugabancin LP Na Nenadi Usman
Siyasa

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Shugabancin LP Na Nenadi Usman

July 7, 2026
Next Post
Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci

Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci

Alummar Bagwai da Shanono Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Barau Jibrin a Matsayin Gwamnan Jihar Kano

Alummar Bagwai da Shanono Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Barau Jibrin a Matsayin Gwamnan Jihar Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
Mauludi: Sabunta Alkawarinmu ga Zaman Lafiya, Tausayi da Jinƙai

Mauludi: Sabunta Alkawarinmu ga Zaman Lafiya, Tausayi da Jinƙai

August 26, 2026
Mauludi: Ku yi addu’ar farfaɗowar tattalin arziki da inganta tsaro — Ashiru ya roƙi al’ummar Musulmi

Mauludi: Ku yi addu’ar farfaɗowar tattalin arziki da inganta tsaro — Ashiru ya roƙi al’ummar Musulmi

August 25, 2026
Aikin Bonga Kudu-Maso-Yamma Aparo: NNPC, Ƙungiyoyin Maƙasanta na OML 118 Sun Kulla Ƙarin Yarjejeniyar PSC da DSA

Aikin Bonga Kudu-Maso-Yamma Aparo: NNPC, Ƙungiyoyin Maƙasanta na OML 118 Sun Kulla Ƙarin Yarjejeniyar PSC da DSA

August 24, 2026
Kamfanin Dangote Cement ta yi bikin Ranar Matasa a Obajana tare da sabunta kudirin ci gaban matasa.

Kamfanin Dangote Cement ta yi bikin Ranar Matasa a Obajana tare da sabunta kudirin ci gaban matasa.

August 19, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by