Daga Bashir Bello, NASS, Abuja
A wannan tattaunawa ta musamman da wasu yan jarida da aka Zaba suka yi da shi, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya yi waiwaye kan yadda Majalisar Dokoki ta Ƙasa zango ta 10 ta gudanar da ayyukanta, inda ya bayyana shi amatsayin jajircewarta wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana, gyaran dokoki da kuma haɗa ‘yan ƙasa cikin harkokin majalisa.
Tambaya
Mai Girma Kakakin Majalisa, wannan ne karo na uku da kuke shirya irin wannan ganawa da ‘yan jarida, ‘Yan Najeriya da dama suna tambayar dalilin da ya sa kuke ci gaba da shirya waɗannan zaman. Mene ne babban manufarsa?
Kakakin Majalisa Abbas
Da farko, ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki saboda rahamarsa.
Tun bayan da na zama Kakakin Majalisar Wakilai, na ɗauki alƙawarin cewa Majalisar Wakilai za ta gudanar da ayyukanta cikin buɗaɗɗen tsari da kuma gaskiya.
Ɗaya daga cikin darussan da muka koya daga Majalisun da suka gabata shi ne cewa ‘yan Najeriya da dama ba su san abin da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ke yi ba saboda ba a isar da bayanan ayyukanmu yadda ya kamata.
Shi ya sa Majalisar Wakilai zango ta 10 ta yanke shawarar buɗe ƙofofinta ga ‘yan Najeriya.
Muna son ‘yan ƙasa ba wai kawai su san abin da muke yi ba, har ma su shiga cikin aikin ta hanyar bayar da shawarwari, gano wuraren da ke buƙatar gyara da kuma taimaka mana wajen ƙarfafa aikinmu na majalisa.
A lokacin Makon Buɗaɗɗen Majalisa (Open Week) da muka gudanar kwanan nan, mun shafe kwanaki da dama muna nazarin ayyukanmu, manufofinmu da nasarorinmu na fannin dokoki.
Mun gayyaci matasa, ƙungiyoyin mata, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula da kuma ‘yan ƙasa daga sassa daban-daban na ƙasar nan domin su tattauna kai tsaye da ‘yan majalisa.
Wannan ganawa ta yi nasara kuma ta samar mana da muhimman shawarwari da suka amfanar da Majalisar Wakilai.
Tambaya
Shin kuna tattara shawarwarin da ake bayarwa a irin waɗannan ganawa sannan ku yi amfani da su wajen aikinku na majalisa?
Kakakin Majalisa Abbas
Lallai kuwa.
Manufar ba wai kawai ita ce mu nuna abin da muka yi ba, amma domin bai wa ‘yan Najeriya damar tantance yadda muka gudanar da ayyukanmu.
Muna gabatar da ayyukanmu na fannin dokoki, ayyukan sa ido da kuma hulɗarmu da mazabu, sannan mu gayyaci mutane su yi mana suka mai ma’ana tare da bayar da shawarwari.
Harilayau, Ra’ayoyinsu da abubuwan da suka lura da su suna taimaka mana wajen inganta ayyukanmu tare da tsara abubuwan da za su kasance a sahun gaba na ayyukanmu na majalisa a nan gaba.
Tambaya
Me za ku bayyana a matsayin manyan nasarorin da Majalisar Dokoki ta Ƙasa zango ta 10 ta samu?
Kakakin Majalisa Abbas
Madalla, babu shakka majalisar Wakilai zango ta 10 ta samu gagarumin nasarori a fannin samar da dokoki a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Mun tantance tare da amincewa da ƙudirin dokoki fiye da Majalisun da suka gabata, kuma Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan adadi mafi yawa daga cikinsu fiye da yadda aka taɓa samu.
Daya daga cikin manyan nasarorin ita ce Shirin Lamunin Karatu na Ɗalibai (Student Loan Scheme), wanda ya bai wa sama da ɗaliban Najeriya miliyan ɗaya damar samun ilimi mai zurfi ba tare da hana su wannan dama ba saboda matsalolin kuɗi.
Wani muhimmin ci gaba kuma shi ne shirin gyaran haraji (Tax Reform).
Najeriya ba za ta iya ci gaba da dogaro kusan gaba ɗaya kan kuɗaɗen shiga daga man fetur ba.
An tsara gyaran harajin ne domin faɗaɗa kuɗaɗen shiga na gwamnati, inganta harkokin kuɗaɗen gwamnati da kuma ba da damar ƙarin zuba jari a hanyoyi, makarantu, asibitoci da sauran muhimman ababen more rayuwa.
An fara aiwatar da waɗannan gyare-gyare a wannan shekara, kuma muna sa ran tasirinsu na dogon lokaci zai ƙara bayyana a cikin shekaru masu zuwa.
Tambaya
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kuma ƙirƙiro Hukumomin Raya Yankuna (Regional Development Commissions). Me ya sa aka ga akwai buƙatar hakan?
Kakakin Majalisa Abbas
An kafa Hukumomin Raya Yankunan ne domin hanzarta ci gaba a yankunan siyasar ƙasar nan.
Kowane yanki yana da nasa ƙalubalen ci gaba na musamman.
Waɗannan hukumomi za su ba da damar a mai da hankali kan abubuwan da suka fi muhimmanci ga kowane yanki, tare da ƙara ƙarfafa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya.
Mun yi imanin cewa za su taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ci gaban ƙasa.
Tambaya
Batun tsaro ne ya mamaye tattaunawa a lokacin Makon Buɗaɗɗen Majalisar Dokoki ta Ƙasa (National Assembly Open Week). Mene ne manyan sakamakon da aka samu?
Kakakin Majalisa Abbas
Tsaro na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Shi ya sa muka gayyaci shugabannin hukumomin tsaro, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, Sarkin Zazzau, da tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Lucky Irabor, tare da sauran masu ruwa da tsaki.
Bayan doguwar tattaunawa, mun fitar da sanarwar ƙarshe (communiqué) mai ɗauke da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin tsaron Najeriya.
Mun kuma yi nazari kan ƙudirin dokar ‘Yan Sandan Jihohi (State Police Bill), sannan muka karɓi muhimman shawarwari daga mahalarta taron.
Tambaya
‘Yan Najeriya da dama suna nuna damuwa cewa gwamnonin jihohi na iya amfani da ‘Yan Sandan Jihohi wurin musgunawa Yan Adawa. Wani matakan kariya aka tanada?
Kakakin Majalisa Abbas
Mun yi la’akari da wannan damuwa sosai.
Ƙudirin dokar ya ƙunshi matakan daidaito da kariya (checks and balances) domin hana Amfani Dasu ta hanyar da bai dace ba.
Gwamnonin jihohi ba za su kasance da cikakken iko ba tare da iyaka kan tsarin gudanar da ‘yan sandan jihohi.
Haka kuma muna ƙarfafa ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki su yi nazarin ƙudirin dokar tare da gabatar da shawarwarinsu kafin a amince da ita a ƙarshe.
Tambaya
Majalisarku tana ba da shawarar ƙarin kujerun majalisa ga mata. Me ya sa kuka ɗauki wannan mataki?
Kakakin Majalisa Abbas
Yawan wakilcin mata a Najeriya har yanzu yana ƙasa da matakin da ya dace a tsarin dimokuraɗiyya.
Shawararmu ita ce a samar da kujerun da aka keɓe wa mata ta hanyar tsarin Kwalejin Zaɓe (Electoral College), tare da ci gaba da riƙe mazabu 360 na Majalisar Wakilai da ake da su yanzu.
Kowace jiha za ta sami ƙarin kujera guda ɗaya da za a keɓe ta ga mata kaɗai.
Hakazalika, ana ba da shawarar ƙarin kujeru 12 na Majalisar Dattawa, inda za a raba kujeru biyu ga kowace shiyya ta siyasa (geopolitical zone) bisa tsarin juyawa.
An tsara waɗannan matakan ne a matsayin na wucin gadi na tsawon shekaru 16, har sai mata sun samu damar yin takara cikin adalci a ƙarƙashin tsarin zaɓen da ake da shi.
Tambaya
Ana ganin kana da kyakkyawar alaƙar aiki da abokan aikinka Yan majalisar ba tare da saɓani ko rikici ba. Mene ne sirrin hakan?
Kakakin Majalisa Abbas
(Dariya…) Ina ganin ya kamata a yi wannan tambayar ga abokan aikina. Su ne suka fi dacewa su ba da amsa.
Sai dai, duk wani matsayin shugabanci da ka tsinci kanka a ciki, ka tabbatar da riƙon amana, gaskiya, adalci, daidaito da kuma tabbatar da adalci ga kowa.
Idan ka iya yin hakan, to za a sami zaman lafiya.
Wannan shi ne ainihin abin da muke yi a matsayin shugabannin Majalisar Wakilai.
Muna tabbatar da cewa ra’ayin kowa yana da muhimmanci, domin muna wakiltar Najeriya ne.
Tambaya
Wasu ‘yan Najeriya suna bayyana Majalisa zango ta 10 a matsayin Yan amshin shatan Shugaban Kasa Bola Tinubu. Ta yaya za ku mayar da martani kan hakan?
Kakakin Majalisa Abbas
Ban yarda da wannan ra’ayi kwata-kwata ba.
Majalisar Dokoki ta Ƙasa tana goyon bayan manufofin da muka yi imanin za su amfani ‘yan Najeriya.
Idan bangaren zartarwa ya gabatar da gyare-gyaren da suka yi daidai da ci gaban ƙasa, nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mana shi ne mu yi nazarinsu sosai kafin mu amince da su.
Haɗin gwiwa mai ma’ana tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa bai kamata a ɗauke shi a matsayin rauni ba.
A faɗin duniya, dimokuraɗiyyun da suka yi nasara suna aiki ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin waɗannan bangarori biyu na gwamnati.
Nauyinmu shi ne yi wa ‘yan Najeriya hidima, ba wai mu riƙa adawa da manufofin gwamnati saboda dalilan siyasa kawai ba.
Ma’aunin gaskiya shi ne ko dokokin da aka samar suna amfanar da jama’a.
Na shafe shekaru goma sha shida (16) ina Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Ba mu taɓa samun ƙarin kuɗaɗen ayyukan mazabu ba sai a Majalisa zango ta 9, lokacin da aka ƙara Naira miliyan ɗari (₦100,000,000).
Amma a wannan zangon mulki, wato Majalisa ta 10, Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙara wannan kuɗi zuwa Naira biliyan ɗaya (₦1,000,000,000) ga kowace mazaba domin amfanin ‘yan Najeriya.
Shin wannan ba shi ne ainihin ma’anar kyakkyawan shugabanci ba?
Mu a matsayin ‘yan majalisu bai kamata mu riƙa gaba da bangaren zartarwa ba, musamman idan bangarorin biyu suna ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ta siyasa.
Abin da ake buƙata shi ne yanayin zaman lafiya da haɗin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin ci gaban ƙasa.
Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya sake jaddada cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta 10 na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana, shugabanci mai haɗa kowa da kowa, da kuma aiwatar da gyare-gyaren da za su ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyyar Najeriya.





















