Daga Bashir Bello, Kaduna
Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa (NEMA) ta kammala rabon kwandunan abinci 24,302 da Cibiyar Tallafi da Agajin Jinƙai ta Sarki Salman (KSrelief) ta bayar ga gidaje masu rauni a jihohin Yobe, Benue, Kebbi, Anambra da Taraba.
An fara wannan agaji ne a ranar Alhamis, 18 ga Yuni, 2026, a Damaturu, Jihar Yobe, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na NEMA, Hajiya Zubaida Umar, inda aka gudanar da rabon kai tsaye ga gidaje da aka tantance a jihohin da abin ya shafa.
Sanarwar da Manzo Ezekiel ya sanya hannu a madadin Sashen Ƙafafen Yaɗa Labarai na NEMA, Abuja, a ranar 23 ga Yuli, 2026, ta bayyana cewa an raba kwandunan abinci 6,403 a Jihar Benue, 6,000 a Yobe, 4,399 a Kebbi, 4,000 a Anambra, da 3,500 a Taraba, wanda ya kai jimillar kwandunan abinci 24,302.
A wajen bikin ƙaddamarwa, Hajiya Zubaida Umar ta bayyana wannan tallafi a matsayin wani ƙarin shaida na haɗin gwiwar jinƙai mai ƙarfi tsakanin Ƙasar Najeriya da Masarautar Saudiyya ta hanyar KSrelief.
Darakta Janar ta jaddada cewa wannan agaji zai taimaka wa gidaje masu rauni tare da cike gibin ƙoƙarin jinƙai da ake yi don rage wahalhalu ga al’umman da bala’o’i, rikice-rikice, matsalolin yanayi da ƙalubalen tattalin arziki suka shafa.
Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen tunatar da al’umma game da haɗarin ambaliya a lokacin damina, inda ta shawarci jama’a su share magudanan ruwa, su guji zubar da shara a cikin hanyoyin ruwa, su bar wuraren da ambaliya ke yawan faruwa idan ya zama dole, tare da bin shawarwarin gargaɗin farko da hukumomi suka bayar.
Ta ƙara da shawartar iyaye su tabbatar da cewa yara ba sa wasa a cikin ruwan ambaliya ko wuraren da ƙasa ke lalacewa a lokacin ruwan sama mai yawa.
Hajiya Zubaida Umar ta sake jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, na inganta rayuwar ‘yan ƙasa da ƙarfafa tallafi ga al’umman da ke cikin rauni a faɗin ƙasar.
Ta yi kira ga masu cin gajiyar tallafin da su yi amfani da abincin yadda ya dace, tare da bayyana fata cewa wannan agaji zai kawo sauƙi da kwanciyar hankali ga gidajensu.A madadin KSrelief, wakilin cibiyar, Mista Majeed Alanazi, ya bayyana cewa wannan tallafi ya yi daidai da manufar cibiyar ta bayar da agaji ga al’umman da ke cikin rauni a duniya.
Ya jaddada cewa wannan mataki na nuna jajircewar KSrelief wajen ci gaba da goyon bayan al’ummar Najeriya.
Da kammala wannan aikin, dukkan kwandunan abinci 24,302 sun isa kai tsaye ga gidaje masu rauni da aka tantance a jihohi biyar, wanda ya kawo sauƙi a kan lokaci tare da ƙarfafa haɗin gwiwar jinƙai mai ɗorewa tsakanin NEMA da KSrelief.




















