Daga Bashir Bello, Abuja
Tawaga daga Gwamnatin Jihar Kano ta kai ziyarar ta’aziyya zuwa Jihar Sakkwato bisa rasuwar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji, a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Tawagar, wadda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Murtala Sule Garo, ya jagoranta, tare da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim; Sarkin Rano, Mai Martaba Muhammad Isa Umar; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa; da Kwamishiniyar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hajiya Aisha Lawan Saji, tare da wasu manyan jami’an gwamnati, ta ziyarci gidan marigayi Sardaunan Sakkwato inda suka miƙa saƙon ta’aziyyar Gwamna Yusuf ga iyalansa.
Babban dan marigayin, Aminu Abubakar Alhaji, ne ya tarbe su, inda ya gode wa gwamnan bisa nuna alhini da goyon baya a wannan lokaci na jimami.
Har ila yau, tawagar ta kai ziyara zuwa Fadar Sarkin Musulmi domin isar da saƙon ta’aziyyar Gwamna Yusuf ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku.
Sarkin Musulmin ya gode wa Gwamna Yusuf kan wannan kyakkyawan mataki, yana mai bayyana cewa hakan alama ce ta haɗin kai da ɗorewar yan’uwantaka tsakanin al’ummar Arewacin Najeriya.
Daga bisani, tawagar ta wuce zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato, inda Mataimakin Gwamnan Jihar da Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) suka tarbe su.
A nan ne suka isar da saƙon jaje da ta’aziyyar Gwamna Yusuf ga gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato bisa wannan babban rashi.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayi Sardaunan Sakkwato kura-kuransa, Ya sa shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa, Majalisar Masarautar Sakkwato da daukacin al’ummar jihar haƙurin jure wannan rashi.




















