Ya shafe sama da awa guda a Mahadar Kofar Fanfo domin tabbatar da bin fitilun zirga-zirga
Daga Bashir Bello, Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a ranar Litinin ya jagoranci sa ido da kansa kan yadda ake bin dokokin zirga-zirga a Mahadar Kofar Fanfo, inda ya shafe sama da awa guda yana tabbatar da cewa masu ababen hawa suna bin umarnin fitilun zirga-zirga.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
A yayin wannan atisaye, gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jiha, kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati, domin tabbatar da dawo da da’a da tsari a hanyoyin jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya umarci masu motocin kansu, direbobin motocin haya, masu baburan Adaidaita Sahu da masu tafiya a kafa da su bi dokokin zirga-zirga ba tare da saba ba, yana mai jaddada cewa bin umarnin fitilun zirga-zirga yana da matukar muhimmanci wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin sake fasalin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), domin ta gudanar da aikinta cikin ƙwarewa a matsayin hukuma mai kula da zirga-zirga da tabbatar da lafiyar masu amfani da hanyoyi.
Gwamnan ya ce za a ƙarfafa hukumar domin inganta kula da zirga-zirga, tabbatar da bin dokokin hanya da kuma bunƙasa al’adar biyayya ga dokokin zirga-zirga a faɗin jihar.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsarin sufuri mai aminci, tsari da inganci domin amfanin daukacin al’ummar jihar.
Gwamnan, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan sakacin da wasu masu amfani da hanya ke yi da kuma rashin bin sabbin fitilun zirga-zirgar da aka girka, ya ce bai dace a bar irin wannan gagarumin aikin da aka kashe biliyoyin naira a kansa ya zama ba a amfani da shi yadda ya kamata ba.
Ya ce, “Dole ne hukumomin da abin ya shafa su sanya ido sosai kan masu karya dokokin zirga-zirga tare da hukunta su, domin tabbatar da cewa waɗannan fitilun zirga-zirga ba su zama kayan ƙawata birni kawai ba.”




















