Daga Bashir Bello, Abuja.
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon Manufar don inganta Ilimin Almajiri, wanda ya haramta cibiyoyin karatun Almajiri daga tura dalibai yin bara a tituna.
Manufar ta gabatar da cewa ya Zama tilas karatun rubutu da lissafi, ilimin zamani na kwamfuta da kuma koyon sana’o’i a matsayin wani bangare na gyaran tsarin karatun Alkur’ani na gargajiya a kasar.
An amince da manufar a karkashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, inda ta kuma wajabta rajistar dukkan cibiyoyin karatun Almajiri, daukar bayanan biometrics na dalibai, bayar da takardar shaidar kammala karatu da kuma hukunci ga makarantu da suka karya ka’idojin.
A cewar takardar manufar, gyare-gyaren da nufin kawo karshen dogon al’adar bara da ke da nasaba da tsarin Almajiri tare da shigar da dalibai cikin tsarin ilimi na kasa ba tare da sauya asalin addinin makarantar Alkur’ani ba.
Ta ce, “Ba za a sake tura dalibi ko dalibai yin bara a titi ko yin ayyukan banza ba.”Gwamnati ta kara gargadi cewa, “Duk wata cibiyar karatu da aka yi rajista da ta tura dalibai yin bara za ta fuskanci hukunci da ya dace.”Manufar ta bayyana cewa daya daga cikin muhimman manufofinta shi ne “kawo karshen dukkan nau’o’in bara, cin zarafi da kuma wariya da ke da nasaba da Almajiri bisa ga dokokin kare hakkin yara.”
Baya ga kawo karshen bara, gwamnati ta ce za a fadada kundin karatun don bai wa dalibai ilimin asali da kuma kwarewar sana’a.
Ta bayyana cewa karatun rubutu da lissafi zai zama bangare na ilimin Almajiri a fadin kasa, tare da hada ilimin kwamfuta, koyon sana’o’i, harshen Larabci, ilimin zamantakewa da kuma kwarewar rayuwa.
Takardar ta ce, “Za a hada karatun rubutu da lissafi cikin kundin karatun Almajiri.”Ta kara da cewa, “Za a hada ilimin kwamfuta cikin horon malamai da dalibai.”Manufar ta kuma tanadar cewa dalibai zasu samu damar koyon sana’o’i da fasahar da suke so ko iyayensu suka amince da su domin inganta makomar tattalin arzikin su.
A karon farko, daliban da suka kammala karatun Almajiri a cibiyoyin da aka amince da su za su samu takardar shaidar kammala karatu.
A cewar manufar, “Za a kafa tsarin bayar da takardar shaidar kammala karatu ga dalibai ta Hukumar Kasa kan Ilimin Almajiri da Yara Masu Barin Makaranta tare da hadin gwiwar hukumomin gwamnati”. “Daliban da suka kammala karatun Almajiri za a ba su takardar shaidar kammala karatu.”
Don karfafa kulawa, gwamnati ta umarci cewa dukkan cibiyoyin karatun Almajiri a fadin kasa dole su yi rajista da hukumomin jihohi ko kananan hukumomi da ke kula da ilimin Almajiri.Haka kuma, makarantu dole su rika adana bayanan dalibai ta rubutu ko ta kwamfuta tare da bayanan biometrics.
Manufar ta ce, “Dukkan cibiyoyin karatu dole su yi rajista da hukumomin jihohi ko kananan hukumomi da ke kula da ilimin Almajiri.”Ta kara da cewa, duk wata cibiyar karatu dole ta “adana bayanan dukkan dalibai ta rubutu ko ta kwamfuta tare da bayanan biometrics.”Gyare-gyaren sun kuma gabatar da ka’idojin aiki na kowane makarantar Almajiri ta rana ko ta kwana.
A karkashin sabbin ka’idoji, dalibai dole su yi gwajin lafiya kafin a karbe su, yayin da malamai za su rika yin gwajin lafiya lokaci zuwa lokaci.Dukkan cibiyar karatu dole ta yi rajista da cibiyar lafiya ta gwamnati mafi kusa, ta rike akwatin taimakon gaggawa, ta samar da ruwa da tsafta, ta tabbatar da samun iska da kuma kauce wa cunkoso.
Gwamnati ta kuma umarci cewa a samar da wuraren karatu daban ga maza da mata tare da ka’idojin ajiya na makarantu masu kwana.Manufar ta kuma tanadi tallafin jin kai ga makarantu da aka yi rajista ta hanyar ba su kayan karatu, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, shirin ciyar da dalibai, tallafin karatu ga malamai da kuma albashi ga malamai bisa ga karfin jihohi.
Haka kuma, ta tanadi cewa Alaramma da sauran malamai su shiga cikin shirin ci gaban malamai da hukumomin gwamnati kegudanarwa.
Takardar ta bayyana cewa manufar ba ta nufi rushe tsarin Almajiri ba.“An tsara ta ba don kwace cibiyoyin karatu ba, sai dai don samar da ka’idojin aiki da tsari don tabbatar da tsaron dalibai da malamai, inganta rayuwarsu da kuma samar da tattalin arziki mai dorewa ga dalibai,” in ji ta.
Gwamnati ta danganta matsalolin da ke fuskantar tsarin Almajiri da shekaru na sakaci, barin iyaye, rashin kudade, rashin tsari da kuma kuskuren fahimta.
Ta lura cewa al’adar yara yin yawo a tituna don neman abinci da sadaka ta jefa dalibai cikin hatsarin cin zarafi da kuma kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.Manufar ta kuma ba da kulawa ta musamman ga ‘yan mata da ke shiga karatun Alkur’ani, tana amincewa cewa sun sha fama da rashin kulawa duk da fuskantar barazanar cin zarafi, sakaci, rayuwa mara kyau da kuma rashin samun damar shiga makaranta.
Gwamnatin Tarayya ta bai wa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Hukumar Kasa kan Ilimin Almajiri da Yara Masu Barin Makaranta, gwamnatocin jihohi, hukumomin ilimi na kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, iyaye, shugabannin al’umma da abokan ci gaba nauyin aiwatar da manufar.
Hukumar za ta jagoranci aiwatarwa a fadin kasa, ta kafa bayanan dalibai da malamai, ta samar da kudade, ta tabbatar da ka’idojin kare yara, ta tallafa wa jihohi wajen rajistar cibiyoyin karatu da kuma hada kai da hukumomi wajen shigar da ilimin asali, sana’o’i, ilimin kwamfuta da kwarewar rayuwa cikin tsarin Almajiri.
Manufar ta biyo bayan kafa Hukumar Kasa kan Ilimin Almajiri da Yara Masu Barin Makaranta a shekarar 2023 don jagorantar matakan magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasarnan.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da yawan yara da ba sa zuwa makaranta a duniya, inda kaso mai yawa ke da nasaba da tsarin Almajiri a arewacin Najeriya.
Kokarin gwamnati a baya, ciki har da kafa makarantu na Almajiri da shigar da karatun Alkur’ani cikin shirin Ilimin Asali na Kasa, ya samu sakamako mai gauraya saboda rashin kudade, rashin tsari da kuma rashin kulawa.
Sabuwar Manufar Kasa don Inganta Ilimin Almajiri da aka saki yanzu ana sa ran za ta samar da cikakken tsarin kasa na farko da zai jagoranci rajista, kundin karatu, jin kai, kudade, kulawa da kuma tsari na cibiyoyin karatun Almajiri a fadin kasa.




















