Daga Bashir Bello, Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa dakatar da shirin ƙara kuɗin jarabawar Hukumar jarabawa ta kasa (NECO), inda ya bayyana wannan mataki a matsayin tsoma baki mai hikima da zai rage nauyin kuɗi ga iyalan miliyoyin ‘yan Najeriya tare da tabbatar da samun ingantacciyar ilimi.
Gwamna Yusuf ya yi wannan yabo ne a ranar Talata yayin bikin kaddamar da rabon takardun naɗin aiki na dindindin ga malamai 4,900 da aka ɗauka don makarantu na firamare da sakandare, tare da ɗaukar masu taimakawa 3,688 na Abba Gida-Gida BESDA Cohort V a filin wasa na cikin gida na Sani Abacha, Kofar Mata, Kano.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano ranar Talata.
Gwamnan ya kuma yaba wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi shirin Renewed Hope Agenda da nufin inganta samun ilimi, inganci, da daidaito.
Ya yi godiya ga Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, bisa jagoranci da jajircewarsa wajen manufofin da ke tallafawa ilimi mai sauƙi da ya haɗa kowa a fadin ƙasar.
Gwamna Yusuf ya kara nuna godiya ga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Ilimin Firamare ta Ƙasa (UBEC), ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Garba, bisa goyon bayan da ba ya gushewa ga Jihar Kano, musamman sakin kuɗin haɗin gwiwa a kan lokaci wanda ya hanzarta gina da gyaran makarantu da kuma aiwatar da muhimman ayyukan ilimin firamare a fadin jihar.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada shirye-shiryen gwamnatin jihar na ƙarfafa haɗin gwiwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, UBEC, NECO, da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa jarin da ake zuba a ilimi ya haifar da ingantattun sakamako





















