Daga Bashir Bello, Abuja.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya malaman jihar Katsina da na faɗin duniya murnar Ranar Malamai ta Duniya, inda ya bayyana malamai a matsayin ginshiƙin ci gaba na gaskiya da kuma masu tsara makomar jihar.
Sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar 5 ga Oktoba, 2026, ta ce Gwamna Radda ya yaba wa malamai bisa jajircewarsu, sadaukar da kansu da kuma juriyar da suke nunawa wajen gudanar da aikinsu, yana mai cewa tasirin aikin malamai bai tsaya ga koyarwa a aji kawai ba, domin suna taka muhimmiyar rawa wajen gyara ɗabi’a, bada ilimi da samar da ’yan ƙasa masu kishin ƙasa da sanin nauyin da ke kansu.
Gwamnan ya sake jaddada cewa walwala da jin daɗin malamai na daga cikin manyan ginshiƙan ajandar gwamnatinsa ta ‘Building Your Future’, wadda ta mayar da hankali wajen ɗaukar matakai na zahiri domin dawo da martabar aikin koyarwa.
Gwamna Radda ya kuma bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta riga ta samu wajen inganta jin daɗin malamai.
Ya ce, “Biyan albashi, ƙarin girma da sauran alawus-alawus kan lokaci; biyan ƙarin alawus na musamman ga malaman da ke aiki a yankunan karkara masu wahalar isa; da kuma gina cibiyoyin horas da malamai guda uku a shiyyoyin uku na Katsina, Daura da Funtua, inda ake ci gaba da gina cibiyar Katsina.”
Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnati ta samar da babura masu amfani da lantarki guda 3,000 domin sauƙaƙa zirga-zirgar malaman da ke aiki a yankunan karkara, tare da raba na’urorin tablet domin inganta koyarwa da koyo.
Ya ce, an kuma samar wa malamai damar cin moriyar rance, baya ga ci gaba da shirye-shiryen horaswa da ƙara wa malamai ƙwarewa, yayin da wasu ƙarin tsare-tsare ke kan hanya.
Gwamna Radda ya tuna cewa a bikin Ranar Malamai ta Duniya na shekarar 2025, gwamnatin jihar ta karrama malaman da suka yi fice ta hanyar bai wa malamai 30 da suka yi zarra sabbin babura da kuma N100,000 kowannensu.
Ya ce gwamnati ta kuma bai wa shugabannin makarantu 14 da suka yi fice kyautar N200,000 kowannensu, tare da ƙarin tallafin N200,000.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ƙara bullo da wasu tsare-tsaren inganta jin daɗin malamai da kuma damar samun ƙarin ƙwarewar aiki, domin ƙara musu kwarin gwiwa da kuma inganta sakamakon koyo a makarantun gwamnati a faɗin jihar.
Ya buƙaci malamai da su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen gudanar da wannan aiki mai albarka, tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da yi musu jagora, Ya ba su ƙarfi gwiwa, sannan Ya saka musu da alheri bisa hidimar da suke yi wa al’umma.





















