
Daga BAshir Bello, Abuja
Kamfanin Simintin Dangote, reshen masana’antar Obajana, ya ƙara ƙarfafa alaƙarsa da al’ummar Jakura ta hanyar bayar da tallafin karatu ga ɗalibai, tare da tallafa wa manoma da mata ’yan kasuwa domin inganta rayuwar su da bunƙasa tattalin arzikin su.
Da yake jawabi a wajen bikin rabon tallafin da aka gudanar ranar Litinin, Daraktan Masana’antar Obajana, Injiniya Azad Nawabuddin, ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin kamfanin na cika alƙawuran da ke cikin yarjejeniyar haɗin gwiwar cigaban al’umma, wato Community Development Agreement (CDA).
Nawabuddin, wanda Shugaban Sashen Hulɗa da Cigaban Al’umma na Masana’antar Obajana, Prince Ademola Adeyemi, ya wakilta a wajen taron, ya ce shirin ya shafi ɗalibai, manoma da mata masu sana’ar kasuwanci.
Ya bayyana cewa, shirin wata alama ce ta yadda kamfanin ke ci gaba da ba da muhimmanci ga ci gaban al’ummomin da yake gudanar da ayyukansa a cikinsu, rage talauci da kuma taimaka wa jama’a su dogara da kansu ta fuskar tattalin arziki.
Daraktan ya ce, ɗalibai 20 daga manyan makarantun gaba da sakandare daban-daban sun samu tallafin karatu, yayin da wasu ɗalibai 60 na makarantun sakandare su ma suka amfana da tallafin da ya kai miliyoyin naira.
Ya kuma bayyana cewa, kamfanin ya tallafa wa manoma 20 da kayan aikin gona da kuɗaɗen gudanar da ayyukan su.
A cewarsa, an tsara shirin ne domin inganta noman amfanin gona, ƙarfafa amfani da ingantattun hanyoyin noma da kuma taimakawa wajen samar da wadataccen abinci a yankin.
Haka kuma, mata ’yan kasuwa 20 sun samu jarin fara sana’o’i da tallafin bunƙasa sana’o’insu, domin ƙarfafa kasuwancin su, ba su damar dogaro da kansu ta fuskar kuɗi da kuma ƙara kuɗin shigar iyalansu.
Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, wakilan gwamnati da shugabannin al’umma, ciki har da Mai Martaba Obaron Jakura, Oba Usman Adoga Ajibola; wakilin Olorun Oworo, Cif K. A. Mahmood, wanda shi ne Obalumema na ƙasar Oworo; Injiniya E. O. Olaitan na Ma’aikatar Bunƙasa Ma’adinai ta Tarayya; da kuma Misis A. O. Onimode ta Ma’aikatar Ma’adinai da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Kogi.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da ƙungiyoyin matasa da mata da kuma mambobin majalisar sarakunan gargajiya ta Jakura.
Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Shugaban Kwamitin Yarjejeniyar Cigaban Al’ummar Jakura, Cif Bonibade Ajiboye, ya yaba wa kamfanin Siminti. Dangote na Obajana bisa cika alƙawuran da ya ɗauka na taimaka wa al’ummar yankin.
Ya bayyana cewa baya ga shirin tallafa wa ɗalibai, manoma da ’yan kasuwa, aikin samar da wutar lantarki a yankin ya kusa kammalawa.
Cif Ajiboye ya kuma yaba wa kamfanin bisa wannan taimako, musamman ganin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin.
A yayin taron, wakilan majalisun sarakunan gargajiya na Jakura da Oworo, da kuma wakilan gwamnatin tarayya da ta jiha, sun gabatar da saƙonnin jinjina da godiya ga kamfanin bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.
A nasa jawabin, Mai Martaba Obaron Jakura, Oba Usman Adoga Ajibola, ya gode wa Allah bisa albarkata al’ummarsa da ɗimbin ma’adinai, sannan ya yaba wa Alhaji Aliko Dangote bisa zaɓen yankin a matsayin wurin zuba jari.
Sarkin ya kuma yaba wa kamfanin Simitin Dangote bisa ayyukan raya ƙasa da yake gudanarwa a yankin, yana mai cewa sabon shirin tallafin wata alama ce da ke nuna aniyar kamfanin na inganta walwala da rayuwar al’ummomin da yake gudanar da ayyukansa a cikinsu.
Ya yi alƙawarin cewa al’ummar Jakura za ta kula da ayyukan da aka gudanar domin su cigaba da amfani, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka amfana da tallafin sun yi amfani da shi yadda ya dace.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya cigaba da dafa wa Alhaji Aliko Dangote, Ya saka masa da alheri bisa karamcinsa, ayyukan taimakon jama’a da gudunmawar da yake bayarwa wajen kyautata rayuwar al’umma.




















