Daga Bashir Bello, Abuja
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa na Najeriya, NNPC Limited, ya samu ci gaba a kai a kai wajen samar da danyen mai da iskar gas, inda samar da danyen man ya kai ganga miliyan 1.67 a kowace rana a watan Afrilu na shekarar 2026.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Andy Odeh, Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC Ltd, ya sanya wa hannu, a matsayin martani ga wasu kalamai da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito daga Oil and Gas Professionals Forum (OGPF), waɗanda ke nuna shakku kan yadda shugabancin Kamfanin ƙarƙashin Babban Jami’in Gudanarwa na Rukuni, Injiniya Bayo Ojulari, yake gudanar da ayyukansa.
Kamfanin ya ce duk da cewa yana maraba da bincike da suka, wanda ya yi daidai da ƙudurinsa na tabbatar da gaskiya da bayyana gaskiya, yana da muhimmanci a fayyace wasu bayanai game da zarge-zargen da suka shafi zangon raba lasisin hakar mai da Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ta kammala kwanan nan.
NNPC Ltd ya bayyana cewa bisa tanadin Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 (PIA 2021), gudanar da zangon raba lasisin hakar mai da kuma rabon rijiyoyin mai suna ƙarƙashin cikakken ikon doka na NUPRC.
Sanarwar ta ce: “Tun bayan kafuwarta, NNPC Limited tana aiki ne kawai a matsayin kamfani na kasuwanci, kuma ba ta da ikon kula da harkokin gudanarwa ko na raba rijiyoyin mai.”
Dangane da samar da danyen mai, Kamfanin ya ce bayanan da ke akwai ga jama’a sun nuna ci gaba mai ɗorewa. A watan Afrilu na 2025, matsakaicin samar da danyen mai ya kasance ganga miliyan 1.60 a kowace rana, ciki har da condensate.
A watan Afrilu na 2026, samarwar ta ƙaru tare da daidaitawa zuwa ganga miliyan 1.67 a kowace rana, ciki har da condensate.
Wannan na nufin ƙarin ganga kusan 80,000 a kowace rana, wanda ya yi daidai da haɓakar kashi 6%.
Waɗannan alkaluma suna cikin Rahoton Ayyukan NNPC Ltd na Wata-wata, wanda ke samuwa ga jama’a.
Dangane da iskar gas kuwa, matsakaicin samarwa ya kai miliyan 7,354 na cubic feet a kowace rana (mmscfd) a watan Afrilu na 2025. Zuwa watan Afrilu na 2026, adadin ya ƙaru zuwa mmscfd 7,729, wanda ke nuna haɓakar kashi 5%.
Kamfanin ya ce wannan ci gaban na nuna ƙarin samar da iskar gas domin tallafa wa tsaron makamashin cikin gida na Najeriya da kuma cika alkawurran fitar da makamashi zuwa ƙasashen waje.
NNPC Ltd ya ce ya ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa cikin gaskiya da bayyana bayanai, kuma zai ci gaba da yin bayani a fili kan batutuwan da suka shafi ayyukansa da yadda yake gudanar da harkokinsa.
Kamfanin ya kuma ce yana da haƙƙin ɗaukar matakan da suka dace domin kare martabarsa da kuma ta shugabanninsa daga yaɗa bayanan ƙarya ko zarge-zargen da ba su da hujja.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Muna ƙarfafa masu sharhi kan harkokin masana’antu, manazarta, da ƙungiyoyin ƙwararru da su tabbatar da bayanai ta hanyoyin da suka dace na hukumomin kula da harkokin masana’antu da na kamfanoni kafin wallafa su.
Hakan zai taimaka wajen tabbatar da Lcewa ra’ayoyin da ake bayyana wa jama’a sun kasance bisa gaskiya, masu daidaito, kuma suna ba da gudummawa mai ma’ana wajen inganta fahimtar jama’a game da harkar makamashi a Najeriya.”




















