Daga Bashir Bello, Abuja
KAMFANIN Man Fetur ta Najeriya (NNPC Limited) ta tabbatar da fashewar wani bututun iskar gas mallakar wani reshenta na Kamfanin NNPC Gas Infrastructure Company Limited (NGIC), a cikin al’ummar Aleto, da ke ƙaramar Hukumar Eleme ta Jihar Rivers a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026.
A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanoni NNPC Limited, Andy Odeh, ya bayyana cewa suna cikin matukar damuwa bisa ga rahotannin raunuka da lalacewar gidaje da kasuwanci da su ka samu.
Acewar sa, tunanin su yana tare da waɗanda abin ya shafa da iyalansu domin kare rayuka da hana ƙarin lahani su ne manyan abubuwan da su ka sa gaba.
Ya ce, “NGIC ta samar da hanyoyin gaggawa na mayar da martani kuma ta ware ɓangaren bututun da abin ya shafa don iyakance ƙarin tasirin shi kuma tana aiki tare da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA), hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don daidaita alamura da kuma tantance tasirin da zai yi wa mutane, dukiya da muhalli.
“Muna kuma hulɗa da shugabannin al’umma don fahimtar buƙatun gaggawa da kuma daidaita tallafin da ya dace ga waɗanda abin ya shafa.
“A halin yanzu ana tantance musabbabin lamarin da kuma cikakken tasirinsa. Kamfanin NNPC Limited ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan kadarorinta cikin aminci da inganci.
“Za a sake duba bayanan aiki masu dacewa, gami da rahotannin da suka gabata da matakan da aka ɗauka, don tallafawa fahimtar yanayin da ke tattare da lamarin.
“Za mu ci gaba da yin aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma tantance matakan gyara da suka dace.” Inji Shi
Sanarwar ta kara da yin kira ga mazauna yankin da jama’a a kan su nisanci yankin da abin ya shafa da kuma bin umarnin tsaro daga masu ba da agajin gaggawa da hukumomin da abin ya shafa.
NNPC Limited ta ci gaba da jajircewa wajen kare lafiyar al’ummomin da su ke masaukin baki, kare muhalli da kuma gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ta ce, “za mu samar da ƙarin bayanai yayin da aka samu ingantattun bayanai.”

















