
Daga Bashir Bello, Abuja
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na gina tattalin arzikin kasuwanci mai ƙarfi, inda ya yi kira ga mata da matasa su haɓaka ƙwarewa, ƙarfi da kasuwanni da ake buƙata domin sauya tunaninsu zuwa kasuwanci mai dorewa.
Gwamna Radda ya bayyana haka a ranar Asabar a taron shugabannin kamfanoni karo na huɗu (CEOs Round Table Summit and Exhibition), wanda aka shirya a Katsina ta hanyar Initiative of Innovative Youthpreneurs Sustainable Development.

Ya bayyana kasuwanci a matsayin ikon gano matsaloli da samar da mafita masu amfani, yana mai jaddada cewa haɓaka kasuwanci na da muhimmanci ga wadata ta gida, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arziki gaba ɗaya.
Hakkan Yana kunshe ne a wata Sanarwa dauke da sa hannun
Ibrahim Kaula Mohammed
Sakataren Yaɗa Labarai na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina.
Acewar sanarwan, Gwamnan Ya yabawa da jajircewar mata ‘yan kasuwa, yana nuna yadda suke ƙara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwanci da rayuwar iyali. Gwamnan ya bayyana cewa samun kuɗi kaɗai ba ya tabbatar da nasarar kasuwanci.

A cewarsa, ‘yan kasuwa suna buƙatar ƙwarewa ta musamman, kasuwanni masu amfani da kuma kuɗaɗe domin gina kamfanoni da za su iya tsayawa tsayin daka bayan matakin farko.
“Mahimman abubuwa sune ƙwarewa, kasuwa da kuɗi,” in ji Radda, yana mai tabbatar wa ‘yan kasuwa da suka cika sharudda cewa Gwamnatin Jihar za ta ci gaba da tallafa musu, musamman mata.
Gwamna Radda ya danganta shiga cikin ayyukan tattalin arziki da tsaro da zaman lafiya, yana mai lura cewa samar da damar tattalin arziki ga matasa na rage zaman banza da wasu matsalolin zamantakewa da ke haifar da rashin tsaro.
Ya ƙarfafa matasa ‘yan kasuwa kada su yi watsi da sana’o’in hannu da na gargajiya, sai dai su inganta su, su ƙara ƙwarewa da kuma gina kasuwanni masu amfani a kan kayayyakinsu.

A baya, mai shirya taron shugabannin kamfanoni, Lubabatu Umar Ahmed, ta ce an ƙirƙiri wannan shiri ne domin haɗa ‘yan kasuwa da tunani, damar kasuwanci da shugabannin kamfanoni wainda sukayi nasara domin daga gare su za su iya koyo.
Ta yaba da yadda gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Radda ta tallafa wa kananan da matsakaitan kamfanoni, tana mai
cewa tsare-tsaren da aka gudanar ta hukumomi da shirye-shirye ciki har da KASEDA, Ma’aikatar Mata da Ilimin ‘Ya’ya Mata sun tallafa wa mutane 17,400 a Jihar Katsina.
Lubabatu Ahmed ta ce taron ya wuce kawai haɗa ‘yan kasuwa wuri ɗaya, yanzu yana mai da hankali kan taimaka wa mahalarta wajen gano damar da za su iya sauya tunaninsu zuwa kasuwanci Wanda zaa samu nasara.
Ta bayyana wannan karo na huɗu a matsayin wani mataki na haɓaka sabuwar ƙarni na ‘yan kasuwa da za su iya gina kasuwanci daga Katsina su kuma iya yin gogayya har wajen Jihohi da Najeriya.
Mai ba da shawara ta musamman ga Gwamna kan harkokin banki da kuɗi, Bilkisu Suleiman Ibrahim, wacce ta wakilci Uwargidan Gwamna, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, ta yi kira ga matasa ‘yan kasuwa da su rungumi fasaha, jagoranci da haɗin kuɗi yayin da suke amfani da tallafin gwamnati da haɗin gwiwa.
Ta bayyana taron a matsayin muhimmin dandali na haɗa shugabannin kasuwanci, masu kirkire-kirkire da matasa ‘yan kasuwa, yana buɗe ƙofofi zuwa haɗin gwiwa da sabbin damar kasuwanci.
Haka kuma, Kwamishinan Noma, Hon. Aliyu Lawal Zakari Shargalle, ya jaddada yadda gwamnatin ke zuba jari a ƙwarewar aiki da haɓaka kasuwanci.
Ya bayyana cewa matasa 120 sun samu horo a ƙarƙashin shirin Songhai a shekara ta farko, sai 361 a shekara ta biyu, sannan wasu 361 suna ci gaba da horo yanzu, wanda ya kai fiye da masu cin gajiyar 800.
Ya ƙara da cewa masu cin gajiyar suna samun kuɗin farawa da tallafi bayan kammala horo.
Kwamishinan ya ƙara bayyana cewa kusan matasa 700 maza da mata suna ci gaba da samun ƙarin horo na ƙwarewa da ilimi, tare da gwamnati tana samar da tallafin kuɗi, kayan aiki na zamani da kuma alawus na kowane wata domin taimaka musu su yi nasara.
A nata jawabin, Kwamishinan Mata, Hajiya Aisha Aminu Abdullahi Malumfash ta ce gwamnatin na faɗaɗa damar tattalin arziki ga mata ta hanyar shirin Nigeria for Women Project.
Ta sanar da cewa mata fiye da 4,000 za su nuna kasuwancinsu a baje kolin da aka shirya ranar 6 ga Oktoba, yayin da mata 2,200 za su samu tallafi. Ta ƙara da cewa an riga an kafa ƙungiyoyin mata 1,700 a ƙarƙashin shirin.
Taron shugabannin kamfanoni ya haɗa jami’an gwamnati, shugabannin kasuwanci, ‘yan kasuwa, masu kirkire-kirkire da sauran masu ruwa da tsaki domin musayar ra’ayi, gina dangantaka da gano damar haɓaka kasuwanci mai dorewa a Jihar Katsina.





















