
Daga Bashir Bello, Abuja.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta samu manyan nasarori cikin makonni biyu da suka gabata, inda ta kama mutane 16 da ake zargi da garkuwa da mutane, ta hallaka wasu fitattun ‘yan bindiga, tare da kwato kadarorin da aka sace na daruruwan miliyoyin naira a sassa daban-daban na jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, 4 ga Agustan 2026, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, psc, mni, ya bayyana cewa wadannan nasarori sun samu ne sakamakon ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin tarwatsa kungiyoyin masu aikata laifuka da ke barazana ga zaman lafiya a jihar Kaduna.
CP Rabiu Muhammad ya bayyana cewa a cikin wannan lokaci, jami’an rundunar sun kwato bindigogi guda 10 na nau’o’i daban-daban, inverter na hasken rana guda 190 da darajarsu ta kai Naira miliyan 69, batirin lithium guda 10 da darajarsu ta kai Naira miliyan 9, shanu 410, wayoyin hannu 32 da aka sace, talabijin na plasma guda biyu, mota guda daya da aka sace, da kuma kunshi 83 na haramtattun kwayoyi.
Ya bayyana wasu muhimman nasarori, ciki har da kama Aisha Barau mai shekaru 20 daga kauyen Ramin Kura a ranar 21 ga Yuli, dauke da takardun dalar Amurka na bogi.
Bayan amsa laifin, jami’ai sun kama Abdullahi Muhammad mai shekaru 55 da Danbala Jibrin mai shekaru 57, wadanda ake zargin su ne suka samar mata da kudin bogin.
A ranar 25 ga Yuli kuma, Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane ya kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai, Luka Samuel mai shekaru 38, John Paul mai shekaru 37 da Musa Elisha mai shekaru 28 a Jos, Jihar Filato.
An kwato bindigogi biyu kirar gida daga hannunsu, kuma sun amsa cewa suna kai wa ‘yan bindiga makamai.
A wani samame da aka kai ranar 24 ga Yuli a kauyen Kargi, hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda da kungiyar ‘Yan Sa Kai ta yi sanadin kama Abdullahi Mohammed wanda aka fi sani da “Aala”, mai shekaru 34, wanda ake zargin jagora ne wajen garkuwa da mutane a yankin Kuzuntu da ke Karamar Hukumar Ikara.
Ya amsa cewa yanada hannu a kashe mambobi biyu na ‘Yan Sa Kai a bara. An kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da harsasai guda biyar.
Har ila yau, rundunar ta kwato wata mota kirar Toyota Sienna da aka sace daga wani masallaci a Unguwan Rimi bayan kama Mohammed Shehu a Zariya.
Bayan amsa laifinsa ne aka kama Zakari Abubakar, wanda ake zargin kwararre ne wajen kera kwafin makullan motoci.
A ranar 26 ga Yuli, jami’an ‘yan sanda a Zariya sun dakile wani yunkurin satar shanu a kauyen Damanko, inda suka kwato shanu 80 da tumaki 10 bayan musayar wuta da masu laifin.
Mutane biyu da suka samu raunuka sakamakon harin suna ci gaba da karbar magani.
A ranar 28 ga Yuli kuma, jami’an rundunar sun gano wani ma’ajiya a Zariya dauke da kayan aikin hasken rana da aka sace, wadanda darajarsu ta kai Naira miliyan 78. Ana zargin cewa an karkatar da kayan ne yayin da ake jigilar su.
A karshe, a ranar 31 ga Yuli, an kama Alex Odoh mai shekaru 36 da Daniel Eze mai shekaru 35 a Kasuwar Magani bisa zargin samar wa ‘yan bindiga haramtattun kwayoyi.
CP Rabiu Muhammad ya yabawa jami’an rundunar bisa jarumtaka da kwarewar da suka nuna wajen gudanar da ayyukansu.
Ya sake jaddada kudirin rundunar na ci gaba da bin masu aikata laifuka ba tare da sassauci ba, tare da rokon al’umma su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri a kan lokaci.
Ya ce, “Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna na aiki tukuru domin tabbatar da cewa jihar ta kasance cikin aminci ga daukacin al’umma. Muna aiki tare da rundunar soji, Hukumar DSS, NSCDC, kungiyoyin ‘yan sa kai da sauran hukumomin tsaro domin cimma wannan buri.”
Ya kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.



















