
Daga Bashir Bello, Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa na Najeriya, Mai Girma Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa), ya yi ta’aziyya ga al’ummar masarautar Bungudu da sauran al’ummomi a jihar Zamfara kan matsalolin tsaro da asarar rayuka da suka faru kwanan nan.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya samu wakilci a wajen tarurrukan ta’aziyyar daga ɗan takarar kujerar Sanata a Zamfara ta Tsakiya, karkashin Jamiyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar Saleh Ruwandoruwa, kuma Baraden Maru.
A yayin ziyarar, Baraden Maru ya isar da sakon ta’aziyya na Alhaji Atiku Abubakar da dukan Yan Jamiyar ADC ga jama’ar jihar.
Ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa, dawowar waɗanda akayi garkuwa da su lafiya, da kuma ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa.
Ziyarar farko ita ce ta’aziyya zuwa fadar Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Atto, bayan harin da aka kai garin Bungudu. Wannan lamari ya jawo sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu wanda har yanzu yana hannun masu garkuwa da Mutane da kuma kisan jami’an tsaro a bakin aiki.
A lokacin ziyarar, Baraden Maru ya isar da saƙon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, inda ya yi addu’ar rahama ga rayukan jami’an tsaron da suka rasu, da kuma roƙon Allah ya kubutar da shugaban ƙaramar hukumar da aka sace cikin gaggawa da lafiya.
Harila yau, Ɗan takarar Sanatan ya kuma ziyarci Sarkin Maru tare da kai ziyara ta gida zuwa garinsu Ruwan Doruwa a ƙaramar hukumar Maru, inda ya yi gaisuwar ban girma ga mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwa. Ya ce wannan ziyara ce ta neman addu’o’i da albarka kafin zaɓen 2027.
Haka kuma, Baraden Maru ya ziyarci ƙaramar hukumar Tsafe domin yin ta’aziyya ga shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Garba Shehu Fanchers, kan rasuwar mahaifiyarsa. Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ba ta Aljannatul Firdaus, ya kuma ba iyalan hakuri wajen jure wannan rashi.

Wannan jerin ziyarce-ziyarcen na nuna jajircewar ‘yan takarar ADC wajen nuna tausayi, haɗin kai, da jagoranci na gari, tare da ƙudirin jam’iyyar na tsayawa tare da jama’ar Zamfara a lokutan baƙin ciki.




















