
Janar Manajan Sashen Ayyukan Jama’a na Kamfanin Dangote Cement, reshen Obajana, Ademola Adeyemi yana ba wani dalibi kayan karatu a Makarantar primary ta UBE LGEA, St. Luke Model II, Adankolo, Karamar Hukumar Lokoja a karshen mako.
Daga Bashir Bello, Abuja
Kamfanin Dangote Cement Plc, reshen Obajana, ya ƙara faɗaɗa ayyukansa na tallafa wa al’umma ta hanyar raba kayan karatu ga ɗalibai a birnin Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.
Babban Manajan Sashen Ayyukan Zamantakewa na Kamfanin Dangote Cement, reshen Obajana, Ademola Adeyemi, ya bayyana cewa wannan wani ɓangare ne na ci gaba da shirye-shiryen Nauyin da Kamfani ke ɗauka na Tallafa wa Al’umma (Corporate Social Responsibility – CSR).
A cewarsa, wannan tallafin ilimi da aka kai Lokoja ya biyo bayan irin wannan rabon kayan karatu da Kamfanin Dangote Cement Plc ya yi wa ɗaliban makarantun gwamnati da ke al’ummomin Oyo, Iwaa, Obajana da Apata.
Haka kuma, kamfanin ya ƙaddamar da wani asibiti na miliyoyin nairori a Obajana, wanda ya ƙara cikin jerin manyan ayyukan ci gaban al’umma da suka haɗa da wasu asibitoci da aka gina a baya a al’ummomin Iwaa da Oyo.
Harila yau, Ya bayyana cewa, tsawon shekaru, kamfanin ya zuba biliyoyin nairori wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’ummomin da ke karɓar baƙuncinsa.
Waɗannan sun haɗa da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki, gina hanyoyi da samar da ruwan sha mai tsafta. Ya kuma jaddada cewa kamfanin na ci gaba da jajircewa wajen faɗaɗa da kuma dorewar waɗannan ayyuka.
A cewar sa shirye-shiryen CSR na kamfanin sun yi daidai da manufofin ci gaban gwamnati, kuma ana aiwatar da su ne ta hanyar haɗin gwiwa mai ɗorewa da amfani ga kowane ɓangare.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar kuma aka bai wa manema labarai a Lokoja, an ce:
“Kayan karatun da aka raba sun haɗa da jakunkunan makaranta, littattafan rubutu, kayan rubutu, kwalaben ruwa da sauran muhimman kayan koyo da nufin inganta koyon ɗalibai tare da shirya su domin zangon karatu na gaba.”
USanarwar ta ci gaba da cewa:
“An aiwatar da wannan shiri ne bayan binciken tantance buƙatu da Kamfanin Dangote Cement Plc ya gudanar. Binciken ya nuna cewa ɗalibai da dama suna zuwa makaranta ba tare da jakunkunan makaranta ba, yayin da wasu ke riƙe littattafansu da hannu.
Haka kuma an gano cewa ɗalibai da yawa ba su da muhimman kayan karatu kamar littattafan rubutu, alƙaluma, fensir da sauran kayan koyo na yau da kullum.”
Da yake jawabi, Babban Malamin Makarantar UBE LGEA School, St. Luke Model II, Adankolo, a Ƙaramar Hukumar Lokoja, Abubakar Sanni, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga mahukuntan Kamfanin Dangote Cement Plc bisa wannan kyakkyawan tallafi.
Babban Malamin ya kuma gode wa Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, saboda faɗaɗa shirin tallafin ilimi na kamfanin zuwa makarantun da ke babban birnin jihar, ba wai kawai ga al’ummomin da kamfanin ke gudanar da ayyukansa ba.
Daga Cikin Waɗanda suka amfana da tallafin, akwai shugabannin makarantu, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a al’umma sun kuma bayyana godiyarsu ga Kamfanin Dangote Cement Plc bisa wannan taimako da ya zo a kan lokaci.
Sun kuma yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba kamfanin nasara da bunƙasa a ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma da kuma tallafa wa ci gaba mai ɗorewa.





















