• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Ƙasashen Duniya

Sarkin Kano, Hajiya Fatima Sun Ƙarfafa ‘Yan Kano Su Mallaki Hannun Jarin Dangote Refinery Domin Gina Makomar Tsararraki

September 20, 2026
in Ƙasashen Duniya
Reading Time: 2 mins read
0
Sarkin Kano, Hajiya Fatima Sun Ƙarfafa ‘Yan Kano Su Mallaki Hannun Jarin Dangote Refinery Domin Gina Makomar Tsararraki
0
SHARES
15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daga Bashir Bello, Abuja.

Karanta HakananPosts

Idi Hong: IPO na Matatar Dangote Yana Bunkasa Tattalin Arzikin Alumma.

Dangote Ya Dauki Nauyin Bikin Baje kolin Kasuwanci Na Abuja

Sarkin Kano Ya Bayyana IPO na Matatar Dangote a Matsayin “Komawa Gida”, Ya Yi Kira ga Al’ummar Kano Su Zuba Jari

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II (PhD) da Daraktar Yanki kuma Babbar Mashawarcin Aliko Dangote, Hajiya Fatima Wali Abdurrahman, sun yi kira ga al’ummar Kano da su yi amfani da damar sayen hannun jarin Dangote Refinery wajen gina dukiya da samar da makoma mai inganci ga kansu da ‘ya’yansu.

Yayin da Mai Martaba Sarkin Kano ya mai da hankali kan buƙatar ‘yan Kano su shiga cikin kasuwar hannun jari (Capital Market), Hajiya Fatima ta jaddada muhimmancin iyaye su fara tunanin makomar ‘ya’yansu ta hanyar zuba musu hannun jarin da zai iya bunƙasa rayuwarsu nan gaba.

Sarkin ya bayyana cewa mutanen Kano sun daɗe suna a harkokin kasuwanci da samar da arziki, amma ba su cika shiga kasuwar hannun jari ba kamar yadda suke shiga sauran harkokin kasuwanci.

Saboda haka, ya ƙarfafa su da su yi amfani da wannan dama ta Dangote Refinery, yana mai cewa kamfanin da Aliko Dangote ya kafa yana da alaƙa ta musamman da Kano, domin shi ɗan Kano ne.

Ya ce: “Dangote Refinery tamu ce. Aliko Dangote namu ne. Kuma Shi ɗan Kano ne.”

Mai Martaba ya bayyana cewa shiga hannun jarin ba wai kawai batun sayen wani abu ba ne, illa wata dama ce ta mallakar wani ɓangare na babban kamfani da kuma koyon wata sabuwar hanyar gina dukiya.

A nata ɓangaren, Hajiya Fatima Wali Abdurrahman ta mayar da hankali kan makomar ‘ya’ya, inda ta shawarci iyaye da su yi la’akari da sayen hannun jari domin ‘ya’yansu, su bar jarin ya bunƙasa tare da lokaci.

Ta ce irin wannan tanadi zai iya taimakawa wajen biyan bukatun ‘ya’ya a nan gaba, musamman wajen ilimintar da su da gina rayuwarsu.

Hajiya Fatima ta kawo misalin yadda Aliko Dangote ya gina makomar ‘ya’yansa ta hanyar ba su ingantaccen ilimi, tarbiyya, da horo a harkokin kasuwanci, inda a yau suke rike da mukaman daraktoci a sassa daban-daban na kamfanoninsa.

Ta ce iyaye ba sai sun sayar da gidaje, gonaki ko wasu kadarorinsu ba kafin su fara zuba jari.

Maimakon haka, ta bukaci su fara da abin da suke da shi, gwargwadon ƙarfinsu, domin su samu damar gina abin da zai iya zama wani ɓangare na makomar ‘ya’yansu.

“Ba sai kun sayar da kadarorinku ba. Ku fara da abin da kuke da shi, gwargwadon ƙarfinku. Ku yi wannan zuba jarin domin makomar ‘ya’yanku, kuma da yardar Allah ba za ku yi nadama ba,” in ji ta.

A yayin da Sarkin Kano ya ƙarfafa al’umma su faɗaɗa sanin kasuwancinsu zuwa kasuwar hannun jari, Hajiya Fatima ta nuna yadda irin wannan zuba jari zai iya zama wani ɓangare da iyaye zasu tanadar wa ‘ya’yansu makoma.

Previous Post

Sarkin Kano Ya Bayyana IPO na Matatar Dangote a Matsayin “Komawa Gida”, Ya Yi Kira ga Al’ummar Kano Su Zuba Jari

Next Post

Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano

Related Posts

Idi Hong: IPO na Matatar Dangote Yana Bunkasa Tattalin Arzikin Alumma.
Ƙasashen Duniya

Idi Hong: IPO na Matatar Dangote Yana Bunkasa Tattalin Arzikin Alumma.

October 2, 2026
Dangote Ya Dauki Nauyin Bikin Baje kolin Kasuwanci Na Abuja
Ƙasashen Duniya

Dangote Ya Dauki Nauyin Bikin Baje kolin Kasuwanci Na Abuja

September 30, 2026
Sarkin Kano Ya Bayyana IPO na Matatar Dangote a Matsayin “Komawa Gida”, Ya Yi Kira ga Al’ummar Kano Su Zuba Jari
Ƙasashen Duniya

Sarkin Kano Ya Bayyana IPO na Matatar Dangote a Matsayin “Komawa Gida”, Ya Yi Kira ga Al’ummar Kano Su Zuba Jari

September 18, 2026
Tasirin Ayyukan ADF Ya Yi Matukar Tasiri Inji Ƙungiyar MAN da Sauransu
Ƙasashen Duniya

Tasirin Ayyukan ADF Ya Yi Matukar Tasiri Inji Ƙungiyar MAN da Sauransu

September 3, 2026
Kamfanin Dangote Cement Ta Ƙara Himma Wajen Tallafa wa Ilimi a Jihar Kogi
Ƙasashen Duniya

Kamfanin Dangote Cement Ta Ƙara Himma Wajen Tallafa wa Ilimi a Jihar Kogi

August 2, 2026
‎Kamfanin Siminti na Dangote dake Gboko Ta Kaddamar Da Shirye-shiryen Tallafi Na Miliyoyin Naira Ga Al’ummomin dake  yankin Masaukin ta a Benue
Ƙasashen Duniya

‎Kamfanin Siminti na Dangote dake Gboko Ta Kaddamar Da Shirye-shiryen Tallafi Na Miliyoyin Naira Ga Al’ummomin dake  yankin Masaukin ta a Benue

May 20, 2026
Next Post
Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano

Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano

NNPC Ltd Ta Yi Maraba Da Shawarar Karshe I’ma Gas Na Zuba Jarin Dala Miliyan 800

NNPC Ltd Ta Yi Maraba Da Shawarar Karshe I'ma Gas Na Zuba Jarin Dala Miliyan 800

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

October 14, 2026
Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

October 13, 2026
Auto Draft

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

October 8, 2026
Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Sakatarorin Dindindin Hudu

Ranar Malamai ta Duniya: Ba Za Mu Bar Malaman Katsina Su Yi Aiki Cikin Wahala Ba – Gwamna Raɗɗa

October 7, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin