• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Kasuwanci

Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano

September 25, 2026
in Kasuwanci
Reading Time: 4 mins read
0
Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano
0
SHARES
8
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daga Bashir Bello, Abuja

’Yan masana’antu ƙarƙashin ƙungiyar Manufacturers Association of Nigeria (MAN) sun yi cincirindo a rumfar Kamfanin Dangote Group da ke wajen baje kolin, domin neman bayani da ƙarin haske kan Bayar da Hannun Jari ga Jama’a ta Farko (IPO) da ake gudanarwa a halin yanzu na Matatar Man Fetur da Petrochemicals ta Dangote (DPRP).

Karanta HakananPosts

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote

Babban Taron Shekara-shekara (AGM) na kwanaki uku na reshen Kano-Jigawa na ƙungiyar MAN, wanda shi ne karo na 54, ya ƙare a ranar Alhamis.

A yayin taron, wakilin Dangote Group ya karɓi mahalarta tare da tattaunawa da ’yan masana’antu waɗanda suka nuna matuƙar sha’awa kan shirin IPO na Matatar Dangote da ake gudanarwa a halin yanzu.

IPO na Matatar Dangote yana bai wa ’yan Najeriya da sauran masu zuba jari da suka cancanta damar sayen hannun jari a Matatar Man Fetur da Petrochemicals ta Dangote, ta yadda za su zama masu mallakar wani kaso na ɗaya daga cikin manyan ayyukan masana’antu a Afirka, tare da samun damar cin gajiyar ci gabanta a nan gaba.

Shirin IPO na Matatar Dangote an fara gudanar dashi ne daga 14 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan Oktoba, 2026.

Dangote Industries Limited na daga cikin masu ɗaukar nauyin taron AGM na MAN karo na 54.

Tun da farko, a jawabin buɗe taron, Shugaban Ƙungiyar Manufacturers Association of Nigeria (Masu kere kere ta Ƙasa MAN), reshen Sharada/Challawa, Alhaji Nura S. Madugu, ya bayyana damuwar da ake ciki game da ƙarin nauyin haraji, kuɗaɗen caji da sauran levis da ake ɗora wa ’yan masana’antu, yana mai gargadin cewa lamarin na ƙara tsadar gudanar da kasuwanci tare da rage ƙarfin gasa na masana’antun cikin gida.

Madugu ya roƙi Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya da su rage wa ’yan masana’antu nauyin haraji tare da hanzarta ƙoƙarin daidaita haraji da kuɗaɗen levies da ake karɓa daga ’yan kasuwa.

Ya yi tir musamman da tsarin biyan haraji sau biyu ko fiye da haka, inda ya ce hakan na ci gaba da ƙara matsin tattalin arziki ga ’yan masana’antu waɗanda tuni suke fama da tsadar makamashi, ƙarancin ababen more rayuwa, tsadar samun kuɗin jari, rashin tsaro, matsalolin canjin kuɗaɗen waje da kuma gasar da ba ta dace ba daga kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje.

“Muna matuƙar damuwa da yadda ake samun yanayi na biyan haraji sau biyu, har ma fiye da haka, inda matakai uku na gwamnati ke ɗora irin wannan haraji ne kawai amma a ƙarƙashin sunaye da hanyoyi daban-daban. Wannan tsari yana jefa kayayyakinmu cikin babban rashin daidaito a kullum yayin da suke fafatawa da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Wannan matsalar kuma tana ƙara muni saboda tsadar samar da wutar lantarki ta madadin da kuma sauye-sauyen farashin canjin kuɗin waje.”

Madugu ya tunatar da taron irin gagarumar gudunmawar da MAN ke bayarwa ga al’umma, musamman wajen samar da ayyukan yi ga dubban ’yan Najeriya, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen samar da kuɗaɗen shiga na haraji ga ƙasa.

Ya ce:
“Muna samar da ayyukan yi ga dubban ’yan Najeriya. Muna taka rawa sosai wajen samar da kuɗaɗen shiga na haraji ga jihohi da Gwamnatin Tarayya ta hanyar cire VAT daga cikin kayayyakinmu, tura kuɗin Pay-As-You-Earn (PAYE) a madadin ma’aikatanmu, da kuma biyan Withholding Tax, Education Tax, Tertiary Education Tax, Company Income Tax, da kuma wasu levies da dama waɗanda ba za a iya ambaton su ɗaya bayan ɗaya ba.

“Baya ga batun haraji, muna kuma cika nauyinmu na Corporate Social Responsibility (CSR) yadda ya kamata ga al’ummomin da muke gudanar da ayyukanmu a cikinsu.

“Ko da yake abin da muke samu a madadin waɗannan gudunmawa ba shi da yawa, muna ci gaba da yi wa wannan ƙasa hidima da ƙwazo da kyakkyawar niyya, tare da tallafa wa tattalin arzikinta.

Muna yin hakan ne saboda mun yi imani da Najeriya da Jihar Kano. Amma dole ne a faɗi gaskiya a sarari,” in ji Madugu.

A nasa jawabin, Shugaban MAN na reshen Bompai/Jigawa, Mohammed Bello I. Umar, ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa jajircewarsu, sadaukarwarsu da ci gaba da zuba jari a tattalin arzikin Najeriya duk da ƙalubalen da ake fuskanta wajen gudanar da harkokin kasuwanci.

Ya bayyana cewa taron ya ba mambobin ƙungiyar damar yin nazari kan ayyukanta, duba ƙalubalen da ke fuskantar kasuwancinsu, amincewa da ci gaban da suka samu, tare da tsara wata hanya mafi ƙarfi domin bunƙasa harkar masana’antu a ƙasar nan a nan gaba.

Sai dai ya ce dole ne mambobin su amince cewa har yanzu harkar masana’antu na fuskantar matsananciyar barazana.

Ya bayyana cewa tsadar makamashi, yawan haraji da levies, ƙarancin ababen more rayuwa, tsadar samun kuɗin jari, rashin tsaro, matsalolin canjin kuɗin waje da kuma gasar da ba ta dace ba daga kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje na ci gaba da shafar ƙarfin gasa na masana’antun cikin gida.

“Ɗaya daga cikin batutuwan da ke buƙatar kulawarmu gaba ɗaya shi ne shigo da kayayyakin haram da marasa inganci. Waɗannan kayayyaki suna raunana ’yan masana’antun cikin gida waɗanda ke zuba jari mai yawa…” Inji Shi

Ya ƙara da cewa:
“Samun ingantacciyar wutar lantarki mai araha na daga cikin muhimman abubuwan da ake buƙata domin bunƙasa masana’antu.”

Sai dai ya yi maraba da sauye-sauyen da ake yi a fannin wutar lantarki, da kuma ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar ke yi wajen samar da ingantaccen tsarin wutar lantarki a jihar.

Ya yi kira da a gaggauta aiwatar da sauye-sauyen da za su samar da kasuwar wutar lantarki mai inganci, gasa da kuma araha ga masana’antu.

Ya bayyana cewa ’yan masana’antu na ci gaba da samar da ayyukan yi, samar da arziki, tallafa wa al’ummomin yankunansu da kuma bayar da muhimmiyar gudunmawa ga kuɗaɗen shiga na gwamnati ta hanyar samar da kayayyaki,
ɗaukar ’yan Najeriya aiki da kuma bin ƙa’idojin gwamnati.

Ya ce:
“Saboda haka dole ne mu tsaya tsayin daka tare mu yi kira da a ƙara tsaurara matakan sa ido da aiwatar da dokoki a kan iyakokin ƙasa da kasuwanni.

Ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da fasa-ƙwaurin kaya, jabun kayayyaki da shigo da kayayyakin da ke yin gasa ba bisa ƙa’ida ba da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.

Previous Post

Sarkin Kano, Hajiya Fatima Sun Ƙarfafa ‘Yan Kano Su Mallaki Hannun Jarin Dangote Refinery Domin Gina Makomar Tsararraki

Next Post

NNPC Ltd Ta Yi Maraba Da Shawarar Karshe I’ma Gas Na Zuba Jarin Dala Miliyan 800

Related Posts

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026
Kasuwanci

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

October 14, 2026
Auto Draft
Kasuwanci

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

October 8, 2026
Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote
Kasuwanci

Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote

October 4, 2026
Dangote: Ci Gaban Tattalin Arzikin Najeriya Ya Danganta da Ƙara Samar da Kayayyaki a Cikin Gida.
Kasuwanci

DANGOTE: ƘARFAFA ƘERA KAYAN AMFANI A CIKIN ƘASA ITA CE HANYAR SAMUN ƘARFIN TATTALIN ARZIKI MAI DOREWA A NIJERIYA

October 4, 2026
Kamfanin Dangote Cement ta yi bikin Ranar Matasa a Obajana tare da sabunta kudirin ci gaban matasa.
Kasuwanci

Kamfanin Dangote Cement ta yi bikin Ranar Matasa a Obajana tare da sabunta kudirin ci gaban matasa.

August 19, 2026
Kamfanin Siminti na Dangote Ta Fara Amfani da Fasahar AI da Telematics Don Ƙarfafa Tsaron Sufuri
Kasuwanci

Kamfanin Siminti na Dangote Ta Fara Amfani da Fasahar AI da Telematics Don Ƙarfafa Tsaron Sufuri

June 7, 2026
Next Post
NNPC Ltd Ta Yi Maraba Da Shawarar Karshe I’ma Gas Na Zuba Jarin Dala Miliyan 800

NNPC Ltd Ta Yi Maraba Da Shawarar Karshe I'ma Gas Na Zuba Jarin Dala Miliyan 800

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited) ya sanar da samun ribar ₦7.2 tiriliyan bayan cire haraji a shekarar kuɗi ta 2025,

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

October 14, 2026
Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

October 13, 2026
Auto Draft

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

October 8, 2026
Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Sakatarorin Dindindin Hudu

Ranar Malamai ta Duniya: Ba Za Mu Bar Malaman Katsina Su Yi Aiki Cikin Wahala Ba – Gwamna Raɗɗa

October 7, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin