Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.
Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanar da shirin haɗin gwiwa da fitaccen ɗan kasuwa na Afirka, Aliko Dangote, da sauran ɓangarorin masu zaman kansu domin ƙarfafa daidaiton kuɗi da ƙarfin tattalin arziki a yankin.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya bayyana wannan shiri a zaman taron ministocin ECOWAS karo na 95 da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.
Touray ya bayyana cewa an zaɓi Dangote a matsayin shugaban farko na Majalisar Kasuwanci ta ECOWAS, wata sabuwar dandalin da aka ƙirƙira domin jawo jari daga ɓangaren masu zaman kansu da kuma tallafa wa haɗin gwiwar tattalin arzikin yankin.
Ya ce: “Muna ci gaba da aiwatar da Majalisar Kasuwanci ta ECOWAS. Mun zaɓi Alhaji Aliko Dangote a matsayin shugaban farko na wannan majalisa saboda ƙwarewarsa da gogewarsa a harkokin kasuwanci a cikin yankinmu, Africa da ma fadin Duniya.
“Ta wannan majalisa, muna fatan haɗa ɓangarorin masu zaman kansu domin tattauna haɗin gwiwar tattalin arziki da ci gaban yankinmu.
“Majalisar Kasuwanci za ta bunkasa tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren masu zaman kansu, gwamnatoci da hukumomin ECOWAS.”
Hukumar ECOWAS na ƙoƙarin rage dogaro da jari daga ƙasashen waje ta hanyar ƙarfafa zuba jari a tsakanin ƙasashen yankin.
Touray ya ce: “Wannan sha’awar zuba jari a cikin yankinmu na nuna muhimmancin tara jari daga cikinmu domin gina al’ummarmu maimakon jiran jari daga ƙasashen waje da ba su da tabbas.
“Ina da tabbacin cewa da irin jarin da muka gani daga irin su Alhaji Dangote, ɓangaren masu zaman kansu na yankinmu na iya jagorantar ci gaban al’ummarmu idan aka ba su dama da ƙarfafawa.”
Ya kuma bayyana damuwa kan matsalolin da ke fuskantar kasuwar wutar lantarki ta ECOWAS, yana mai cewa: “Wannan dandali ne na kasuwar wutar lantarki ta yankinmu da ke fuskantar ƙalubale saboda bashin da kamfanonin wutar lantarki na ƙasa ke bin sa.”
Ya bukaci ƙasashen mambobi su tallafa wajen dawo da waɗannan bashi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tattalin arzikin yankin.
Baya ga jawo ɓangaren masu zaman kansu, jawabin Touray ya tabo batutuwan da suka shafi juriyar yankin, haɗin kuɗi da ƙirƙirar rundunar yankin don yaƙi da ta’addanci.
An kuma gabatar da sabbin bayanai kan shirin aiki na shekara, kasafin kuɗi da binciken asusun hukumomin ECOWAS domin tantancewa.
Ya ce: “Muna fatan tattaunawarku kan batutuwan da ke gaban wannan taro za su buɗe hanya ga yankin da ke dogaro da kansa, ba tare da rinjayar waje ba ko fuskantar girgizar tattalin arziki daga waje.”
Ministan Harkokin Wajen Saliyo kuma Shugaban Majalisar Ministocin ECOWAS, Timothy Kabba, ya bukaci ƙasashen Yammacin Afirka da su ƙarfafa haɗin kai wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, tattalin arziki da dimokuraɗiyya.
A lokacin buɗe taron, Kabba ya ce: “Wannan taro yana ƙara tabbatar da jajircewarmu ga haɗin gwiwar yankin, bisa hangen nesanmu na Yammacin Afirka da kuma mai bunƙasa.”
Ya ce a cikin kwanaki biyu na taron, ministoci za su duba rahotanni da takardun shawarwari da nufin inganta haɗin gwiwar tattalin arziki da siyasa a cikin al’umma.
Yayin bikin cika shekaru 50 da rattaba hannu kan yarjejeniyar Lagos, wanda ya kafa ECOWAS, Kabba ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tattalin arziki.
Ya ce: “Dole ne mu ci gaba da ƙoƙari wajen samar da yanayi mai kyau ga bunƙasar ɓangaren masu zaman kansu, wanda shi ne ginshiƙin ajandar haɗin tattalin arziki.”
Ya kuma bukaci ƙarin cinikayya a tsakanin ƙasashen yankin, inganta hanyoyin sufuri da haɗin wutar lantarki, da kuma cikakken amfani da yarjejeniyar cinikayya ta Afirka (AfCFTA) domin bunƙasa yankin.
Shugaban ya kuma tabo batutuwan tsaro da ke addabar Yammacin Afirka, ciki har da ta’addanci, tsattsauran ra’ayi, laifukan ƙungiyoyi da sauya gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Ya jaddada cewa: “Bai kamata kowace ƙasa ta fuskanci waɗannan ƙalubale ita kaɗai ba. Sai ta hanyar ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ƙasashenmu za mu iya shawo kansu.”
Ya bukaci a zuba jari a shirye-shiryen zaman lafiya da tsaro, haɗin gwiwar leƙen asiri da kuma ƙaddamar da Rundunar Tsaro ta ECOWAS.
Kabba ya la’anci juyin mulki da aka yi a wasu ƙasashen yankin, yana mai cewa: “Al’ummarmu dole ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da juyin mulki ko duk wani take dokar mulki.”
Ya nuna damuwa kan abubuwan da suka faru a Jamhuriyar Guinea-Bissau da ƙoƙarin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, yana mai cewa: “Wannan na barazana ga tsarin mulki, dimokuraɗiyya da ƙimar da ke haɗa mu a matsayin al’umma.”
Ya yaba da yadda ECOWAS ta hanzarta mayar da martani kan rikicin siyasa a Guinea-Bissau, yana mai cewa: “Martaninmu cikin gaggawa da haɗin kai, wanda ya haɗa da tattaunawa cikin gaskiya da buɗaɗɗen zuciya, ya nuna jajircewarmu wajen shawo kan rikicin siyasa da dawo da zaman lafiya da tsarin mulki.”
A ƙarshe, Kabba ya ƙarfafa mambobi da su shiga taron da ƙwazo da fata mai kyau.
A nata jawabin, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Jakadiya Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ja hankalin mahalarta taron kan ƙalubalen da ke fuskantar yankin.
Ta ce: “Shekarun baya sun shaida rashin daidaito a siyasa da rashin haɗin kai, ciki har da sauya gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, jinkirin sauya mulki da rashin tabbas a shugabanci a wasu ƙasashe mambobi.
“Wannan na barazana ga ƙimomin dimokuraɗiyya da muka amince da su, kuma na iya lalata ci gaban da muka samu da wahala.”
Game da haɗin tattalin arziki, Jakadiya Odumegwu-Ojukwu ta jaddada buƙatar ƙarin cinikayya a tsakanin ƙasashen yankin da samar da dama ga matasa.
Ta ce: “Makomar yankinmu na dogara ne da zurfafa cinikayya a tsakaninmu, ƙarfafa sarkar samar da kayayyaki, sauƙaƙa zuba jari da samar da dama ga mutane sama da miliyan 400, musamman matasa yan ƙasa da shekaru 25 da ke da kusan kashi 65 cikin 100 na yawan jama’a. Ba shakka suna dogaro da ECOWAS wajen jagorantar su zuwa ci gaba.”
Ministar ta jaddada muhimmancin rawar da majalisar ke takawa wajen tsara manufofi.
Ta ce: “Takardun da ke gabanku na magana ne kan muhimman batutuwa da suka shafi shugabanci, haɗin tattalin arziki, amsa ga bala’o’i, zaman lafiya da tsaro, noma da ingancin hukumomi.”
Ta Kara da cewa Yammacin Afirka na fuskantar ƙarin rikice-rikicen siyasa da matsalolin tsaro, inda wasu ƙasashen ECOWAS ke fama da juyin mulki, ƙoƙarin juyin mulki da sauyin mulki maras tabbas.
Mali, Nijar da Burkina Faso na ƙarƙashin mulkin soja, yayin da Guinea-Bissau ta shiga wannan rukuni bayan wani shigar sojoji. A ranar Lahadi, an hana wani ƙoƙarin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.
Halinda ta ƙara taɓarɓarewa sakamakon tsananta matsalolin jinƙai, inda miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu a sassa daban-daban na Mali, Nijar, Najeriya da Burkina Faso.



















