Kudaden jama’a tsarkaka ne. Ba su kamata su zama kayan yakin neman zabe ko lada ga masu biyayya ga jam’iyya ba. Amma yanzu ana kara samun yadda wasu Kananan Hukumomi ke cire makudan kudade daga asusun gwamnati, suna nuna su a bainar jama’a, sannan su raba su ga mambobin jam’iyya alamar tabarbarewar doka da shugabanci.
Doka ba ta da rudani. Dokar Hana almundahanan da safaran Kudi ta 2022, musamman Sashe na 2(1), ta haramta wa kungiyoyi ciki har da Kananan Hukumomi yin mu’amalar kudi fiye da Naira miliyan goma (₦10m) a wajen hanyoyin banki da aka amince da su. Sashe na 2(2) kuma ya wajabta bayar da rahoto ga hukumomin da suka dace, ciki har da SCUML. Duk wanda ya karya wannan doka, an dauke shi da aikata mu’amala mai shakku.
Nuna makudan kudade a fili ba kyauta ce kawai ba, hujja ce a gaban doka a Najeriya.
Doka a Najeriya tana amincewa da bayanan da ke cikin kafafen sada zumunta da na dijital a matsayin hujjoji da za su iya haifar da bincike daga EFCC.
Irin wannan hali yana karya gaskiya da rikon amana, yana kuma nuna yunkurin kauce wa biyan hisabi.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne lokacin da ake raba wadannan kudade na jama’a ga mambobin jam’iyya.
Tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya takaita amfani da dukiyar gwamnati ne kawai don amfanin jama’a. Amfani da kudaden Karamar Hukuma wajen harkokin jam’iyya laifi ne, cin hanci, almundahana, da karya amana, kamar yadda dokokin EFCC da ICPC suka tanada, kuma yana iya haifar da hukunci a karkashin Dokar Zabe.
Dokokin kudi an kafa su ne don kare dimokuradiyya, ba don a take su ba. Ba za a bar shugabanci ya koma raba kudi a matsayin tallafi ba.
Hon. Sama’ila Aliyu Makarfi
ADC, Karamar Hukumar Makarfi
7 ga watan Janairu, 2026

















