
Hakane Yana kunshe ne a wani Sanarwa dake dauke da sa hannun Andy Odeh, Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC Ltd, kuma a Raba wa Yan jaridu a Abuja.
A yayin taron buɗe bikin taron makamashi na kasa da kasa (NIES) 2026 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, Babban Daraktan Kamfanin NNPC Ltd, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa gas shi ne ginshiƙin dabarun makamashin Najeriya.
“Makomar arzikinmu tana cikin yadda za mu iya amfani da albarkatunmu yadda ya kamata. Gas shi ne gadar zuwa makoma mai tsabta, injin masana’antu, da kuma tubalin ci gaban fitar da kaya,” in ji Ojulari.
Ya bayyana kalubalen makamashin Afirka da ya kira “trilemma” samun damar amfani, sauƙin farashi, da dorewa, inda ya nuna cewa sama da mutane miliyan 600 a nahiyar ba su da wutar lantarki duk da wadatar albarkatun makamashi. Da Najeriya ke da ganga biliyan 37 na man fetur da kuma tiriliyan 209 na gas, Ojulari ya ce ƙasar da NNPC Ltd za su jagoranci sauya labarin makamashin Afirka.
“Dole ne asamu mafita Wanda ta kasance mai adalci, mai daidaito, kuma mai mayar da hankali ga jama’a. Dole ne ta fitar da al’ummarmu daga talauci, ta ƙarfafa masana’antu, ta tallafa wa noma, ta sauya harkar sufuri, kuma ta buɗe ƙirƙira da fasahar matasan Afirka,” ya ƙara da cewa.
Ojulari ya bayyana cewa NNPC Ltd ba kawai kamfani na kasuwanci ba ne, har ma mai kawo zaman lafiya da ci gaba. Ya sanar da ƙaddamar da sabon Gas Masterplan da kuma ci gaba da manyan ayyukan gina bututun gas kamar Obiafu-Obrikom-Oben (OB3),Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK), da faɗaɗa bututun Escravos-Lagos (ELPS).
“Waɗannan ayyuka ba kawai bututun gas ba ne, su ne hanyoyin tattalin arziki,” in ji shi.

















