• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Kasuwanci

Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci

December 11, 2025
in Kasuwanci
Reading Time: 3 mins read
0
Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci
0
SHARES
6
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Attajirin nan na Afirka Aliko Dangote ya bai wa gwamnatin Najeriya da al’ummarta shawarwari kan yaƙi da talauci, bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasar Bola Tinubu a farkon wannan mako.

Daga alƙaluma na baya-baya da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar, kimanin kashi 30.9% na al’ummar Najeriya ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci, a cewar Bankin Duniya.

Karanta HakananPosts

Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka

Rukunin Dangote Ya Haskaka Manufar 2030 a Taron Kasuwanci na Kaduna

Kamfanin Dangote ta Bai wa Abokan Ciniki 50 Kyautar Motoci da Kudi

Hakan na nufin suna rayuwa a ƙasar da dalar Amurka 2.15 a kowace rana.

Bankin Duniya ya bayyana cewa gwamnati na buƙatar samar da sauye-sauyen da suka dace domin shawo kan matsalar talauci da ke ci gaba da yi wa al’umma katutu. Rahoton Bankin ya ce duk da gwamnatin tarayyar ta ce ta fito da wasu shirye-shiryen, to amma ana tafiyar hawainiya wajen aiwatar da su.Aliko Dangote, wanda ya fi kowa arziƙi a Afirka na da dukiyar da kimarta ta kai kimanin dala biliyan 30, bisa rahoton mujallar Forbes, inda ya tara arzikinsa ta hanyar manyan kamfanoninsa na siminti da sukari da takin zamani, sannan a baya-bayan nan katafariyar matatar man fetur.

Attajirin ya nuna damuwarsa kan yadda wasu masu kuɗi da manyan ‘yan kasuwa ke rayuwa ba tare da la’akari da bukatun ƙasa ba.

Ya yi tsokaci kan yadda rayuwar alatu ke karkatar da hankali daga abin da zai kawo ci gaban tattalin arziki da ayyukan yi a ƙasa.Zuba jari maimakon rayuwar alatu
Attajirin ya nuna damuwa kan yadda wasu masu kuɗi da ƴan kasuwa ke kashe kuɗi a kan abin alatu ba tare da la’akari da bukatun ƙasa ba. Ya yi kira ga masu arziƙi da ƴan kasuwa su mayar da kuɗaɗensu zuwa gina masana’antu da samar da ayyukan yi ga jama’a musamman a yankunan da ake bukata.

Ya ce duk wanda yake da kudin sayen motar alfarma ta Rolls-Royce da jiragen sama na alfarma, kamata ya yi ya kafa masana’anta.

Juya arziƙi a Najeriya maimakon ƙasashen wajeDangote ya yi kira da a daina jiran masu zuba jari daga ƙasashen waje, ya ce babu yadda masu zuba jari daga ƙetare za su shigo Najeriya idan masu dukiya a cikin gida ba sa zuba jari a gida.

“Kyakkyawan tsari da shugabanci mai gaskiya da dokoki na gari ne ke janyo masu jarin waje.” in ji shi.

Saboda haka masu kuɗi da ‘yan kasuwa na cikin gida ne ginshiƙin tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce masu kuɗi su buɗe masana’antu a yankunansu saboda hakan ne hanyar inganta rayuwar jama’a kuma zai janyo masu zuba jari daga waje.

A rage dogaro da kaya daga waje
Hukumomi a Najeriya na yawan kokawa kan yadda al’umma suka fi mayar da hankali wajen amfani da kayan ƙasashen ƙetare, wani lamari da ya sanya gwamnatin Najeriya ta haramta shigo da wasu kayan da take ganin za a iya sarrafawa a cikin gida.

Dangote ya ce “muna ƙoƙarin ganin mun mayar da Najeriya cibiyar sarrafa abubuwa a Afirka.

“Ƙasasehn Afirka na shigo da kaya, amma muna so ne mu tabbatar cewa muna sarrafa duk abin da muke buƙata a cikin gida.”

A yi koyi da shugabannin baya
Dangote ya yi amfani da misalai na rayuwar shugabannin ƙasa a zamanin mulkin soja, inda ya ce: “A lokacin soja, kowa, duk girman muƙaminsa yana amfani ne da mota samfurin Peugeot 504—shi ne mafi girma. To wane ne kai da za ka hau mota Rolls-Royce?”

“Za ku iya jin dadin ku, amma yana da kyau a dinga yin abubuwa da tsari.”

Ya bayyana cewa idan kana da irin waɗannan kudaɗen kamata ya yi ka kafa masana’anta.

A riƙa biyan haraji yadda ya kamata
Dangote ya ce haraji ne ke gina makarantu, asibitoci da gadojin da ake amfani dasu saboda haka ya kamata masu kuɗi da ƴan kasuwa su riƙa biyan haraji yadda ya kamata

“Gwamnati ita ce babbar mai zuba jari ga duk wani mai kamfani ko ɗan kasuwa saboda haka biyan haraji wajibi ne domin shi ne tushen ci gaban kasa.” in ji shi.

Dangote ya kuma jaddada cewa Najeriya na fuskantar ƙalubale mai girma sakamakon yawan haihuwa, inda ake samun yara miliyan 8.7 duk shekara.

Ya ce wannan yana nuni da cewa akwai buƙatar samar da wutar lantarki da ababen more rayuwa, domin tabbatar da cewa ƙasa na iya ɗaukar wannan ƙaruwa ba tare da matsaloli ba wanda shi ya sa waɗannan shawarwari ke da muhimmanci. Daga:BBC Hausa

Previous Post

Kudurin Dokar Kafa Hukumar Kula da Ingancin Cibiyoyin Kiwon Lafiya Ya Tsallake Karatu Na Biyu

Next Post

Alummar Bagwai da Shanono Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Barau Jibrin a Matsayin Gwamnan Jihar Kano

Related Posts

Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka
Kasuwanci

Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka

February 27, 2026
Rukunin Dangote Ya Haskaka Manufar 2030 a Taron Kasuwanci na Kaduna
Kasuwanci

Rukunin Dangote Ya Haskaka Manufar 2030 a Taron Kasuwanci na Kaduna

February 16, 2026
Kamfanin Dangote  ta Bai wa Abokan Ciniki 50 Kyautar Motoci da Kudi
Kasuwanci

Kamfanin Dangote ta Bai wa Abokan Ciniki 50 Kyautar Motoci da Kudi

February 15, 2026
NDIC Ta Tabbatar da Cikakken Kariya ga Masu Ajiya a Bankuna
Kasuwanci

NDIC Ta Tabbatar da Cikakken Kariya ga Masu Ajiya a Bankuna

February 12, 2026
Taron Baje Kolin Kaduna: Masari da Shugaban KADCCIMA Sun Jaddada Muhimmancin Bunkasa Ci gaban Abubuwan Cikin Gida
Kasuwanci

Taron Baje Kolin Kaduna: Masari da Shugaban KADCCIMA Sun Jaddada Muhimmancin Bunkasa Ci gaban Abubuwan Cikin Gida

February 12, 2026
Dole Africa Ta Daidaita Tsarin Ayyuka, Dokoki da Jarin Kuɗi Don Cimma Tsaron Makamashi Inji Ojulari
Kasuwanci

Dole Africa Ta Daidaita Tsarin Ayyuka, Dokoki da Jarin Kuɗi Don Cimma Tsaron Makamashi Inji Ojulari

February 11, 2026
Next Post
Alummar Bagwai da Shanono Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Barau Jibrin a Matsayin Gwamnan Jihar Kano

Alummar Bagwai da Shanono Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Barau Jibrin a Matsayin Gwamnan Jihar Kano

Fashewar Bututun Gas na Escravos zuwa Lagos, NNPC Ta Dauki Matakin Gaggawa a Jihar Delta

Fashewar Bututun Gas na Escravos zuwa Lagos, NNPC Ta Dauki Matakin Gaggawa a Jihar Delta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
“Dole ne mutum ya kasance mai taka-tsantsan da haƙuri kafin yin kasuwancin waya” — Abba

“Dole ne mutum ya kasance mai taka-tsantsan da haƙuri kafin yin kasuwancin waya” — Abba

December 30, 2025
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
AREWA: Ina Alfaharinmu na Arewa?

AREWA: Ina Alfaharinmu na Arewa?

February 28, 2026
Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka

Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka

February 27, 2026
Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025

Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025

February 26, 2026
DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci

DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci

February 26, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by