Gidauniyar NNPC ya kammala da kuma mika cikakkiyar na’urar Magnetic Resonance Imaging (MRI) mai ƙarfi 1.5 Wanda Tesla ta kirkiro ga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe (NAUTH), Nnewi, domin ƙarfafa damar samun kulawa da lafiya a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.
Kyautar, wacce aka aiwatar ta hannun sashen ayyukan Kamfanin ga Alumma wato Corporate Social Responsibility na Kamfanin NNPC Ltd., ba ta ƙunshi na’urar MRI kaɗai bane, har ma da cikakken kayan aikin tallafi. Wannan ya haɗa da tsarin kariya na RF, injin sanyaya (chillers), na’urar UPS mai ajiyan wutar lantarki, kayan hoto na musamman, iska don numfashi, CCTV, na’urar lura da iskar oxygen, intercom, da kayan jin daɗin marasa lafiya domin tabbatar da ingantaccen aiki.
Shekaru da dama, marasa lafiya daga jihohin Anambra, Enugu, Imo, Abia, Ebonyi da makwabciyar Delta sun sha wahala wajen samun damar yin MRI saboda tsadar kuɗi, dogon lokaci da kuma nisan tafiya. Sabuwar na’urar da aka girka za ta rage waɗannan matsalolin sosai.
Wannan na cikin sanarwar manema labarai da Andy Odeh, Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC Ltd., ya sanya hannu kuma aka rabawa ‘yan jaridu a Abuja.
A wajen bikin kaddamarwa da aka gudanar a cibiyar ICT ta Igwe Orizu, dake NAUTH, Babban Jami’in NNPC Ltd., Engr. Bashir Bayo Ojulari, ya ce aikin ya nuna yadda kamfanin ke mai da hankali wajen gina cibiyoyi masu ɗorewa ba wai kyauta ta lokaci ɗaya ba.
“Ina so in jaddada cewa girka MRI a NAUTH na nuna jajircewarmu wajen gina cibiyoyi masu ɗorewa, tsarin da zai dawwama da kuma gadon alheri,” in ji Ojulari wanda Daraktar NNPC Foundation, Mrs. Emmanuella Arukwe ta wakilta. “Samun ingantacciyar kulawa da lafiya shi ne ginshiƙin mutunci, tsawon rai da kuma haɓakar tattalin arziki.”
Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, wanda Kwamishinan Lafiya Dr. Afam Obidike ya wakilta, ya ce wannan na’ura za ta inganta bincike da gano cuta da magani cikin sauki da daidaito ga marasa lafiya a yankin. Ya yaba wa Gidauniyar NNPC saboda cike gibin da ke cikin tsarin lafiya na jihar.
Mataimakiyar Shugaban NNPC Ltd. a harkar Business Services, Mrs. Sophia Mbakwe, wacce Engr. Isokariari Telema ya wakilta, ta sake jaddada alkawarin kamfanin na zuba jari cikin adalci a al’umma.
“A cikin fiye da shekaru arba’in da NNPC ta yi, ta ci gaba da taka rawa wajen inganta rayuwa a Najeriya, ta tallafa wajen ci gaban ababen more rayuwa, jin daɗin al’umma, tallafin ilimi da sauran shirye-shirye da ke nuna ƙimominmu na gaskiya, ƙwarewa da dorewa,” in ji ta.
Shugaban Asibitin NAUTH, Farfesa Joseph Ugboaja, ya yi maraba da wannan taimako, yana mai cewa marasa lafiya sun sha wahala wajen yin dogon tafiya da tsadar kuɗi don samun irin wannan hoto na zamani.
“Na dade ina ganin yadda marasa lafiya a yankinmu ke yin dogon tafiya da tsadar kuɗi don samun irin wannan ganewar cuta. Wannan na’ura za ta kawar da wannan nauyi,” in ji Ugboaja. “NNPC Foundation ta nuna cewa aikin al’umma ba wai magana ce kawai ba, amma wata hanyar ceto ga cibiyoyi kamar namu.”
Wannan taimako ya yi daidai da dabarun NNPC Ltd. na haɗa aikin samar da makamashi da zuba jari a al’umma domin inganta jin daɗin jama’a da haɓaka ƙasar baki ɗaya.


















