Daga Bashir Bello, Abuja
NNPC Foundation Limited/Gte, reshen Corporate Social Responsibility (CSR) na NNPC Ltd., ta lashe CSR Champion Award (Health) 2025 da Independent Newspapers ta karrama. An mika wannan lambar yabo a lokacin bikin cikar shekaru 25 na Independent Newspapers Awards, mai taken “Game Changers: Breaking Barriers and Shaping Tomorrow,” wanda aka gudanar a Eko Hotel and Suites ranar Asabar, 18 ga Afrilu, 2026.
A cewar sanarwar manema labarai da Andy Odeh, Babban Jami’in Hulɗar Jama’a na NNPC Ltd. ya sanya hannu, wannan lambar yabo ta nuna irin gudummawar da Gidauniyar NNPC ta bayar wajen kiwon lafiya da kuma shirin zuba jari na zamantakewa da suka shafi lafiya, ilimi, muhalli, da samun makamashi.
An karrama Gidauniyar ne saboda jerin manyan ayyukan lafiya da ta gudanar, ciki har da:
– Bincike da tiyatar ido kyauta da suka dawo da gani na Yan Najeriya fiye da 6,000, ciki har da yara da aka haifa makafi.
– Shirin rigakafi da maganin cutar daji da glaucoma.
– Ayyukan kiwon lafiya a yankunan da ba su da isassun cibiyoyin lafiya.
– Gyara da samar da kayan daki a dakuna uku da kujeru 100 a Asibitin Kashi na Ƙasa, Igbobi.
– Tallafin tiyatar zuciya.
– Samar da kayan tsaftar hakora ga yara a makarantu na musamman.
Jinjinawa da Godiya
Emmanuella Arukwe, Babban Daraktan Gidauniyar NNPC, ta bayyana wannan lambar yabo a matsayin tabbaci ga aikin Foundation da kuma amincewar da ‘yan Najeriya suka nuna.
“Wannan ya nuna ƙarfin gwiwar al’ummomin da muke yi wa hidima, jajircewar tawagarmu, da ƙarfin haɗin gwiwa da suka ba mu damar yin ayyuka masu ma’ana a fannin lafiya, ilimi, dorewar muhalli da samun makamashi,” in ji ta.
Arukwe ta kara da cewa jagoranci da goyon bayan NNPC Ltd. Management team sun taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa Gidauniyar don ci gaba da bayar da gudummawar zamantakewa a fadin ƙasa.
A karshe, Gidauniyar ta yi alkawarin ci gaba da ƙarfafa shirin kiwon lafiya da zai inganta rayuwa da kuma bayar da gudummawa ga ci gaban ƙasa.


















