Daga Bashir Bello
Babban Shugaban Gudanarwa na Kamfanin NNPC Limited, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya samu lambar yabo ta jaridar Vanguard ta shekarar 2025 a matsayin “Gwarzon Shekara Wajen Samar Da Sabbin Dubaru Da Gyara A Fannin Makamashi.”
Wannan lambar yabo, wadda ake bayarwa don karrama ‘yan Najeriya da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban, an mika ta ne ga Babbar Mataimakiyar Shugaban Kamfanin ta fuskar Ayyukan Kasuwanci, Sophia Mbakwe, wadda ta wakilci shugaban a birnin Legas ranar Juma’a.
Mbakwe ta karɓi wannan gagarumar lambar yabo ne daga hannun Shugaban Bankin Standard Chartered na Najeriya, Ayodeji Adelagun. Ta samu rakiyar Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin, Andy Odeh, a wurin taron.
A cewar kamfanin Vanguard Media Limited, an ba Ojulari wannan karramawa ne sakamakon gagaruman nasarorin da ya samu a NNPC Ltd., musamman wajen gyare-gyaren dabaru, haɓaka ayyuka, kyakkyawan shugabanci, da kuma samar da sabbin dabarun da ke ƙara darajar kamfanin; waɗanda suke sake fasalin makomar makamashin ƙasar nan.
#MakamashiNaYau
#MakamashiNaGobe




















