
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi kira ga rukunin kamfanonin Dangote (Dangote Group) da su faɗaɗa ayyukansu na zuba jari ta hanyar amfani da albarkatun ma’adinai da jihar ke da su.
Da yake jawabi a wurin taron buɗe baje kolin kasuwanci na jihar Nasarawa karo na uku (NASTFE), Gwamnan, wanda Darakta mai kula da harkokin kasuwanci a ma’aikatar ciniki da zuba jari ta jihar, Dr. Ahmed Agbo II ya wakilta, ya bayyana cewa tuni akwai kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin jihar da kamfanin na Dangote.
Gwamnan ya ce jihar Nasarawa tana da albarkatun ma’adinai da dama waɗanda za su ja hankalin rukunin kamfanonin Dangote don zuba jari.
Haka kuma, ya yaba wa kamfanin kan namijin ƙoƙarin da yake yi wajen samar da ayyukan yi, inda ya ƙara da cewa burin kamfanin na samar da dala biliyan 100 nan da shekarar 2030 (Vision 2030) zai taimaka matuƙa, ba kawai ga ƙananan sana’o’i ba, har ma da tattalin arziƙin Najeriya baki ɗaya.
Kamfanin Dangote shi ne babban mai ɗaukar nauyin wannan baje kolin na NASTFE, wanda ke da taken: “Buɗe Hanyoyin Haɗin Gwiwar Masana’antu: Zurfafa Sarƙar Daraja da Haɓaka Ci Gaba Mai Haɗi a Jihar Nasarawa.”
Jihar Nasarawa ita ce matattarar kamfanin sikari na Dangote (Nasarawa Sugar Company Limited – NSCL), wanda babban aiki ne da ke da nufin samar da danyen kaya a cikin gida a fannin sikari na tattalin arzikin Najeriya. Ana sa ran idan aka kammala aikin sikarin, zai kasance ɗaya daga cikin manyan ayyukan zuba jari a fannin sikari a nahiyar Afirka.
A gefe guda kuma, ƙungiyar masu masana’antu na ƙanana da matsakaita ta Najeriya (NASSI) ta bayyana cewa shirin Dangote na Vision 2030 zai tallafa wa ƙananan masana’antu a Najeriya. Wannan na zuwa ne yayin da mahalarta taron ke ta tururuwa zuwa rumfar kamfanin a wurin baje kolin na NASTFE da ake gudanarwa.
Da yake magana da manema labarai, shugaban ƙungiyar NASSI reshen jihar Nasarawa, Comrade Nidan Sambo Manasseh, ya ce nasarorin kamfanin abin koyi ne ga ƙananan sana’o’i a Nasarawa da Najeriya baki ɗaya. Ya bayyana cewa NASSI tana haɗin gwiwa da kamfanin Dangote don haɓaka ƙananan sana’o’i a Najeriya daidai da burin kamfanin na shekarar 2030.
Ya ce: “Tsarinmu shi ne mu daidaita ci gaban sana’o’in gida da manyan tsarin masana’antu daidai da taken wannan baje kolin.” Ya ƙara da cewa ta hanyar babban shirin kamfanin na koyar da sana’o’i (ESAP), an horar da dubun-dubatar matasa a fadin jihar Nasarawa.
A nata jawabin a wajen bude taron, Daraktar shiyya kuma Babban Mashawarciya ga Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Mrs. Fatima Wali-Abdurrahman, ta lura cewa wannan baje kolin ya samar da dandamali mai mahimmanci ga kamfanin don tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan Najeriya masu sha’awar yin kasuwanci da kamfanin.




















