Daga Bashir Bello, Abuja
Rukunin kamfanonin Dangote wace Babban kamfani ne a fadin Afirka da duniya zai gabatar da manyan ayyukansa na Dangote Refinery da Kamfanin Petrochemical a bikin kasuwanci na Nasarawa 2026, wanda Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule, zai bude a ranar 20 ga Afrilu.
Dangote Industries Limited zai kuma nuna Manufar 2030, wadda ta mayar da hankali kan kirkire-kirkire da bunkasa masana’antu a Afirka.
Dangote Group shi ne babban mai daukar nauyin bikin kasuwanci da nune-nunen Nasarawa (NASTFE) mai taken: Buɗe Hadin Gwiwar Masana’antu: Zurfafa Silsilar Ƙima da Inganta Ci gaban Jama’a a Jihar Nasarawa.
A cewar mai magana da yawun kamfanin, Anthony Chiejina, sauran sassan kasuwanci na kamfanin za su halarci wannan taron na shekara-shekara a babban birnin jihar, Lafia.
Ya bayyana cewa kayayyakin da za a nuna a bikin sun hada da na sassan kasuwanci kamar Dangote Cement, Dangote Sugar, Dangote Salt da kayan yaji, Dangote SinoTruk, Dangote Packaging, da Dangote Fertiliser.
Sanarwar ta kuma ambaci Fatima Wali Abdurrahman, Darakta na Yanki/Kwararriyar Shawara ga Shugaban Dangote Group, wadda ta ce Jihar Nasarawa na da muhimmanci ga zuba jari na kamfanin a Afirka.
“Tana dauke da Dangote’s Nasarawa Sugar Company Limited (NSCL). Wannan aikin sukari, idan an kammala shi, zai kasance daya daga cikin manyan jarin sukari a Afirka,” in ji ta.
Ta kara da cewa bikin kasuwanci na samar da dandalin muhimmi ga kamfanin don tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da kuma ’yan Najeriya masu sha’awar gano damar kasuwanci tare da kamfanin.
Ta bayyana cewa za a samar da Help Desk na musamman don karɓar tambayoyi, wanda zai bai wa kamfanin damar tattaunawa da mahalarta kan sassan kasuwanci na Dangote Group.
A yayin da yake magana da ’yan jarida a Lafia, Nidan Sambo Manasseh, Shugaban kungiyar ’yan masana’antu kanana (NASSI) reshen Nasarawa, ya ce taken bikin kasuwanci na bana ya dace da hangen nesa na Dangote Group.
“Mun daidaita sosai da hangen nesa na Aliko Dangote, wanda jagorancinsa ke ci gaba da tsara makomar tattalin arzikin Najeriya. Mayar da hankalinsa kan masana’antu, samar da kayayyaki a cikin gida, da ƙirƙirar ƙima yana karfafa kokarinmu na haɗa MSMEs da silsilar ƙima mai tsari.
“Ta wannan haɗin gwiwa, muna gina gada tsakanin kasuwancin ƙananan matakai da manyan masana’antu, don inganta ci gaban jama’a,” in ji shi.
Ya ce wannan bugu na uku na NASTFE an tsara shi a matsayin dandalin kasuwanci, masana’antu, da ci gaban ƙwarewar ɗan adam, ba kawai nune-nune ba.
A cewarsa: “Babban abin da ya fi daukar hankali a shirin bana shi ne Shirin Koyon Ƙwarewa (ESAP), wanda aka tsara shi a matsayin aikin kunshe don samun tallafin daukar nauyi.
“ESAP shiri ne na shekara-shekara daga Yuli zuwa Disamba da ke nufin amfanar da mutane 2,000 a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.
“An tsara shirin a matsayin tsarin horo mai motsi, yana tafiya daga karamar hukuma zuwa wata don tabbatar da cikakken shiga daga matakin ƙasa.”
Yayin da yake magana kan Manufar 2030 na Dangote Group, ya ce: “Manufarmu ita ce daidaita ci gaban kasuwancin cikin gida da manyan tsarin masana’antu.”



















