
Kwamitin Sauyin Yanayi da tabbatar da inganci na Jihar Kaduna (KADCCAM) ya yaba wa Kungiyar Manoma Kayan lambu ta Jihar Kaduna bisa kaddamar da dasa tsirrai 5,000 na tattalin arziki da marasa tattalin arziki, yana bayyana wannan mataki a matsayin muhimmiyar gudunmawa wajen rage sauyin yanayi, dawo da muhalli da kuma karfafa al’umma.
Shirin dasa itatuwan ya hada masu fafutukar kare muhalli, masu aikin lambu, shugabannin gargajiya da na addini, jami’an gwamnati, manoma, dalibai, kungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki na muhalli.
A yayin taron, Mataimakin Shugaban KADCCAM, Kwamared Ibrahima Yakubu, ya yaba wa Kungiyar Manoma Kayan Lambu bisa daukar matakin zahiri kan kalubalen muhalli da ke kara ta’azzara a Jihar Kaduna. Ya ce, dasa itatuwa na daya daga cikin hanyoyin zahiri da al’umma za su iya bayar da gudunmawa wajen kare muhalli, domin itatuwa na shan iskar carbon dioxide daga sararin samaniya, suna bayar da inuwa, suna kare kasa daga lalacewa, suna tallafawa nau’o’in halittu, kuma suna karfafa al’umma daga wasu tasirin sauyin yanayi.
“Dole ne aikin kare muhalli ya wuce tattaunawa da manufofi zuwa matakan zahiri da al’umma za su iya gani kuma su shiga ciki. Dasa da kuma kare itatuwa na daya daga cikin wadannan matakai,” in ji shi.

Kwamared Yakubu ya kira da a kara hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, kungiyoyin manoma, kungiyoyin fararen hula, shugabannin gargajiya da na addini, makarantu da al’umma domin tabbatar da cewa itatuwa 5,000 an dasa su yadda ya kamata, an kare su kuma an kula da su.
Ya jaddada cewa nasarar shirin ba za a auna ta da yawan tsirrai da aka raba ba, sai dai da yawan itatuwan da suka tsira kuma suka ci gaba da bayar da fa’idar muhalli da tattalin arziki a nan gaba.
Shugaban Kungiyar Manoma Kayan Lambu ta Jihar Kaduna, Kwamared Bala Umar, ya ce shirin an tsara shi ne domin inganta Jihar Kaduna ya Zama mai Bunkasa lafiya da kuma mai juriya ga sauyin yanayi.
Ya bayyana cewa itatuwa na bayar da fa’idoji da dama, ciki har da inganta ingancin iska, rage zafi, kare kasa daga hawan ruwan sama, tallafawa nau’o’in halittu da kuma samar da damar tattalin arziki ga manoma.
Har ilayau Kwamared Umar ya shawarci mazauna jihar da su sanya dasa itatuwa da kare muhalli cikin ayyukan yau da kullum, yana mai jaddada cewa kowace gida, makaranta, gona, al’umma da cibiyoyi na iya bayar da gudunmawa wajen kare muhalli.
Haka kuma, Babban Sakatare na Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Halitta ta Jihar Kaduna, Hajiya Linda Asabat Yakubu, ta bayyana jin dadinta da shirin tare da yaba wa kungiyar bisa tallafawa kokarin gwamnati wajen magance matsalolin muhalli.
Ta sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Jihar Kaduna na samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasa da kuma tallafawa shirye-shiryen kare muhalli da ci gaba mai dorewa.
Hajiya Yakubu ta kuma yaba wa kungiyoyin fararen hula da na gwamnati marasa riba bisa cike gibin kokarin gwamnati wajen dasa itatuwa da matakan sauyin yanayi.
Ta kara yabawa KADCCAM bisa ci gaba da shiga tsakani tare da masu ruwa da tsaki, tana mai cewa magance sauyin yanayi na bukatar hadin gwiwar gwamnati, al’umma, kungiyoyi da kuma kowane mutum.
Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kaduna Shawara kan Sauyin Yanayi, Hon. Yusuf Idris Amoke, ya kuma yaba wa masu shirya taron tare da kira da a kara hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa matakan kare muhalli a fadin jihar.

Ya kara karfafa daliban da suka halarci taron da su zama jakadun muhalli ta hanyar dasa da kuma kare itatuwa a makarantunsu da al’ummominsu.
A cewarsa, matasa su ne shugabannin gobe, dole ne a samar musu da ilimi da kwarewa da za su taimaka wajen fahimtar sauyin yanayi da kare muhalli.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana fata cewa itatuwa 5,000 za su tsira kuma su girma zuwa manyan itatuwa da za su iya bayar da gudunmawa wajen Inganta iska, rage lalacewar muhalli, inganta yanayin zafi na yankuna da kuma karfafa juriya ga sauyin yanayi a cikin al’ummomin Kaduna.
Shirin ya kara nuna muhimmancin hada manufofin sauyin yanayi da matakan zahiri a matakin al’umma, yayin da Kaduna ke ci gaba da fuskantar kalubalen muhalli da ke da alaka da sauyin yanayi, ciki har da karuwar zafi, lalacewar kasa da sauyin yanayin ruwan sama.

















