Daga Bashir Bello, Abuja.
Shugaban Kungiyar kwallon Kwando ta Najeriya (NVBF), Injiniya Musa Nimrod ya taya murna ga Mista Isaiah Kemje Benjamin bisa sake zaben sa a matsayin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida na Wasanni ta Najeriya (SWAN).
Injiniya Nimrod, wanda shi ma mai tallafawa SWAN ne, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 30 ga Agusta, 2026, a Kaduna.”
Ina, Injiniya Musa Nimrod, Mai Tallafawa Kungiyar ‘Yan Jarida na Wasanni ta Najeriya, SWAN, ina taya abokina Isaiah Kemje Benjamin murna bisa nasarar sake zaben sa a matsayin Shugaban SWAN na kasa a zaben da aka gudanar a ranar Juma’a, 28 ga Agusta, 2026 a Kaduna.
“Wannan sabuwar dama alamar amincewa da kwarin gwiwar da mambobin SWAN ke da shi ga jagorancinka, hangen nesanka, da jajircewarka wajen bunkasa aikin jaridar wasanni a Najeriya,” in ji shi.
Engr. Nimrod ya bayyana cewa wa’adin farko ya kafa tubalin hadin kai, kwarewa, da kare muradun ‘yan jarida na wasanni.”Ina da tabbacin cewa wannan wa’adi na biyu zai gina kan wadannan nasarori tare da kawo ci gaba mai yawa ga kungiyar da kuma aikin rahoton wasanni a kasa.
“A matsayina na Mai Tallafawa, ina tabbatar maka da kai da sabbin shugabannin da aka zaba cewa zan ci gaba da bayar da goyon baya yayin da kuke aiki don inganta walwalar mambobi, kare ka’idojin aiki, da kuma haskaka wasannin Najeriya a gida da waje.
“Na sake taya ka murna. Ina addu’a cewa wa’adinka zai kasance mai zaman lafiya, mai tasiri, kuma abin tunawa,” in ji shi.Sa hannu



















