CG CUSTOM
Ƙungiyar da ke kan gaba a tebur, ‘yan wasan Chief of Army Staff (COAS) Spikers, sun ci gaba da nasarorinsu a Gasar Firimiya ta Ƙwallon Volleyball ta Babban Kwanturolan Janar na Kwastam 2026, wadda ke gudana a dakin wasanni na filin wasa na ƙasa da ke Abuja.
A wasa na biyar na maza da aka yi ranar Alhamis, ‘yan wasan COAS Spikers sun samu nasara 3-0 a kan ƙungiya mai ƙarfi, Police Machine.
Duk da nuna ƙwarin gwiwa, Police Machine ba su iya tunkarar ƙarfin abokan karawarsu ba, waɗanda suka mamaye wasan tun daga farkon Wasan.
Zagaye na farko ya ƙare 25-22, na biyu 25-16, na uku kuma 25-20.
Da yake zantawa da manema labarai, kocin COAS Spikers, Elishama Elam, ya ce yana godiya ga Allah da suka ci dukkan wasanninsu zuwa yanzu.
“To, da farko, ina godiya ga Allah da ya sa hakan ya yiwu. Yaran nan suna kokari kuma suna son su nuna ƙarfin su.
“Ina fatan za su ci gaba da haka. Sai dai mun fara ne. Har yanzu muna da wasanni takwas. Don haka addu’ata ita ce kada a samu rauni,” in ji shi.
Da yake ƙara bayani, ya ce ‘yan wasansa suna buga wasa bisa umarni.
“A yadda aka saba akwai taron shirin wasa kafin mu fito kuma sun san dalilin da ya kawo su nan. Ba na yawan magana ba, ba kamar yadda kuka saba sanina a baya ba.
“A wannan karon, ba na yawan magana saboda sun zo don aiki ne, kuma ina addu’a su ci gaba da haka,” ya bayyana.
Kan abin da yake sa ran gani a ƙarshen gasar, ya nuna ƙwarin gwiwar samun nasara.
“Wannan ita ce addu’ar kowa, addu’ar kowane koci. Babu kocin da ya zo wannan gasa da ba ya neman nasara. Amma ina roƙon Allah ya ba ni nasara a ƙarshe,” ya yi addu’a.





















