Daga BAshir Bello, Abuja
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirin kafa babbar hanyar jigila da rarraba man fetur a faɗin Afirka, ta hanyar zuba jari a bututun mai, wuraren ajiya da hanyoyin samar da kayayyakin mai.
Haka kuma, ya buƙaci gwamnatocin ƙasashen Afirka su samar da manufofin da za su kare masana’antun cikin gida da kuma hanzarta bunƙasa masana’antu.
Dangote ya ce, rukunin kamfanoninsa na ƙara faɗaɗa ayyukan jigilar man fetur da kayayyakin makamashi a Gabashi, Tsakiya da Kudancin Afirka, da nufin inganta wadatar makamashi, sauƙaƙa samun tataccen man fetur da kuma kawo ƙarshen matsalolin da suka daɗe suna kawo cikas ga samar da man fetur a nahiyar.
Attajirin ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da editan sashen Afirka na jaridar Financial Times, David Pilling, a taron ƙoli na FT Africa Summit da aka gudanar a birnin Landan na Birtaniya.
A yayin tattaunawar, Dangote ya bayyana cewa kamfaninsa ya sayi kaso 25 cikin 100 na hannun jari a tsarin bututun jigilar man fetur na Kenya. Ya kuma ce suna ci gaba da shirye-shiryen wasu manyan ayyukan more rayuwa da za su haɗa Djibouti da Habasha, tare da zuba jari a Kamaru da Namibiya.
A cewarsa, burin Afirka na samun sauyi mai ɗorewa a tattalin arzikinta zai yi wuya ya tabbata ba tare da zuba jari mai yawa a ababen more rayuwa da kuma samar da manufofin masana’antu da za su ƙarfafa sarrafa kayayyaki a cikin gida, kare ƙarfin samar da kayayyaki da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ba.
“Idan muka bari kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje su maye gurbin waɗanda ake samarwa a cikin gida, to muna fitar da ayyukan yi daga nahiyarmu ne, muna kuma shigo da talauci cikinta,” in ji Dangote.
Ya bayyana cewa shirin faɗaɗa harkokin jigilar man fetur wani ɓangare ne na babban tsari na samar da ingantacciyar hanyar samar da makamashi da za ta haɗa manyan matatun mai da kasuwannin da ba sa samun isassun kayayyakin makamashi. Waɗannan kasuwanni sun daɗe suna dogaro da man fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje da kuma hanyoyin rarraba kayayyaki marasa inganci.
Da aka tambaye shi game da shirin kamfaninsa na zuba jari a ma’ajiyar man fetur, bututun mai da sauran kayayyakin jigilar makamashi, Dangote ya ce suna gudanar da ayyukan ne cikin sauri da azama.
Ya bayyana cewa sun kammala sayen kaso 25 cikin 100 na hannun jari a hanyar bututun man fetur ta Kenya ne da goyon bayan gwamnatin ƙasar. A cewarsa, wannan mataki zai taimaka sosai wajen inganta jigilar tataccen man fetur a Gabashin Afirka.
“Bari na gaya muku, a jiya, tare da goyon bayan shugaban ƙasar Kenya, mun sayi kaso 25 cikin 100 na hanyar bututun da ake amfani da ita wajen rarraba kayayyakin man fetur,” in ji shi.
Dangote ya ce kamfaninsa na kuma gina wata babbar hanyar jigilar man fetur da za ta haɗa Djibouti da Addis Ababa, babban birnin Habasha. Shirin ya haɗa da gina wuraren ajiya da manyan tankunan man fetur domin sauƙaƙa jigilar kayayyakin mai da adana su cikin inganci.
Ya ƙara da cewa wani muhimmin aikin da suke gudanarwa a Kamaru ya kusa kammala, yayin da aka zaɓi Namibiya a matsayin muhimmiyar cibiyar da za ta taimaka wa kamfaninsa wajen shiga kasuwannin Kudancin Afirka.
Dangote ya bayyana cewa Namibiya ta dace da wannan shiri saboda kusancinta da matatar man fetur ta Dangote da ke Legas.
“Daga matatar manmu zuwa Namibiya, tafiyar jirgin ruwa na ɗaukar kusan kwanaki huɗu,” in ji shi.
Ya ce za a riƙa jigilar tataccen man fetur daga matatar Legas zuwa Namibiya, sannan a rarraba shi zuwa sauran kasuwannin da ke da alaƙa da ita, ciki har da Botswana da Afirka ta Kudu.
Ya kuma bayyana cewa kamfaninsa na nazarin wasu hanyoyin jigilar kayayyakin mai da za su kai ga Zimbabwe da Zambiya, a wani ɓangare na shirin kafa babbar hanyar rarraba man fetur da za ta mamaye nahiyar, tare da dogaro da wuraren ajiya da hanyoyin sufuri da aka tanada bisa tsari.
Wannan faɗaɗa harkokin rarraba man fetur na tafiya ne kafada da kafada da shirin gina wata sabuwar matatar mai a Lamu, Kenya, wadda ake hasashen za ta iya tace gangunan ɗanyen mai 700,000 a kowace rana.
Dangote ya ce bunƙasar tattalin arzikin Gabashin Afirka, ƙarfin ɓangaren haƙar ma’adanai da kuma ƙaruwa da buƙatar makamashi sun sa yankin ya zama wuri mai jan hankali ga masu zuba jari a harkokin matatun mai.
Ya bayyana cewa sabuwar matatar za ta riƙa samun ɗanyen mai daga kasuwanni daban-daban, maimakon dogaro da kayayyakin mai daga Kenya ko Uganda kaɗai. A cewarsa, hakan zai ba da damar sassauci wajen samo ɗanyen mai da kuma tabbatar da dorewar ayyukan matatar na dogon lokaci.
Ya ce binciken fasaha ya nuna cewa Lamu ce ta fi dacewa da aikin, saboda tana da damar karɓar manyan jiragen ruwa, kayayyakin more rayuwar sufuri ta ruwa da sauran muhimman abubuwan da ake buƙata wajen gudanar da matatar mai mai girma.
Dangote ya bayyana cewa sun kammala yanke shawarar zuba jarin a cikin watanni huɗu, duk da cewa, a cewarsa, wasu ’yan kasuwa masu muradin kansu sun yi ƙoƙarin kawo cikas ga aikin ta hanyar shigar da ƙara a kotu jim kaɗan kafin a sanar da shirin ga jama’a.
Baya ga ayyukan makamashi, Dangote ya jaddada muhimmancin samar da manufofin da za su kare masana’antun cikin gida daga gasar kasuwanci marar adalci. Ya ce ba za a iya samun bunƙasar masana’antu a Afirka ba idan aka bar masana’antun da ke tasowa su fuskanci shigo da kayayyaki ba tare da wani takunkumi ba daga ƙasashen da suka riga suka ci gaba a fannin masana’antu.
Ya tambayi dalilin da ya sa ya kamata a hana ƙasashen Afirka tallafa wa masana’antunsu na cikin gida, alhali kuwa ƙasashe masu ci gaba suna amfani da irin waɗannan matakai domin ƙarfafa masana’antunsu da samar da ayyukan yi ga jama’arsu.
Dangote ya yi nuni da matakan da manyan ƙasashen duniya ke ɗauka a baya-bayan nan, yana mai cewa kare masana’antun cikin gida wata sahihiyar dabara ce ta tattalin arziki da ƙasashe da dama ke amfani da ita.
“Idan har Amurka yanzu tana cewa za ta kare masana’antunta, to me ya sa mu a Afirka ba za mu kare namu masana’antun ba?” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa rukunin kamfanoninsa ya ware kusan dala biliyan 50 domin zuba jari tsakanin shekarar 2026 da 2030.
A cewarsa, shirin ba wai kawai na faɗaɗa harkokin kasuwancin kamfanoninsa ba ne, har ma yana da manufar nuna cewa kamfanonin Afirka na iya gudanar da manyan ayyukan masana’antu masu kawo sauyi a tattalin arziki.
“Abin tarihi da muke son bari a baya shi ne yadda za mu mayar da nahiyarmu ta zama cibiyar masana’antu,” in ji shi.
Dangote ya ce wannan shirin zuba jari zai kuma ƙarfafa gwiwar sauran ’yan kasuwa da masu zuba jari na Afirka wajen rungumar manyan ayyukan masana’antu da za su iya sauya makomar tattalin arzikin nahiyar.
Da yake magana kan sauran matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban nahiyar, Dangote ya lissafa ƙarancin wutar lantarki, raunin tsarin kuɗi da rashin ingantattun manufofin masana’antu a matsayin manyan abubuwan da ke hana tattalin arzikin Afirka bunƙasa yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa wutar lantarki muhimmin ginshiƙi ne ga ci gaban masana’antu, musamman a fannonin sarrafa kayayyaki, haƙar ma’adanai da sarrafa albarkatun ƙasa. A waɗannan fannoni, samun wutar lantarki mai ɗorewa yana da muhimmanci wajen ƙara wa albarkatun ƙasa ƙima kafin sayar da su.
Dangote ya ce kimanin ’yan Afirka miliyan 650 har yanzu ba su da damar samun wutar lantarki. Ya jaddada cewa magance wannan matsala zai buɗe ƙofofin samar da ayyukan yi, bunƙasa masana’antu da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga ƙasashen nahiyar.
Ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa Afirka, duk da yalwar albarkatun ƙasa, filayen noma da yawan matasa, ke ci gaba da fama da talauci.
A cewarsa, nahiyar tana da dukkan abubuwan da ake buƙata domin zama babbar cibiyar masana’antu a duniya, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne samar da tsare-tsaren da za su ba da damar amfani da waɗannan albarkatu wajen bunƙasa tattalin arziki.
Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Dangote ya nuna kwarin gwiwa kan makomar Afirka, yana mai cewa tuni nahiyar ta fara farkawa daga dogaro da shigo da kayayyaki zuwa ƙoƙarin bunƙasa masana’antunta.
“An riga an fara tafiya,” in ji shi. “Amma yanzu mun farka, kuma za mu tabbatar da cewa mun cimma burinmu.”



















