
Daga Bashir Bello, Abuja
Taron Open Mic with Shine na Shekara ta 2026 wanda aka gudanar a Harabar Physics, babban harabar Jami’ar Abuja, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Daliban Physics, ya cika alkawarin da aka yi masa na zama cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da farkar da tunanin al’umma. Mai shiryawa kuma wanda ya kafa shirin, Mr. Shine Enyinnaya Nwosu, ya ce an tsara shirin ne domin tada tunani mai zurfi ta hanyar abubuwan adabi, karatun waƙoƙi, gasar faɗar baiti, gabatar da gajerun labarai, da kuma jawabi mai ƙarfafa gwiwa daga baƙon mai jawabi.
Tun daga farkon Taron harzuwa karshen, mahalarta da waɗanda suka halarta sun yabi Mr. Shine bisa gina wani dandali na musamman da ya haɗa fasaha da tattaunawa kan matsalolin ƙasa ta hanyar wayar da Kan matasa.
Da yake gabatar da babban jawabi a kan taken “Nijeriya da Ɗabi’a,” Mr. Shine Enyinnaya Nwosu ya rushe ra’ayin da aka saba da shi na ɗora laifin rashin cigaban Nijeriya kawai a kan ‘yan siyasa. Duk da cewa ya bayyana cewa jawabinsa ba na siyasa ba ne, ya lura cewa ba za a iya tattauna ƙasa ba tare da mutanenta, cibiyoyinta, da shugabanninta ba.
“A matsayinmu na mutane masu tunani, kamata mu yi tunanin abin da za mu yi don gyara ƙasa maimakon zargin masu mulki,” ya bayyana cewa al’adar rashin ɗaukar nauyi ce ke ƙara jawo koma bayan ƙasa. Ya buƙaci ‘yan Nijeriya su daina jiran “Mai Ceto” su ɗauki nauyin kansu, yana mai cewa, “Kowa ya kamata ya yi aiki.”
Mr. Shine ya bayar da hujjar cewa cin hanci, talauci, da rashin tsaro ba su samo asali daga halittar jiki ba ne, illa dai daga al’ada da yadda aka reni mutum. Da yake kawo bayanai daga duniya, ya lura cewa ‘yan Afirka sun ci gaba da zama mafi talauci ko da a ƙasashe masu dimokuraɗiyya da shugabanni na gari, tun daga Amurka zuwa Afirka ta Kudu da Austiraliya.
“Ko kawo shugaban ƙasar Amurka mafi nagarta ya mulki Nijeriya, zai gaza. Sun riga sun mulka, kuma baƙaƙen fata a ƙasarsu sun ci gaba da zama talakawa,” in ji shi.
Ainihin abin da ke jawo matsalar, in ji shi, al’ada ce wani abu da ba ya numfashi amma yana da ƙarfi. Iyalai, makarantu, ƙungiyoyin addini, kafofin watsa labarai, da ƙungiyoyin abokai su ne ke tsara ɗabi’a, kuma idan waɗannan cibiyoyi suka lalace, al’umma za ta shan wahala.
Ya yi misali da labarin tagwaye da aka raba tun suna jarirai: ɗaya wanda iyaye masu ilimi da wadata suka rene ya zama injiniya; ɗayan kuma, wanda wata karuwa ta ɗauke shi, ya zama mai zamba. “Muhalli ne ya yi aiki,” in ji Mr. Shine.
Mai Gudanar da Sashen Yaɗa Labarai na Open Mic with Shine, Hussain AbdulQadir Zaguru, ya bayyana taron a matsayin wani shiri da ake yi duk bayan watanni uku domin taimakawa ɗalibai su fahimci ƙarfin adabi da faɗar baiti, musamman wajen shugabanci. Ya yabi Mr. Shine bisa hangen nesansa da jajircewarsa ga ci gaban matasa, yana cewa,
“Shine ya sanya a gabansa ya ƙarfafa matasa, shi ya sa ya fara da jami’a inda zai iya tuntuɓar su kai tsaye. Taron ya yi kyau ƙwarai kowa ya ga ƙarfin adabi yana tattauna muhimman batutuwa kamar ɗabi’a a Nijeriya domin mu zama jami’an canjin da muke fata.”
Zaguru ya shawarci matasa da ke cikin “jarabar Japa” da su fara bincikar kansu su nemi hanyoyin kawo sauyi a gida, domin “ba kowa ba ne zai iya barin ƙasar.”
Ya yabi Mr. Shine bisa kawo waɗannan muhimman batutuwa a gaba da kuma bai wa matasa dama su bayyana ra’ayinsu.
Da yake zantawa da manema labarai, Comrade Muhammad Abdulmajeed, Shugaban Sashen Physics, Jami’ar Abuja, ya yabi Mr. Shine bisa ɗaukar nauyin taron da kuma “sanya irin wannan babban amana ga ɗalibai.” Ya ce shirin ya yi tasiri ƙwarai kuma yana nuna abin da ɗalibai suka fi buƙata a yanzu.
“A ‘yan kwanakin nan, ɗalibai da dama suna kaucewa daga ainihin manufar zuwa makaranta, kuma hakan yana da alaƙa da batutuwan ƙima da ɗabi’a. Sakamakon taron ya yi daidai da taken da aka sa.

“Wasan kwaikwayon ya nuna a fili cewa ɗalibai sun san ƙalubalen da ke akwai kuma a shirye suke su yi magana a kai su kuma ƙarfafa sauyi. Wannan taron ya wuce nishaɗi kawai.” Da yake magana a madadin waɗanda suka yi nasara, wanda ya zo na farko, Enyojo Victory Abo, ya gode wa Mr. Shine bisa damar da ya samu ta halartar gasar, yana mai cewa, “Makomar Nijeriya tana hannunmu kuma dole ne mu shirya mu biya farashin.”

Wanda ya zo na farko ya tafi gida da kyautar Naira ₦100,000, yayin da na biyu da na uku suka samu ₦75,000 da ₦50,000 bi da bi. Baƙi sun bayyana Open Mic with Shine a matsayin wani kira na lokaci da ya dace na farfaɗo da ɗabi’u, suna yabon Mr. Shine Enyinnaya Nwosu bisa ƙarfin zuciyarsa, fayyace maganarsa, da kishin ƙasa da ya nuna.

















