
By Bashir Bello, Abuja
An kafa tarihi a jihar Kaduna yayin da Gwamna Uba Sani ya maida jihar cibiyar Koyon Sana’o’i da kwarewa ta Najeriya a cikin shekaru uku kacal da ya yi kan karagar mulki.
Cibiyar Horar da Sana’o’i da Ci gaban Kwarewa ta Jihar Kaduna, KIVTSD, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen mako, inda ta yaba wa gwamnan bisa jagorancinsa da hangen nesa da ya kawo sauyi na zahiri a rayuwar alumma
Ma’aikatan cibiyar KIVTSD ƙarƙashin jagorancin Provost Alhaji Husaini Muhammad, sun taya Gwamna Uba Sani murnar cikar shekaru uku a ofis. Cibiyar ta ce KIVTSD wacce aka gina a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Uba Sani tuni ta ke ba dubban matasa, ciki har da Mutanen da ke da Nakasa, kwarewa da aka amince da ita a duniya. Ta ce wannan nasara ta zama fitila ta sauyi ga matasan Najeriya baki ɗaya.
Ko da yake sabuwar cibiya ce, KIVTSD ta samu nasara a matsayin cibiyar jagora ta Najeriya wajen horar da sana’o’i da fasahar zamani. Tana da ƙarfin samar da Masu Koyon Sana’o’i 32,000 masu kwarewa a kowace shekara, tare da sansanonin zamani guda uku da aka kafa a dukkan yankunan sanata na jihar Kaduna. Wannan tsari ya sa Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohi.
Cibiyar KIVTSD ta ce tana cike gibin kwarewa ta hanyar shirye-shiryen da suka dace da bukatun masana’antu, waɗanda suka yi daidai da ƙa’idojin cikin gida da na ƙasa da ƙasa. Masu kammala karatu daga cibiyar suna samun takardar shaidar Recognition of Prior Learning, RPL, da Nigerian Skills Qualifications, NSQ, da sauran takardun cancanta da ke ba su damar yin aiki a ko’ina a duniya. Cibiyar ta tabbatar da cewa waɗannan matasa suna Kan Gaba Wajen kawo ci gaban kirkire-kirkire, tattalin arziki, da cigaban zamantakewa a fadin ƙasa.
Ana gudanar da horon a cibiyar ba tare da son zuciya na addini ko kabila ba, kuma ana neman ɗalibai masu ilimi na boko ko marasa ilimi. KIVTSD ta jaddada cewa tana aiki da tsarin haɗa kowa, inda mata da Mutanen da ke da Nakasa ke da wakilci mai ƙarfi a matsayin ɗalibai da kuma malamai. Wannan ya sanya cibiyar ta zama wuri na gari ga duk wanda ke son dogaro da kansa.
A ƙarshe, shugaban KIVTSD ya ce Gwamna Uba Sani ya yi abin da babu wani Gwamna da ya taɓa yi a tarihin Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai. Sun ce ya shimfiɗa tubali da za a tuna da shi har zuwa ƙarni masu zuwa, domin ya ba al’umma ba fata kawai ba, har ma da hanyar samun abin dogaro na hakika. Sun kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da ƙarfafa masa jagoranci don ci gaban jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.


















