• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Kasuwanci

DANGOTE: ƘARFAFA ƘERA KAYAN AMFANI A CIKIN ƘASA ITA CE HANYAR SAMUN ƘARFIN TATTALIN ARZIKI MAI DOREWA A NIJERIYA

October 4, 2026
in Kasuwanci
Reading Time: 5 mins read
0
Dangote: Ci Gaban Tattalin Arzikin Najeriya Ya Danganta da Ƙara Samar da Kayayyaki a Cikin Gida.
0
SHARES
10
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

By Bashir Bello, Abuja

Karanta HakananPosts

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote

Rukunin Kamfanonin Dangote ta yi kira ga Nijeriya da ta ƙara ƙaimi wajen bunƙasa masana’antun cikin gida, rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, tare da gina ƙarfin samar da kayayyaki da ake buƙata domin samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa da juriya.

Ƙamfanin ta bayyana cewa makomar tattalin arzikin Nijeriya na dogon lokaci za ta dogara ne da ikon ƙasar na samar da kayayyaki cikin inganci da farashi mai gasa domin amfanin cikin gida, tare da bunƙasa ƙarfin fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin yankuna da na duniya.

Daraktar Yanki kuma Babbar Mai Ba Shugaban Ƙungiyar Kamfanonin Dangote Shawara, Hajiya Fatima Wali-Abdurrahman, ce ta yi wannan kira yayin da take jawabi ga ɗimbin mahalarta taron bikin baje kolin kasuwanci na ƙasa da ƙasa na Abuja karo na 21.

Babban Manajan Ƙungiyar, Bello Dan-Musa, ne ya wakilce ta a wajen taron.
Ta bayyana cewa samun ƙarfin tattalin arziki na gaskiya ba wai kawai tsira daga lokutan matsin tattalin arziki ba ne, illa gina ƙarfin masana’antu da cibiyoyi da za su taimaka wajen rage dogaro da wasu ƙasashe.

Ta ce, “Ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya a ƙarshe zai dogara ne da wani muhimmin zaɓi: ko za mu ci gaba da shigo da kayayyakin da za mu iya samarwa a cikin gida, ko kuma mu gina ƙarfin samarwa, yin gasa da fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.”

Hajiya Fatima ta bayyana irin jarin da Ƙungiyar Kamfanonin Dangote ta zuba a muhimman sassa na tattalin arzikin Nijeriya, ciki har da siminti, takin zamani, sukari, sinadaran masana’antu da tace man fetur.

Ta ce waɗannan zuba jari sun nuna yadda ci gaba da saka hannun jari a samar da kayayyaki a cikin gida zai iya sauya masana’antu, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tsarin samar da kayayyaki a cikin ƙasa.

Ta lura cewa jarin da Dangote ya zuba ya taimaka wajen sauya Nijeriya daga ƙasar da ta fi dogaro da shigo da siminti daga ƙasashen waje zuwa ƙasar da ke samar da siminti tare da fitar da shi zuwa wasu ƙasashe.

Haka kuma, hakan ya samar da ayyukan yi tare da tallafa wa dubban kasuwanci a sassa daban-daban na tsarin samar da kayayyaki.

A cewarta, wannan manufa ce ta jagoranci zuba jarin ƙungiyar a sauran muhimman sassa, musamman masana’antar man fetur.

Ta bayyana cewa matatar man fetur ta Dangote, wadda a halin yanzu take aiki da ƙarfin tace kusan ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana, tana da shirin faɗaɗa ayyukanta domin kaiwa ga tace ganga miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekarar 2030.

Haka kuma, ta bayyana babban shirin faɗaɗa ayyukan ƙungiyar a faɗin Afirka, ciki har da shirin gina sabuwar matatar mai a Lamu, ƙasar Kenya.

Ta ce irin waɗannan zuba jari wani ɓangare ne na jajircewar ƙungiyar na dogon lokaci wajen ƙarfafa masana’antu da ƙarfin samar da makamashi a Afirka.

Ta ce manufar ba wai gina kamfanoni guda-guda kawai ba ce, a’a, ita ce samar da masana’antun da za su iya biyan buƙatun Afirka da ke ƙaruwa, tare da rage dogaron nahiyar kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Dangane da batun haraji, Hajiya Fatima ta jaddada muhimmancin samar da tsarin haraji mai tabbas da gaskiya, wanda zai tallafa wa ci gaban tattalin arziki tare da ƙarfafa gwiwar ‘yan kasuwa wajen zuba jari na dogon lokaci.

Ta ce haraji yana da muhimmanci wajen samar da kuɗaɗen gina ababen more rayuwa da gudanar da ayyukan jama’a, amma ta yi gargaɗin cewa dole ne a tsara manufofin haraji ta yadda ba za su kawo cikas ga harkokin kasuwanci, zuba jari da ƙarfin gasa ba.

Saboda haka, ta yi kira da a samar da manufofin gwamnati masu tabbas da kuma gaskiya, tana mai cewa ‘yan kasuwa suna buƙatar yanayin gudanar da ayyuka mai daidaito domin yanke shawarar zuba jari na dogon lokaci, faɗaɗa samar da kayayyaki da samar da ayyukan yi.

Wakiliyar Ƙungiyar Kamfanonin Dangote ta kuma yi tsokaci kan ci gaba da gudanar da tayin sayar da hannun jari ga jama’a a karon farko (IPO) na kamfanin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals FZE, inda ta bayyana shi a matsayin wata dama da ‘yan Nijeriya za su samu ta shiga cikin mallakar ɗaya daga cikin manyan jarin masana’antu a Afirka. Tayin ya ƙunshi hannun jari biliyan 4.1, inda ake sayar da kowane hannun jari a kan naira 525. Ana sa ran rufe tayin a ranar 13 ga Oktoba, 2026.

Ta ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama, tana mai cewa faɗaɗa damar jama’a su mallaki hannun jari a masana’antu wani muhimmin mataki ne na ƙara faɗaɗa shigar jama’a cikin harkokin kuɗi da tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya suna da kaso a sauyin da ake samu a fannin masana’antu na ƙasar.

Hajiya Fatima ta ce hangen nesa na ƙungiyar na shekarar 2030, wanda ke da burin gina daular kasuwanci mai darajar dala biliyan 100, ya wuce batun haɓaka kuɗaɗen shiga kawai.

Ta bayyana cewa wannan buri ya ta’allaka ne kan samar da kayayyakin da Afirka ke amfani da su, ƙirƙirar damammaki ga al’ummar nahiyar da ke ƙaruwa, bunƙasa ƙwarewar ma’aikata na cikin gida, da gina kamfanonin Afirka da za su iya yin gasa cikin nasara a kasuwannin duniya.

Ta jaddada cewa ƙarfin tattalin arzikin Afirka a nan gaba zai dogara matuƙa ne da ikon nahiyar na bunƙasa masana’antun da za su iya yin gasa, ƙarfafa hanyoyin samar da kayayyaki a cikin gida, da kuma tabbatar da cewa an riƙe kaso mafi girma na ribar tattalin arziki a cikin nahiyar.

Mataimakin Shugaban Farko na Ƙungiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Abuja (ACCI), Farfesa, Adesoji Adesugba, ya yaba wa Ƙungiyar Kamfanonin Dangote bisa ci gaba da tallafa wa bikin baje kolin kasuwanci na Abuja.

Ya bayyana kamfanin a matsayin babban ginshiƙi na bikin, tare da nuna cewa hakan shaida ce ta ƙarfin masana’antun Nijeriya wajen yin gasa a kasuwannin duniya.

Ya ce ƙungiyar na fatan ƙara zurfafa haɗin gwiwarta da Ƙungiyar Kamfanonin Dangote, tare da gano wasu ƙarin fannoni na haɗin gwiwa da za su samar da fa’ida mai yawa ga ‘yan kasuwa, masu amfani da kayayyaki da kuma tattalin arzikin Nijeriya.

Farfesa Adesugba ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin bunƙasa kasuwanci, zuba jari, ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

Ya lura cewa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyi da ‘yan kasuwa yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci da kuma buɗe hanyoyin amfani da damar tattalin arzikin Nijeriya.

Taron musamman na Ƙungiyar Kamfanonin Dangote, wanda aka gudanar cikin yanayi na farin ciki da armashi, ya samu halartar manyan shugabannin masana’antu, abokan hulɗar kasuwanci, jami’an gwamnati, masu zuba jari, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci bikin baje kolin kasuwanci na ƙasa da ƙasa na Abuja karo na 21.

Previous Post

ACI Ta Bukaci Masu Zabe a Arewa Su Bai Wa Jin Ci Gaban Alumma da Tsaro Muhimmanci a Zaben 2027

Next Post

Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote

Related Posts

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026
Kasuwanci

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

October 14, 2026
Auto Draft
Kasuwanci

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

October 8, 2026

Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano
Kasuwanci

Mambobin Ƙungiyar MAN Sun Yi Cincirindo a Rumfar Dangote Domin Neman Bayani Kan IPO na Matatar Mai a Taron AGM na Kano

September 25, 2026
Kamfanin Dangote Cement ta yi bikin Ranar Matasa a Obajana tare da sabunta kudirin ci gaban matasa.
Kasuwanci

Kamfanin Dangote Cement ta yi bikin Ranar Matasa a Obajana tare da sabunta kudirin ci gaban matasa.

August 19, 2026
Kamfanin Siminti na Dangote Ta Fara Amfani da Fasahar AI da Telematics Don Ƙarfafa Tsaron Sufuri
Kasuwanci

Kamfanin Siminti na Dangote Ta Fara Amfani da Fasahar AI da Telematics Don Ƙarfafa Tsaron Sufuri

June 7, 2026
Next Post
Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote

Bikin Kasuwanci: Samar da Kaya a Cikin Ƙasa Muhimmi Ne Ga Ƙarfafa Tattalin Arziki, in ji Dangote

Gwamna Yusuf Ya Tabbatar da Aiwatar da Bin Dokokin Zirga-zirga a Kano

Gwamna Abba Yusuf Ya Saki Naira Miliyan 235 Domin Ƙarin Girma Ga Ma’aikatan SUBEB 18,984

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

Kamfanin Simintin Dangote Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta 2026

October 14, 2026
Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

October 13, 2026
Auto Draft

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

October 8, 2026
Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Sakatarorin Dindindin Hudu

Ranar Malamai ta Duniya: Ba Za Mu Bar Malaman Katsina Su Yi Aiki Cikin Wahala Ba – Gwamna Raɗɗa

October 7, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin