Daga Bashir Bello, Abuja
Kungiyar Arewa Cohesion Initiative (ACI) ta yi kira ga masu kada kuri’a a Arewacin Najeriya da su zabi ‘yan takarar da suke da karfin iya ba da fifiko ga jin dadin jama’a da kuma magance dimbin kalubalen da ke addabar yankin.
Da yake magana a shirin safe na gidan rediyon Liberty Radio, wanda aka saurara a Kaduna a ranar Talata, Darakta Janar na kungiyar ACI, Dr. Abdullahi Idris, ya nuna mamakinsa kan yadda Arewa, wadda take da mafi yawan masu kada kuri’a a kasar, ke ci gaba da kasancewa yankin da ya fi fama da talauci da kuma rashin tsaro.
Saboda haka, Dr. Idris ya yi kira ga masu kada kuri’a da su kasance masu fifita muradun kansu a wannan karon, ta hanyar zabar ‘yan takarar da za su iya samar da mafita ga matsalolin yankin, wadanda suka hada da rashin tsaro, rashin aikin yi ga matasa, koma-bayan ilimi, matsalar almajirci da kuma talauci.
Yayin da yake ishara da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bayyana cewa tsaro da jin dadin jama’a su ne manyan manufofin gwamnati, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa mafi yawan zababbun jami’an gwamnati daga yankin suka kasa cika alkawuran da suka dauka a lokacin rantsuwar kama aiki, lamarin da ya haifar da halin da Arewa ke ciki a yanzu.
Darakta Janar na kungiyar ACI ya kuma jaddada muhimmancin shugabanci nagari, hadin kai da kuma zaman tare a matsayin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen samar da mafita ga matsalolin yankin da kuma cimma burin ci gaba.
Ya kuma yi magana kan wasu matsalolin da ke addabar Arewa, ciki har da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma rashin kyakkyawan shugabanci, inda ya yi kira ga shugabannin yankin da su kara kaimi wajen tunkarar wadannan matsaloli kai tsaye.





















