Daga; BAshir Bello, Abuja
DAN takarar Majalisar Dattijai ta Jihar Kano ta tsakiya, a karkashin Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Dakta Nafiu Sankara, ya bayyana cewa kishin ganin cigaban al’umma ne ya sanya shi tsayawa takarar kujerar Sanata ta Majalisar Dattijai.
Dakta Sankara ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai inda ya nuna cewa duk mutumin da yake kishin al’umma zai ga akwai dubban dalilan da zai sa ya bada ta shi gudunmuwar wajen ganin an kawo cigaba ga al’umma.
Ya kara da cewa a matsayinsa na Matashi, a kullum suna ganin cewa su ya kamata mu jagoranci abubuwan da zai kawo cigaban al’umma domin su ne kaso mafi yawa a cikin al’umma.
Acewarsa, Idan ana maganar cewa wani ya dade yana yi, sai a duba a ga yaushe ya soma musamman idan aka duba tarihin siyasar Jihar Kano, za a ga mafi akasarin mutanen da su ka yi suna, kuma su ke bada gudunmuwa a fanni na Siyasa, sun soma ne saboda damar suka samu da karancin shekaru.
Ya ce, “kasancewar sun fara yin takara tun suna matasa shi ne dalilin da yasa suka jima kuma har suka samu wannan gogewar da ake gani har ake cewa sun jima sun goge. Misali shi ne marigayi tsohon Gwamnan Jihar Kano na farar hula Alhaji Abubakar Rima don lokacin da ya zama Gwamna yana shekaru talatin da Yan kai.
“Haka shi ma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso lokacin da ya zama Mataimakin Kakakin Majalisa na Kasa yana da shekaru talatin da shida, haka Sardaunan Dutse yana da shekaru talatin ya zama minista kuma kamin nan yana Majalisa a matsayin dan Shekara ashirin da biyar kuma damar da suka samu ne lokacin da suke da karancin shekaru yasa suka dade a Majalisar har suka samu gogewa.
“Don haka a matsayina na matashi, wannan ba tafiya ta ba ce ni kadai, tafiya ce ta Matasa domin mun duba mun hangi cewa akwai bukatar mu shiga cikin harkokin Siyasa domin a dama da mu kuma ba wannan ne karo na farko ba domin a baya na shiga takara ta Majalisar Dattijai a karamar Hukumar mu ta Tarauni amma Allah ba nufa ba.
“Amma hakan bai sa mun yi kasa a gwiwa ba ko mun gajiya ba shi ne yasa na sake fitowa takara a yanzu tare da sahalewar Yan uwana Matasa da iyayen mu maza da mata, kuma muna fatan Allah zai shiga ciki Ya dafa mana.” Inji Shi
Dan takarar Dakta Sankara, ya ci gaba da cewa Ita Siyasa magana ce ta mutane kuma ta al’umma da yawa, don ba kallon mutum za a yi ba a matsayin na wane don ya jima yana kaza, face magana ce a kan su waye masu zaben kuma ina hankalin su yafi rinjaya.
Ya kara da cewa da bayar da tabbacin cewa a bana siyasar Jihar Kano ta tsakiya za ta ba da mamaki domin za ta fitar da sabon samfurin Siyasa saboda an daina ta Uban gida da ta Jam’iyya ko kana cikin Gwamnati, illa kawai mutane za su duba su ga wa ya kamata su aika ya je ya yi musu wannan aikin.
“Babban abin da muka maida hankali a wannan tafiyar ta mu shi ne mun zauna mun mayar da hankali mun fitar da abu hudu, na daya yana da alaka da abun yi ga Matasa wato ayyukan yi, kuma ba wai a dauke su aikin Gwamnati kawai ba don za mu kuma mayar da hankali wajen horar da su a kan sana’o’i na zamani wajen shigo musu da abubuwan da za su yi tamkar yadda ya ke a wasu kasashe.
“Na biyu akwai abin da ya shafi kiwon lafiya don akwai karancin ma’aikatu musamman a kan abin da ya shafi Kula da lafiya a matakin farko daga Gwamnatin Tarayya a nan Kano ta tsakiya domin babu su dayawa, don haka mu ke son mu yi amfani da wannan damar wajen shigo da su musamman don kula da kananan yara.
Bayan nan akwai abin da ya ke da alaka da Ilimi domin Ilimi haske ne kuma anan Kano ta tsakiya muna fama da matsaloli a kan abin da ya shafi kananan yara da su ke yawo a titi basa zuwa makaranta amma sai dai yadda ake fadar adadin su bai kai haka ba saboda akwai yara wanda almajirai ne na tsangaya amma saboda yanayin da mu ka tsinci kan mu, sai ya zamana aka saki wannan Karatu na tsangaya kuma aka masa rikon sakainar kashi ba a kulawa da shi.
“Haka kuma wani abin takaici shi ne za a ga Yan siyasar mu za su iya zuwa makarantun boko su gina musu ajujuwa amma ba za su iya zuwa makarantun tsangaya domin a samar musu da wajen Karatu mai kyau ba, balle har a Kula da darrusan su.
Sannan abu na karshe yana da alaka da shi kan shi ainihin aikin Dan Majalisa wanda yake yin doka na tattalin arziki, wanda idan aka duba za a ga Masana’antu dayawa sun Mutu kamar yadda a kwanakin baya an zo da wani tsari na kulle bakin iyaka inda aka koma Norma tare da sarrafa shinkafa a nan Jihar Kano, amma daga baya an zo an sake sakin bakin iyaka wanda ya yi sanadin rushewar Kamfanoni tare da haifar da rashin aikin yi wanda shi kuma ya ke alaka da matsalar rashin tsaro da abubuwa dayawa.
“Don haka, za mu mayar da hankali wajen samar da gurabe wanda idan aka bi su za a samar da cigaban tattalin arzikin Jihar Kano, a cewar Dan takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya Dakta Nafiu Sankara.”
Dan takarar ya shawarci Matasa da kar su yarda a zo a din ga amfani da su a lokutan zaben wanda bayan idan an kafa Gwamnati sai a yi watsi da su inda su ke komawa zuwa ga cewa za su yi zanga-zanga, don haka gara ace mutum ya aika da wanda ya ke da kusanci da shi kuma su ke da kamanceceniya na tunanin yanayin rayuwa, saboda wadanda su ke Jagoranci a yanzu, a yanayin tunaninsu ya sha bamban da na al’umma.
Hakazalika, ya kara da jan hankalin Matasa Yan uwasa da su fito su yi wannan tafiyar ta kwatar yanci don sun yarda su suke da kaso mafi yawa a cikin al’umma, saboda haka yana da kyau su nuna cewa wannan ga ra’ayin su, ga tsarin su don ita kadai ce mafita ga Kasar baki daya ba ma Jihar Kano kawai ba.
Daga karshe, Dakta Sankara ya gargadi Matasa a kan su gukewa duk wata hanya ta daukar doka a hannun su domin yin hakan yana nuna alakar shugabanni da Matasa, sannan mafita ita ce a ranar zabe su je su zabi wanda su ka yarda da amincin masa kana su tsaya su kare kuri’ar su wanda hakan shi ne mafita.





















