
Daga; Bashir Bello, Abuja
KAMFANIN Man Fetur na Najeriya (NNPC Limited), ta lashe kyautar Ƙungiyar ‘World Branding Forum’ (WBF) ta 21 a fannin sayar da man fetur, saboda rawar da ta taka wajen kawo sababbin dabaru a Najeriya da kuma kafa ma’aunin kwarewa a fannin sayar da man fetur a kasar.
A wata takardar sanarwar dake dauke da sa hannun Babban Jami’in Sadarwa na Kamfani, Andy Odeh, ya bayyana cewa an bai wa kamfanin wannan babbar kyauta ne a yayin bikin bayar da kyaututtuka na Ƙungiyar WBF na shekarar 2026-2027, wanda aka gudanar kwanan nan a fadar Hampton Court da ke birnin Landan.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ‘World Branding Forum’ (WBF), Richard Bowles, ya bayyana cewa suna taya NNPC Limited murna bisa samun amincewar jama’a, samar da kyakkyawan ayyuka, da kuma ci gaba da daukaka sunan NNPC tare da kafa ma’aunin kwarewa a fannin sayar da man fetur a Najeriya da ma kasashen waje.
Bowles ya kara da cewa, an zabi NNPC Limited ne bayan an gudanar da tsarin tantancewa mai zurfi, wanda ya hada da kimanta darajar kamfani, bincike kan kasuwar masu amfani da kayayyaki, da kuma kada kuri’a ta yanar gizo daga jama’a.
“Kun cancanci wannan kyauta, kuma ya kamata mutane su sani, ku sanar da abokan cinikayyarku, ku sanar da ma’aikatanku, ku sanya shi a shafin yanar gizonku da kuma cikin ayyukanku na tallata hajoji,” inji Bowles.
Da yake jawabi bayan karbar kyautar, Manajan Darakta na NNPC Retail Ltd., Huub Stokman, ya nuna godiyarsa ga WBF bisa wannan karramawa.
Ya jaddada cewa, hakan zai karfafa wa kamfanin gwiwar kara himma wajen samar da ingantaccen ayyuka da gogewa mai kyau ga dimbin abokan cinikayyarku.
Stokman, wanda Darakta mai kula da ayyuka na NNPC Retail Ltd., Baba Kukawa, ya wakilta, ya sadaukar da kyautar ga dukkan ma’aikatan kamfanin. Ya kara da cewa, kamfanin na amfani da fasahar zamani don ingantawa da fadada ayyukanta.
Haka kuma, a wajen taron akwai Manaja mai kula da harkokin Sadarwa da Gudanar da Sunan Kamfani (Brand Management) na NNPC Ltd., Mista Mohammed S. Umar, da kuma Manaja mai kula da Tallace-tallace na NNPC Retail Ltd., Uwargida Henrietta A. Ogon.
‘World Branding Awards’ (WBA) wani shiri ne na kasa da kasa da ke karrama sunayen kamfanoni, wanda ‘World Branding Forum’, wata kungiya ce mai zaman kanta da ke birnin Landan ke gudanarwa.
An kafa kungiyar WBA a shekarar 2014, kuma ta shafe sama da shekaru goma tana gudanar da ayyukanta, inda take karrama manyan sunayen kamfanoni (brands) a matakin duniya, yanki, da kasa, ta hanyar tsarin tantancewa mai matakai uku: kimanta darajar kamfani, zaben jama’a, da kuma binciken kasuwa.
Wadannan kyaututtuka suna bayar da karin girma ga nasarorin da aka samu wajen gina sunan kamfani, samun amincewar masu amfani da kayayyaki, da kuma tasiri a kasuwa a fannoni daban-daban na kasuwanci a duk fadin duniya.
Daga cikin wadanda suka taba karbar wadannan kyaututtuka a baya, akwai shahararrun kamfanonin samar da makamashi irin su Abu Dhabi National Oil Company (ADNOC) Distribution da kuma PTT Stations.



















