Daga Bashir Bello, Abuja
Fitowar Hajiya Amina Lawal Rafindadi a matsayin ‘yar takara a Gundumar Sanata ta Katsina ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ana ganin alama ce ta alheri ga mutanen yankin. Takararta tana nuni da sabon salo na shugabanci da ke ba da fifiko ga ƙirƙira, haɗa kowa, da ci gaban al’umma daga ƙasa.
Tare da zurfin alaƙarta da Katsina, inda ta girma kuma ta yi karatu, ta kawo fahimtar ƙalubalen da mutanenta ke fuskanta da kuma ƙudurin magance su kai tsaye.
Da take zantawa da manema labarai a sakatariyar ADC da ke Abuja, Hon. Amina Rafindadi ta yi alƙawarin canza rayuwar mutanen mazabarta ta hanyar kafa gidajen solar domin ƙara yawan wutar lantarki da rage dogaro da wutar ƙasa baki ɗaya.
A cewarta, wannan shiri ba kawai zai samar da makamashi mai ɗorewa ba, har ma zai ƙarfafa ƙananan ‘yan kasuwa, musamman waɗanda mata ke gudanarwa.





















