Duba da yadda Jihar Zamfara take gaba, gaba cikin jihohin da suke fama da tsaro a jerin jihohin dake Nijeriya. Duba da yadda Gwamnatin Jihar ta yanzu ta kasa shawo matsalar tsaro da kare rayukan al’umar ta, yana da kyau al’umar jihar su sake nazari da baiwa tsohon jami’in tsaro AIG Musa Yusuf Garba daman kawo karshen wadannan ‘yan ta’addan da sauran matsalolin raya Jihar da taka samu a karkashin Jam’iya mai mulki.
Musa Yusuf Garba kamar yadda aka sani. Yayi ritaya ne a matsayin Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda AIG na hukumar ‘yan Sanda ta kasa. Wanda hakan ya bashi daman sanin makaman aikin da sanin harkar tsaro idan muka yi la’akari tare da kawo misali da Jihar Kaduna a lokacin daya riketa a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda. A lokacin duk wasu matsalolin na tsaro daya tarar sai da yaga bayansu.
A wannan lokacin da yake aikin kaki mutanen Jihar Zamfara sun shede irin aiki tukuru da yayi domin bautawa kasar sa. Haka nan kuma ba a boye yake ba an sheda yadda ya taimakawa al’umar jihar sa da taimakawa matasa shiga aiyukan tsaro da kuma samarmusu gurabe a ma’aikatu da dama na gwamnatin tarayya. Wannan yake alamta cewa idan har ya samu daman zama gwama zai daura ne kawai daga abubuwan da yake yiwa Jihar da al’umar jihar.
Jihar Zamfara tana bukatar mutanen da zasu samarmata tsaro da zaman lafiya, da kuma ci gaba na raya kasa ba tare da la’akari da jam’iyar wanda zai iya samar musu da wadannan ci gaban ya ke ba.
Lokaci yayi da mutanen Zamfara zasu baiwa Musa dama su morewa arzikin da Allah Ya albarkaci Jihar dasu. Babu shakka hanya guda da Zamfara da al’umar ta zasu dawo cikin hayyacinsu shine baiwa Musa Yusuf Garba damar zaman Gwamnan Jihar a zabe mai gabatowa.




















