• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Siyasa

Duk Gwamnonin Da Ke Hana Filin Taron Siyasa Yankan Rake Ne – Sanata Ningi

November 21, 2026
in Siyasa
Reading Time: 5 mins read
0
Duk Gwamnonin Da Ke Hana Filin Taron Siyasa Yankan Rake Ne – Sanata Ningi
0
SHARES
12
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daga; Bashir Bello, Abuaj

DAN Majalisar Dattijai mai wakiltar shiyyar Jihar Bauchi ta tsakiya a Tarayyar Najeriya, Sanata Abdul Ningi, ya bayyana cewa duk Gwamnonin da ke kokarin hana wasu yan siyasar da ba Jam’iyyar su daya ba yin gangamin Siyasa a Jihohin su ba ki ne da ba su jima a harkar Siyasa ba.

Karanta HakananPosts

Abubuwa 4 Ne Su Ka Saka Ni Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya – Dakta Sankara

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Sanya Sarautun Gargajiya A Cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

An karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Da Lambar Yabo Ta Girmamawa

Sanata Abdul Ningi, wanda ya kasance Shugaban kwamitin harkokin wasanni a Majalisar Dattijai ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja.

Acewar sa, idan ba a mayar da hankali ba a kan wannan lamarin, matsifar da ta ke tafe za ta iya haifar da hana a yi zabe ko kuma idan an yi zaben ta zama ba mai inganci ba saboda babu kwanciyar hankali da lumana kamin zaben.

Ya kara da cewa abu daya ko biyu daya sani shi ne, shi ma dan Najeriya ne kuma mai son zaman lafiya kuma shi dattijo ne sannan Siyasa ta kan canza wanda ada su ne suke gudanar da Gwamnati a karkashin PDP kafin APC ta zo.

Hakazalika, duk wani abu kamin a yiwa Shugaba Bola Tinubu an yiwa Atiku, ba wai kuma jita-jita ba don a lokacin yana Birnin Kebbi haka na Sakkwato, kuma ya ji labarin abin da aka yiwa Obi da Sowore amma duk lokacin da aka ce Shugaban Kasa, toh ya wuce abin wasa amma idan kuma aka masa abu ya zama kankat kenan.

Sanata Ningi ya ce, “ganin yadda ita Gwamnati ta ɗauki abun da cewa ta na da karfin ta yi ko ta hana a duk lokacin da ta gadama, toh an nuna mata a yanzu cewa Yan Najeriya suna da karfin da za su iya yin wadannan abubuwan amma wannan abubuwan da ake yi ba shi ne demokoradiyya ba, domin demokoradiyya ita ce ka jira ka yi amfani da kuri’ar ka domin cimma manufar ka.

“Babu shakka, mutanen Najeriya sun kawo iya wuya saboda wahala, kuma abu ne da yan siyasa ya kamata su yiwa kan su fada musamman masu tazarar shekaru wanda sun ga jiya sun ga yau, kuma sun san abin da wasu ke kokarin su yi ta nuna karfin mulki ba mafita ba ce, saboda haka na kawo wannan kuduri domin a nunawa Yan Najeriya cewa ba wannan tafarkin ba ne.

“Wasu dayawa daga cikin mutanen da su ke cikin sanatoci sun nuna cewa ba su jidadin da na yi maganar Obi da Atiku ba saboda wannan abun ya faru da Shugaban Kasa, shi yasa na bude lamarin domin nuna cewa ba al’amari ba ne wanda aka ware wani domin an yiwa wasu kamin a yiwa Shugaban Kasa.

“Sannan su jami’an tsaro su sani cewa aikin su na duka Yan Najeriya ne bawai ga Gwamnati da ta ke ci ba kadai domin wadanda ba sa cika ma hakki ne a gare su na kare mutuncin su da sauran shugabanni, saboda da mu ka je Sokoto Otel, an hana mu masauki amma har wasu na yi mana dariya.

“Mu abin da muka sani shi ne tun a shekarar 1999 idan ko da tsohon Shugaban Kasa ne ya je wani waje, hakki ne ga Gwamnati ta ba shi masauki, haka ko da Mataimakin Shugaban Kasa ne, kuma a ba shi filin da zai yi siyasa, toh amma an zo an kwabkwaba alamarin wanda shi ne ya ke jawo wannan tashin hankalin.

“Toh amma na zo na ga bayanin Shugaban Kasa kuma ya yi kira ga su Gwamnoni kan cewa dole su canza salo domin su suke mayar da lamarin na a Mutu ko ayi rai, amma lokacin da mu ke je Bauchi dukda ba ma Jam’iyya daya da shi Gwamnan, ya ba da filin taro tare da masauki wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma mu da sauran Yan Najeriya mun yaba.” Inji Shi

Acewar sa, abin Sanata Kawu Sama’ila ya fada na goyon bayan kudirin da ya gabatar gaskiya ne domin a duk lokacin da aka ga yara sun yi gungu, toh wani dan Siyasa ne ya dauke su haya kuma wannan ya ta’alaka ga yadda Matasa su ka samu kan su cikin kuncin rayuwa ba aikin yi, wanda da Naira dubu daya ko dubu biyar aka ba wani da niyar ya yi jifa sai ya yi jifan.

“Ni ina cikin Mota a Kebbi, na ga yaro ya ɗauki Dutse a gaban ofishin APC da za mu shiga Birnin Kebbi ya jefo mana amma Allah Ya taimake ni dutsen bai iya shigowa ba, don haka dama duk abin da aka gani laifin Yan siyasa ne da kuma laifin rashin Ilimi na matashi wanda bai ji ba bai gani ba da rana daya za a zo a dauke shi a bashi Kudi, amma ba zai sake ganin Dan Siyasa ba sai bayan shekaru hudu ba.

“Kuma wannan Dan siyasar ne zai sake zuwa ya ce ka zo ka fatattaki wasu mutane, shi yasa na ke cewa maganin wannan mutanen shi ne Matasa su tabbatar sun yi rejista domin cire wanda za su cire, sannan su zabi sabobbin mutanen da suke ganin za su iya musu aiki.

“Ni ban taba daukar harkar Siyasa na ko a Mutu ko ayi rai ba, idan mutane sun ga ka yi, su zabe ka saboda ni ban ga amfanin karfafa cewa sai abin ya zama dole ba, domin daga ranar da ka ce wannan abun ya zama dole, toh an fita daga tafarkin demokoradiyya, illa kawai abar mutane su yi hukuncin su domin duk tsuntsun daya jawo ruwa shi ruwa zai duka, cewar Sanata Ningi.”

Ya ci gaba da cewa Idan aka duba duk wadannan Gwamnonin da ke irin wannan dabi’ar hana wasu zuwa yin gangamin Siyasa a Jihohin su, duk yankan rake ne domin ba su nuna a Siyasa ba saboda ada ai da Atiku ba Bola Tinubu duk a Jam’iyyar daya su ke amma a yanzu su ka rabu, toh meye tabbacin gobe ba za su sake hadewa ba, shi yasa ba a so a tsawala, ba a so a saka gaba a cikin lamarin.

Acewar sa, shin mene ne filin wasa wanda a rana daya za azo a ta fi saboda tamkar Kasuwa ce wacce ba za a ce ga wanda mutum zai sayi abu ko kar ya kasa wannan hajar domin mai so ne kawai zai iya saya, kuma duk masu irin wannan dabi’ar ba su san komai a harkar Siyasa ba kuma sun tabbatar ba zaben su aka yi ba.

Ya ce, “amma duk wanda yasan an zabe shi kuma yasan mutuncin talaka da demokoradiyya, toh ba zai yi irin wannan dabi’ar ba.”

Ya kara da cewa a duk lokacin da aka yi maganar Matasa ko da za a aibota su dole ne a tausaya musu, domin tunanin su daban, karfin jikin su daban da yadda suke ganin alamura daban, don haka shawarar da zai ba Matasa shi ne kar su bari yan siyasa su yi amfani da su domin burin kan mu.

Bugu da kari, su ɗauki mataki tun daga farko kan cewa idan ba ka musu aiki ba, gobe ka gani a kuri’ar ka saboda wannan fadace-fadacen ba shi ne mafita ko da ance wadanda aka kama Shugaban Kasa ya ce a sake su domin akwai wadanda ba su ji ba su gani ba amma anzo an kama su.

Daga karshe, Dan Majalisar Sanata Abdul Ningi, ya kara da bayyana cewa ya kamata su guji yin irn wannan abubuwan duk da yasan suna cikin matsatsin rayuwa kamar yadda kowa ke cikin matsatsin rayuwa, illa kawai su yi kokarin fitar da duk wasu gurbatattun yan siyasa ta hanyar kuri’ar su.

Previous Post

NNPC Da CBN Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Inganta Kudaden Makamashi

Next Post

Abubuwa 4 Ne Su Ka Saka Ni Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya – Dakta Sankara

Related Posts

Abubuwa 4 Ne Su Ka Saka Ni Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya – Dakta Sankara
Siyasa

Abubuwa 4 Ne Su Ka Saka Ni Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya – Dakta Sankara

November 21, 2026
An Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Sanya Sarautun Gargajiya A Cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya
Siyasa

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Sanya Sarautun Gargajiya A Cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

November 14, 2026
An karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Da Lambar Yabo Ta Girmamawa
Siyasa

An karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Da Lambar Yabo Ta Girmamawa

November 4, 2026
ACI Ta Bukaci Masu Zabe a Arewa Su Bai Wa Jin Ci Gaban Alumma da Tsaro Muhimmanci a Zaben 2027
Siyasa

ACI Ta Bukaci Masu Zabe a Arewa Su Bai Wa Jin Ci Gaban Alumma da Tsaro Muhimmanci a Zaben 2027

October 3, 2026
YANKIN AREWA TA ZABI HANYAR DA TAKESO: ABBAS NA JAMIYAR ADP YA GINA TSARI A KAN KANANAN HUKUMOMI 774 KAFIN 2027
Siyasa

YANKIN AREWA TA ZABI HANYAR DA TAKESO: ABBAS NA JAMIYAR ADP YA GINA TSARI A KAN KANANAN HUKUMOMI 774 KAFIN 2027

August 11, 2026
Shugabar Jamiyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana
Siyasa

Shugabar Jamiyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana

August 1, 2026
Next Post
Abubuwa 4 Ne Su Ka Saka Ni Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya – Dakta Sankara

Abubuwa 4 Ne Su Ka Saka Ni Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya - Dakta Sankara

Dangote Coal Ta Bayar Da Tallafin Karatu Na 2026/2027 Ga Dalibai 42 A Jihar Kogi

Dangote Coal Ta Bayar Da Tallafin Karatu Na 2026/2027 Ga Dalibai 42 A Jihar Kogi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

November 26, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

November 25, 2026

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

November 25, 2026
NNPC Ta Lashe Kyautar Duniya Ta Ƙungiyar WBA Bisa Kyawawan Ayyukanta A Fannin Sayar da Man Fetur

NNPC Ta Lashe Kyautar Duniya Ta Ƙungiyar WBA Bisa Kyawawan Ayyukanta A Fannin Sayar da Man Fetur

November 22, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin