• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Labarai

Gwamnan Osun, Masana Ilimi da Sarakunan Gargajiya Za Su Halarci Bikin Cika Shekaru 40 na KIDVARC

November 26, 2025
in Labarai
Reading Time: 2 mins read
0
Gwamnan Osun, Masana Ilimi da Sarakunan Gargajiya Za Su Halarci Bikin Cika Shekaru 40 na KIDVARC
0
SHARES
31
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daga Bashir Bello, Abuja

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, mataimakinsa Prince Kola Adewusi, da sauran mambobin majalisar zartarwa ta jihar sun shirya halartar bikin cika shekaru 40 da kafuwar makarantar KIDVARC Nursery, Primary da Sakandare School da ke Iree, Karamar Hukumar Boripe ta Jihar Osun.

Karanta HakananPosts

Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025

DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci

NNPC Ltd da Dangote Group Sun Kulla Yarjejeniya Don Inganta Tsaron Makamashi don Bunƙasa Najeriya

Hukumomin makarantar KIDVARC Nursery, Primary da Sakandare, Iree sun bayyana cewa shirye-shiryen bikin cika shekaru 40 da kafuwar KIDVARC Nursery da Primary School da kuma shekaru 30 da KIDVARC High School sun yi nisa.

Ana kuma sa ran zuwan sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na ƙasa, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, daliban makarantar na yanzu da na baya, da tsofaffin daliban tsohuwar Kwalejin Ilimi ta Jihar Oyo, wadda yanzu ta koma Kwalejin Ilimi ta Jihar Osun da ke Ila-Orangun, inda marigayi Dr. Samuel Oyedokun Omotoso ya kasance Provost na farko.

Haka kuma, za a gudanar da bikin tunawa da marigayi Dr. Omotoso, wanda ya kafa makarantar, a matsayin cika shekaru 15 da rasuwarsa a lokacin bikin.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai na bikin, Pastor Bamigbola Gbolagunte ya fitar, an bayyana cewa za a fara bikin ne a ranar Alhamis, 11 ga Disamba 2025 da taron manema labarai a dakin taro na Ojuolape, makarantar KIDVARC, Iree da karfe sha daya (11am) na safe.

Acewar Sanarwar “Za a kaddamar da ayyukan da aka kammala a makarantar a ranar Juma’a, 12 ga Disamba 2025, sannan za a ci gaba da taron cin abinci da haɗuwa da tsofaffin dalibai.”

Ta ƙara da cewa: “Za a gudanar da babban taron karshe na bikin a ranar Asabar, 13 ga Disamba 2025, inda za a ƙaddamar da littafi mai suna ‘50 Years of Talking and Chalking’ wanda marigayi Dr. S.O Omotoso ya rubuta, da kuma gabatar da laccar bikin a Leisure Spring Hotel, titin Iwo/Ibadan, Osogbo da karfe goma (10am) na safe.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da bikin tunawa da marigayi Dr. Omotoso a wannan rana da kuma a wannan wuri, inda ake sa ran manyan baki za su halarta.

Marigayi Dr. Omotoso ya kasance Sakataren Gwamnatin Jihar Osun a lokacin gwamnatin farar hula ta farko karkashin marigayi Sanata Isiaka Adetunji Adeleke, kuma ya bayar da gudunmawa mai yawa wajen ci gaban jihar, musamman a fannin ilimi.

Previous Post

NNPC Limited Ta Bayyana Ribar Naira Tiriliyan 5.4

Next Post

Majalisar Dattawa Ta Nemi Ƙarin Cibiyoyin Maganin Ciwon Sankaran Jini (Sickle Cell)

Related Posts

Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025
Labarai

Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025

February 26, 2026
DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci
Labarai

DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci

February 26, 2026
NNPC Ltd da Dangote Group Sun Kulla Yarjejeniya Don Inganta Tsaron Makamashi don Bunƙasa Najeriya
Labarai

NNPC Ltd da Dangote Group Sun Kulla Yarjejeniya Don Inganta Tsaron Makamashi don Bunƙasa Najeriya

February 21, 2026
Kwamitin Majalisar Wakilai Akan Alhazai ya Gargadi NAHCON Kan halin KO innl kula da Kasafin kudi
Labarai

Kwamitin Majalisar Wakilai Akan Alhazai ya Gargadi NAHCON Kan halin KO innl kula da Kasafin kudi

February 21, 2026
Kamfanin Siminti ta Dangote Cement Ta Kaddamar da Sansanonin Tsaro a garuruwan Jihar Kogi
Labarai

Kamfanin Siminti ta Dangote Cement Ta Kaddamar da Sansanonin Tsaro a garuruwan Jihar Kogi

February 19, 2026
Makkah is Calling, but NAHCON Lost the Key
Labarai

Makkah is Calling, but NAHCON Lost the Key

February 13, 2026
Next Post

Majalisar Dattawa Ta Nemi Ƙarin Cibiyoyin Maganin Ciwon Sankaran Jini (Sickle Cell)

Wase Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Danganta Matsalar Tsaro da Addini.

Wase Ya Gargadi 'Yan Najeriya Kan Danganta Matsalar Tsaro da Addini.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
“Dole ne mutum ya kasance mai taka-tsantsan da haƙuri kafin yin kasuwancin waya” — Abba

“Dole ne mutum ya kasance mai taka-tsantsan da haƙuri kafin yin kasuwancin waya” — Abba

December 30, 2025
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
AREWA: Ina Alfaharinmu na Arewa?

AREWA: Ina Alfaharinmu na Arewa?

February 28, 2026
Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka

Dangote Cement, Sinoma Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dala Biliyan 1 Don Ayyukan Siminti a Fadin Afirka

February 27, 2026
Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025

Keyamo Ya Gabatar da Tsarin Kasafin Kuɗi na 2026 ₦184.39bn Ga Majalisar Dokoki, Ya Bayyana Nasarorin 2025

February 26, 2026
DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci

DHQ Ta Tara Dakarun Afirka Ta Yamma Domin Samar Da Dabarun Yaki Da Ta’addanci

February 26, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by