GCEO na NNPC Ltd, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, wanda Manajan Darakta na Gidauniyar NNPC, Mrs. Emmanuella Arukwe (a tsakiya) ta wakilta, ya yanke kyale domin ƙaddamar da na’urar zamani ta 1.5 Tesla Magnetic Resonance Imaging (MRI) a Asibitin Kashi na Ƙasa (NOH), Dala, da ke Jihar Kano, ranar Alhamis.
A wani gagarumin mataki na bunƙasa harkar lafiya a Najeriya, Gidauniyar NNPC, reshen kula da al’umma na Kamfanin NNPC Ltd., ta ƙaddamar da kuma miƙa cikakkiyar na’urar zamani ta 1.5 Tesla Magnetic Resonance Imaging (MRI) ga Asibitin Kashi na Ƙasa (NOH), Dala, Kano.
Wannan tallafi na daga cikin tsare-tsaren NNPC na inganta damar samun kulawar lafiya da kuma ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin ƙasar. Na’urar MRI za ta taimaka wajen gano cututtuka da wuri da kuma magance su, musamman a fannin ƙashi da jijiyoyi, rauni, tsokoki da kuma lafiyar mata.
Kafin wannan shigarwa, marasa lafiya da ke buƙatar irin wannan bincike na MRI kan fuskanci ƙalubale na tafiya mai nisa, jinkiri wajen samun kulawa, da kuma tsadar farashi.
Hakan na kunshe ne a wata Sanarwa dauke da sa hannun Andy Odeh Babban jamin hulda da Jama’a na Kamfanin.
A wajen taron ƙaddamarwa da aka gudanar a harabar asibitin, Shugaban Kamfanin NNPC Ltd., wanda Darakta Janar na NNPC Foundation, Mrs Emmanuella Arukwe ta wakilta, ya bayyana cewa wannan gudummawa na daga cikin manufofin kamfanin na bayar da gudummawar ci gaban kiwon lafiya a ƙasar.
“A NNPC Limited, muna da niyyar tabbatar da cewa jarin da muke yi ga al’umma yana da tasiri, mai ɗorewa, kuma mai amfani ga jama’a. Ta hanyar Gidauniyar NNPC, za mu ci gaba da aiwatar da shirye-shirye da ke kawo sauyi mai ma’ana a faɗin Najeriya,” in ji ta.
Haka kuma, Mrs Sophia Mbakwe, Mataimakiyar Shugaban Kamfanin NNPC a ɓangaren sabis, ta jaddada cewa NNPC ba wai kawai tana samar da man fetur ba, har ma tana taka rawa wajen inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
“Wannan taron shaida ne na jajircewarmu wajen kawo sauyi mai ɗorewa da kuma taimakawa al’umma, musamman marasa galihu da masu rauni. Wannan na’urar MRI za ta inganta harkar lafiya a Kano, Arewa maso Yamma, da kuma Najeriya baki ɗaya,” in ji ta.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Lafiya, Abubakar Labaran Yusuf ya wakilta, ya yaba da wannan gudummawa, yana mai cewa ta kawo babbar nasara wajen inganta bincike da kulawa da marasa lafiya.
Shugaban Asibitin, Dr Isa Nurudeen, ya nuna godiya ga NNPC, yana mai cewa wannan na’ura za ta kawo sauyi mai girma a ayyukan asibitin da kuma kulawa da marasa lafiya.
Taron ya samu halartar jami’an NNPC, ma’aikatan asibitin, jami’an gwamnati, likitoci, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.





















