
Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC Limited, ya rattaba hannu kan yarjejeniyoyin gas guda shida masu muhimmanci tare da abokan hulda domin bunkasa masana’antu da kuma karfafa tsaron makamashin Najeriya.

An rattaba hannun ne ranar Talata a gefen taron NOG Energy Week na 25 da ke gudana a Abuja, kamar yadda Andy Odeh Babban jamin hulda da Jama’a na kamfanin ya sanar.

A cewar NNPC Ltd, yarjejeniyoyin sun hada da: Yarjejeniyar Fahimtar Juna da Kamfanin Karfen Ajaokuta, ASCL; Yarjejeniyar Tattara da Siyar da Gas ga ASCL; Yarjejeniyar Siyar da Gas ga UTM FLNG; da kuma yarjejeniyoyin Shiga Cibiyar Sadarwa guda uku da Chevron Nigeria Ltd, AGPC, da NNPC Exploration & Production Ltd, NEPL suka yi.
Shugaban Kamfanin na NNPC Ltd, Injiniya Bayo Bashir Ojulari, ya ce yarjejeniyoyin sun nuna aniyar kamfanin na tallafawa manufar Gwamnatin Tarayya ta bunkasa masana’antu ta hanyar gas.
“Abin da muke gani a yau ba kawai sa hannu kan yarjejeniya ba ne. Wannan shi ne kunna injin bunkasar masana’antun Najeriya. Gas shi ne mabuɗin. Shi ne tushen samun kudi da riba. Haka kuma shi ne kadai kayan da zai iya yin tasiri irin na masana’antu a Najeriya fiye da kowane mai,” in ji Ojulari.
Ya kara da cewa yarjejeniyoyin sun nuna aniyar NNPC Ltd kan gaskiya, inganci da tsarin daidaitacce na amfani da gas a fadin kasar, wanda zai bude sabbin hanyoyin samar da gas ga kasuwar cikin gida.
Babban abin da ya dauki hankali a taron shi ne yarjejeniyar da aka yi da Kamfanin Karfen Ajaokuta.
A karkashin Yarjejeniyar Fahimtar Juna, NNPC Ltd da ASCL za su fadada hadin gwiwa fiye da samar da gas zuwa hada da samar da kayan danye na bututun mai da gas. Wannan zai taimaka wajen manyan ayyuka kamar bututun Gas na Afirka-Atlantic, AAGP, da kuma Tsarin Bututun Escravos zuwa Lagos na 3, ELPS 3.
Bugu da kari, an kuma sanya hannu kan Yarjejeniyar Siyar da Gas ta shekaru 20 tsakanin NNPC E&P Limited, Kamfanin Tattara Gas na Najeriya, GACN, da ASCL. Yarjejeniyar za ta ga an samar da 3MMscf/d na gas mai tabbas da 47MMscf/d na gas na wani lokaci don amfani a matsayin kayan ciyar da wutar lantarkin da ke ciyar da masana’antar karfen.
NNPC Ltd ta kuma dauki wani babban mataki na cin moriyar albarkatun gas na Najeriya ta hanyar sanya hannu kan Yarjejeniyar Siyar da Gas Mai Ruwashi ta shekaru 15 tsakanin Hadin Gwiwar NNPC Ltd/Seplat Energy Producing Nigeria Unlimited da UTM FLNG Ltd.
A karkashin yarjejeniyar, Hadin Gwiwar za ta samar da 200MMscf/d na gas ga aikin UTM Floating LNG. NNPC ta ce hakan zai ba da tabbacin samar da gas na dogon lokaci da ake bukata don samun kudi da kuma shirya aikin don yanke shawarar Zuba Jari na Karshe a cikin kwata na hudu na 2026.
Bugu da Kari, don kara karfafa kasuwar gas ta cikin gida, NNPC Ltd ta sanar da sauya tsoffin yarjejeniyoyin hada-hada zuwa sabon “Lambar Sadarwar Sufurin Gas ta Najeriya.”
An sanya hannu kan Yarjejeniyoyin Shiga Cibiyar Sadarwa tare da Chevron Nigeria Limited, AGPC, da NEPL. Wadannan yarjejeniyoyin za su shigar da har zuwa 800MMscf/d na iskar gas cikin cibiyar sadarwar sufuri ta cikin gida. Wannan zai yi amfani ga tashoshin wutar lantarki, masana’antun da ke amfani da gas da kuma yankunan masana’antu.
Manyan baki da suka halarci sa hannun sun hada da Ministan Jiha na Ma’aikatar Man Fetur, Gas, Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo; Ministan Jiha na Man Fetur, Mai, Sanata Heineken Lokpobiri; Mai Ba da Shawara ta Musamman ga Shugaban Kasa kan Makamashi, Ms. Olu Verheijen; Babbar Jami’ar NUPRC, Mrs Oritsemeyiwa Eyesan; da Babban Jami’in NMDPRA, Injiniya Rabiu Umar.
Bikin cika shekaru 25 na NOG Energy Week mai taken “Ci Gaba da Buri a Fannin Makamashi don Tattalin Arziki Mai Dorewa” zai ci gaba tsawon mako daya tare da tarurruka da Baka koli da nufin bude sabbin hadin gwiwa don ci gaban makamashin Afirka.





















