Daga; BAshir Bello, Abuja
KAMFANIN Dangote Coal Mines Limited, dake Jihar Kogi, ta raba tallafin karatu na miliyoyin nairori ga dalibai wadanda ke zaune a yankunan da ke al’ummomin da ke karbar bakuncin ayyukansa, domin zaman karatu na shekarar 2026/2027.
Wannan shirin tallafin karatu wani bangare ne na ayyukan kamfanin na ‘Alhakin Kamfani ga Al’umma’ (CSR), wanda aka tsara domin cika yarjejeniyar ci gaban al’umma (Community Development Agreement – CDA) da ke tsakanin kamfanin da al’ummomin yankin, tare da nufin inganta samun ingantaccen ilimi da kuma tallafawa ci gaban dan adam.
Shirin yana nuna jajircewar kamfanin wajen inganta ilimi a al’ummomin da ke karbar bakuncinta, ta hanyar tallafawa dalibai, rage nauyin kudi ga iyaye da masu kula da su, da kuma samar wa matasa damammaki masu yawa don cimma burinsu na ilimi.
Babban Manaja mai kula da Ayyuka na Musamman, Mista Nuhu Elujah, wanda Mista Emmanuel Alonge ya wakilta, ya bayyana cewa, wadannan ayyukan CSR wani bangare ne na kudurin kamfanin na inganta ci gaban al’umma mai dorewa da kuma samar da damammaki ga tsararraki masu zuwa.
Acewar sa, al’ummomin da suka ci gajiyar shirin sun hada da Awo-Akpali, Awo-Ojuwo, Awo-Akpolokuta, Awo-Atte, Onupi, da Ajobe-Ofeanyaka; abin da ke nuna jajircewar kamfanin wajen tabbatar da cewa fa’idojin shirin tallafin iliminsa sun isa ga dalibai a dukkan al’ummomin da ke yankunan da su ke.
Ta hanyar wannan shiri, Dangote Coal Mines Limited na da nufin fadada damammakin ilimi, karfafa kwarewa a fannin karatu, da kuma samar wa da matasa ilimi da kwarewa, wadanda za su iya bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban al’ummominsu da kuma kasar baki daya.
Ya kara da cewa, shirin tallafin karatun wani bangare ne na cika alkawuran kamfanin na ‘Alhakin Kamfani ga Al’umma’ (CSR) kamar yadda aka amince a cikin Yarjejeniyar Ci Gaban Al’umma (CDA), ta hanyar aiwatar da shirye-shirye masu tasiri da ke inganta ilimi, ci gaban dan adam, da ci gaban zamantakewa.
Ya bayyana cewa, kamfanin ta mika takardun biyan kudi (cheques) na tallafin karatu ga dalibai 42 da ke karatu a cibiyoyin ilimi daban-daban, wadanda suka fito daga al’ummomi shida masu arzikin kwal a Karamar Hukumar Ankpa ta Jihar Kogi.
A cewarsa, an tsara wannan shiri ne domin rage nauyin kudi da ke tattare da neman ilimi a matakin gaba da sakandare ga daliban da suka ci gajiyar shirin da kuma iyalansu, tare da karfafa kwarewa a fannin ilimi, da kuma samar wa matasa daga al’ummomin da ke makwabtaka da kamfanin damammaki masu yawa don cimma burinsu na ilimi.
Ya kara da cewa, shirin bayar da tallafin karatu yana nuna jajircewar kamfanin wajen bunkasa al’umma baki daya, tare da nuna imanin cewa saka hannun jari a fannin ilimi yana da matukar muhimmanci wajen samar da tsari mai kyau, bada karfin gwiwa, da kuma amfani, wadanda za su iya bayar da gudummawa ga ci gaban al’ummominsu da kuma al’umma baki daya.
A matsayin nuna godiya ga kamfanin, shugaban al’ummar Awo-Akpali, Dakta Samuel Adejoh wanda ya yi magana a madadin sauran al’ummomin da suka ci gajiyar shirin, ya yaba wa hukumar gudanarwa ta kamfanin Dangote Coal Mines Limited bisa cika alkawuran da ta dauka ga al’ummomin da ke makwabtaka da su.
Ya bayyana cewa, shirin tallafin karatun zai taimaka matuka wajen rage nauyin kudi da ke kan dalibai da iyayensu, tare da bai wa wadanda suka ci gajiyar shirin damar cimma burinsu na ilimi ba tare da fuskantar matsalolin kudi da ba dole ba.
A wani labarin kuma, kamfanin ta ba da takardar kudin haya na filaye na shekarar 2026/2027 ga masu filaye a al’ummomin Awo-Akpali, Awo-Ojuwo, da Awo-Akpolokuta.
Wadanda suka karbi kudaden sun nuna godiyarsu ga hukumar gudanarwar kamfanin bisa biyan kudin hayar filayen a kan lokaci, inda suka bayyana hakan a matsayin shaida ta jajircewar kamfanin wajen kula da kyakkyawar alaka a tsakanin ta da al’ummomin da ke yankin.
Sun yi kira ga kamfanin da ta ci gaba da biyan kudaden hayar a kan lokaci, suna masu nuna cewa wannan tallafin kudi zai taimaka wajen rage matsalolin tattalin arziki da masu filayen da iyalansu ke fuskanta.





















